Moroko za ta koma tarayyar Afrika

Morocco Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shekaru 31 kenan da ficewar Morocco daga kungiyar trayyar Afurka.

A hukumance kasar Moroko ta sanar da aniyarta na sake shiga kungiyar Tarayyar Afrika.

A wani sako da kasar ta aike wa kungiyar da ke taro a kasar birnin Kigali na kasar Rwanda, Sarki Mohammad na shida yace lokaci ya yi da Moroko za ta sake komawa cikin iyalanta.

A shekarar 1985 ne Moroko ta fice daga kungiyar trayyar Afrika, a lokacin da aka kungiyar tai na'am da fafutukar da yankin yammacin Sahara ke yi.

Yayin da ita kuma Moroko ta ce yankin yammacin Saharar ya fada ne cikin iyakarta.

Sai dai a ranar juma'a da ta wuce ne kungiyar tarayyar Afrika ta ce za ta ci gaba da fafutukar karbar wa mutanen yankin yammacin Saharar 'yanci.