Dubban yara 'na fama da yunwa' a Borno

Nigeria
Image caption Unicef na tallafawa dubban mutane a asibitocinta

Akalla yara 250,000 ne ke fama da karancin abinci mai gina jiki a wasu sassa na jihar Borno, da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya, a cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar kula da kananan yara ta Malisar, Unicef, ta yi gargadin cewa dubun dubatarsu ka iya mutuwa idan ba su samu kulawar gaggawa ba.

Unicef ta gano cewa mutane na rayuwa ba tare da ruwa, abinci da abubuwan tsaftace muhalli ba, a yankunan da Boko Haram ke rike da su a baya.

A watan da ya gabata, wata kungiyar agaji ta ce mutanen da suka tsere daga kungiyar Boko Haram na mutuwa saboda yunwa.

Akalla mutane 20,000 ne aka kashe a shekaru bakwai da aka shafe ana rikicin Boko Haram, yayin da sama da miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

'Yara 134 na mutuwa a kowacce rana'

Rahoton ya kara da cewa ya yin da sojojin Najeriya ke kara dannawa kauyukan da Boko Haram ta mamaye, ake kuma samun damar kai agaji yankunan, matsalar rashin abinci mai gina jiki na kara fitowa fili.

UNICEF ta ce cikin yara 2440 da ke fama da rashin abinci maigina jiki a jihar Borno, daya cikin biyar ka iya mutuwa idan har ba a yi gaggawar taimaka musu ba.

Jami'in Unicef mai kula da shiyyar yammaci da tsakiyar Afurka Manuel Fontaine yace wasu yaran 134 ka iya mutuwa a kowacce rana saboda cututtuka masu nasaba da abinci mara gina jiki.

'Zuru-zuru saboda rashin abinci'

Ya yi kira ga dukkan kasashe, da kungiyoyin bada agaji da su shigo cikin lamarin dan ceto rayuwar yaran da kuma kare sauran yara daga fadawa hadarin da su ke ciki.

Mista Fontaine ya kara da cewa a kauyukan da suka ziyarta a jihar Borno, ya ga kauyukan da 'yan Boko Haram suka daidaita amma duk da haka mutane na zaune a cikin su a mawuyacin hali.

"Dubban yara kanana sun yi zuru-zuru saboda rashin abinci cikin tsananin bukatar taimako".

A karshe rahoton yace har yanzu akwai mutane miliyan biyu da har yanzu UNICEF ta gagara isa inda suke, wanda hakan ke nuna ta yiwu matsalar da kananan yaran ke ciki ta karu idan aka isa inda suke.