Thailand ta fara rufe gidajen karuwai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Harkar karuwanci ta yi kamari a Thailand

Hukumomi a Thailand sun fara kai wani gagarumin samame kan gidajen karuwai da matattarar masu neman mata.

Ministar harkokin yawon bude ido ta kasar Kobkarn Wattanavrangkul, ta ce tana so ta kawo karshen irin wadannan al'amura ne don ciyar da harkokin yawon bude ido gaba.

An haramta karuwanci a Thailand, amma harka ce da ta yi kamari a kasar kuma ana ganin tana taimakawa wani bangare na tattalin arziki.

A farkon watan nan ne aka gano 'yan cirani masu karancin shekaru da dama a gidajen shakatawa na Bangkok babban birnin kasar.