Za a kunyata wadanda suka ci bashin banki

Image caption Bankunan sun wallafa sanarwar ce a jaridu

Bankunan Najeriya sun yi barazanar cewa za su kunyata mutanen da suke bi bashi, domin su biya kudaden da ake bin su.

Bankunan sun sanar da haka ne a wata sanarwa da suka wallafa a jaridun kasar, a ranar Litinin.

Sun kuma ce in har suka ga mutanen da suke bi bashi din ba su da alamar biya, to za su wallafa sunayensu a jaridu.

A kwanakin baya babban bankin Najeriya ya sanar da cewa bankunan kasar na bin bashin kusan dala biliyan biyu.

A baya ma dai sai da gwamnati ta tallafawa wasu bankuna da dama sakamakon dumbin bashin da suke bin abokan cinikinsu da basu biya su ba, wanda hakan yasa suka kusa durkushewa.