Yadda Malamai ke wa'azi a shafukan zumunta

Tun lokacin da shafukan sada zumunta na zamani suka bullo jama'a ke amfani da su domin biyan bukatu daban-daban.

Mutane daban-daban, kama daga 'yan kasuwa zuwa shahararrun mawaka da jaruman fina-finai, da masana kimiyya da 'yan kwallo, da sauran su, kan yi amfani da shafukan domin aikewa da sakonni.

Wani rukunin mutane da ya bai wa wadannan shafuka muhimmanci kuma shi ne malaman addini.

Fitattun shugabannin addini irin su Paparoma Francis sun riki wannan hanya domin aikewa da sakonni ga mabiyansu, kuma a yanzu haka yana da mabiya kusan miliyan goma a shafinsa na Twitter.

Haka batun yake ga malaman addinin Musulinci ma, inda fitattun malamai irin su Mohamed Al-Arifi ke kan gaba a cikin malaman addinin Islama na Saudiyya da ma duniyar Musulmai da ke da kwarjini a shafukan sada zumunta.

Mohamed Al-Arifi yana da mabiya sama da miliyan goma sha biyar a shafinsa na Twitter

Wasu daga cikin abubuwan da ya fada a kan mata su kan jawo ce-ce-ku-ce.

Baya ga al'amuran yau da kullum, Al-Arifi yana bayyana ra'ayoyi a kan siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.

A Najeriya da sauran kasashen Afirka ma, akwai malamai da dama da ke rungumar wadannan shafuka domin isar da sakonni ga mabiyansu.

Malam Isa Ali Pantami, wani fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yin wa'azi da gudanar da muhawara a kan batutuwa da dama.

Ya shaida wa BBC cewa babban abin da ya sa ya rungumi wadannan shafuka domin yin wa'azi shi ne, "Kasancewar addinin Musulunci wayayyen addini, wanda ke tafiya da zamani. Shi ya sa yake da kyau mai yin wa'azi ya san duniyar da yake rayuwa a cikinta saboda maganarsa ta dace da al'umma".

Malam Pantami ya kara cewa, a baya wasu Malaman addinin Musulinci sun bayar da fatawar da ke nuna rashin dacewar amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen isar da sako, amma daga bisani suka ga amfani shafukan, lamarin da ya sa suka sauya ra'ayoyinsu a kansu.

Shi ma Fasto Sam Adeyemi, wani fitaccen malamin addinin Kirista, ya mayar da hankali sosai wajen yin kira ga mabiyansa ta shafinsa na Twitter.

Malamin cocin ya shahara sosai wajen fadakarwa da kuma jayo hankalin mabiyansa a kan muhimmanci riko da gaskiya da kuma bin dokokin kasa a shafin nasa.

Fasto ne mai bai wa matasa dama su gina rayuwarsu da kuma hanyoyin da za su bi domin bunkasa rayuwarsu a wannan zamani mai cike da rudani.

Wani malami da ya yi fice wajen amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya shi ne Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Malamin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano da ke arewacin kasar, yana yawaita amfani da shafukan domin aikewa da nasihohi da fadakarwa ta hanyar wallafa ayoyin Al-Kur'ani da hadisan Manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W) da kuma fahimtar malamai a kan matsalolin rayuwa da yadda za a shawo kan su.

Malamin yana da mabiya kusan dubu dari uku a shafinsa na Facebook, wadanda kuma ke yi masa tambayoyi a kan abubuwan da shuka shige musu duhu.

Bayanan hoto,

Sheikh Aminu Daurawa yana daga cikin manyan Malaman da ke isar da sako ta shafukan zumunta na zamani

Menene ra'ayinku kan amfani da shafukan sada zumunta da Malamai ke yi wajen yin wa'azi? Ku bayyana ra'ayoyinku a shafinmu na BBC Hausa Facebook