Mahara sun kashe basarake a Jos

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kashe daya daga cikin manyan sarakunan gargajiyar jihar.

An dai kashe Saf Ron Kulere Mista Lazarus Agai ne a yau da wasu mutane uku dake tafiya tare da shi a mota.

Shi ne dai shugaban sarakunan gargajiya na karamar hukumar Bokkos, kuma yana daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar.

Jihar Filato ta jima tana fama da rikici a baya da ya shafi kabilanci da kuma addini.