Ambaliyar ruwa ta afkawa Jos

Yadda ambaliyar ruwan ta rusa gidaje Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ambaliyar ruwan ta janyo hasarar dukiya.

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato a Nijeriya na cewa ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a wasu unguwannin da ke cikin birnin.

Lamarin dai ya faru ne ranar Litinin da al'umuru, kuma ya tilasta wa dimbin mutane barin gidajensu, inda suka kwana a gidajen 'yan-uwa da abokan arziki da bala'in bai shafa ba.

Ambaliyar ruwan dai ta faru ne a yankin da ya fuskanci irin wannan matsala shekara hudu da suka gabata, inda akai hasarar rayukan mutane da dunbin dukiya.