Wayar salula ta murkushe tankokin yaki

Erdogan Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Shugaba Erdogan ya yi amfani da manhajar Face Time a hirar da aka yi ta shi a gidan talabijin

Yunkurin yujin mulkin da wasu sojoji suka yi a Turkiyya ya ci tura ne sakamakon wasu dalilai da suka hada da kiran da Shugaban Recep Tayyip Erdogan ya yi ta wayar salula cewa jama'a su fito su tunkari sojojin.

Cikin ‘yan mintina kadan duniya ta cika da labari, kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta suka cika makil da labaran juyin mulkin.

Nan take tituna, da manyan gadoji da sauran muhimman wurare a biranen Santabul da Ankara suka cika da motoci masu sulke na soji, yayin da jiragen yaki suka rinka shawagi.

Jama’ar kasar suka shiga cikin rudani, musamman da aka ji labarin cewa Shugaba Erdogan ba ya gida lokacin da abin ke faruwa.

Masu sharhi da dama sun zata juyin mulki ya tabbata ganin yadda sojoji, wadanda ba su samu goyon bayan shugabanninsu ba, suka mamaye gidan talabijin din kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nan take titunan kasar suka cika da masu adawa da juyin mulkin

Sannan suka sanar da kwace iko daga hannun zababbiyar gwamnati.

Sai dai a daidai lokacin da ake ganin tankunan yaki da jirage masu saukar ungulu na kan hanyar kwace iko da kasar, shugaba Erdogan ya yi wani yunkuri da ba za a manta da shi a tarihi ba.

Daga tsibirin shakatawa na Marmaris ya yi hira da gidan talabjin na CNN Turk ta waya, inda ya yi amfani da manhajar Face Time ta wayar iPhone, inda ya ce juyin mulkin ba zai yi nasara ba.

Sannan ya yi kira ga al’ummar kasar da su fita kan tituna domin nuna adawa da masu yunkurin kifar da gwamnatin.

Jim kadan da watsa jawabin na Mista Erdogan, wanda ke da farin jini sosai, sai titunan kasar da wuraren tarurruka suka cika da jama’a wadanda suka amsa kiran shugaban.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jama'a sun kwace tankunan yakin da sojojin suka fito da su

Magoya bayan shugaban sun rika fafatawa da sojojin a sassa daban daban na biranen Santanbul da Ankara, inda aka kashe farar hula fiye da 200, sakamakon bude musu wuta da sojojin suka yi.

A karshe jama’ar kasar sun yi nasarar murkushe juyin mulkin, inda sojoji su rinka guduwa suna barin tankokin yaki da kuma makamansu, inda jama’a suka rinka darewa suna daukar hotuna.

Wayar salular da shugaba Erdogan ya yi amfani da ita wurin hira da gidan talabajin, tare da kira ga jama’a da su fita kan tituna, na sahun gaba wurin dalilan da suka sa juyin mulkin ya ci tura.

Wannan ya sake bude sabon shafi a batun tasirin wayar salula da sauran na’urorin sadarwa na zamani, tunda gashi har ta kai ga korar tankunan yaki.

Sai dai zai iya zama darasi ga shugaban, wanda a baya ya sha rufe shafukan sada zumunta, ganin yadda a yanzu ya yi amfani da su wurin cimma bukatunsa.