Turkiyya ki kai zuciya nesa — Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption John Kerry ya ce bai kamat Turkiyya ta zargi Amurka da hannu a yunkurin juyin mulki ba

Amurka ta bukaci Turkiyya da ta kai zuciya nesa, sakamakon matakan da take dauka kan 'yan kasar bayan wani yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba.

Tun daga ranar Juma'a da lamarin ya faru, gwamnatin Turkiyya ta kama dubban sojojin kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya bukaci mahukuntan Turkiyya da su kasance masu bin doka yayin da suke gudanar da bincike a kan yunkurin juyin mulkin.

John Kerry ya ce duk ikirarin da ake yi cewa Amurka na da hannun wajen yunkurin juyin mulkin, ba zai tsinana komai ba face raunana dangantakar da ke tsakanin kasashe biyun, wadanda dukkansu mambobi ne na kungiyar tsaro ta NATO.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya bukaci shugaba Obama, da ya tisa-keyar wani shehun Malami mai suna Fethullah Gulen, zuwa Turkiyya, sakamakon zarginsa da hannu a shirya juyin mulkin, amma Malamin ya musanta.

Amurka, a nata bangaren, ta ce ba za ta dauki matakin tisa-keyar Falehullah Gulen ba, sai Turkiyya ta kafa hujjar laifin da take zargin ya aikata.

Ko a ranar Lahadi ma, dakarun tsaron Turkiyya na cigaba da kama karin sojoji da ake zarginsu da hannu a shirya juyin mulkin.