Dan majalisa ya rasa mukami kan badakalar kasafin kudi

Abdulmumini Jibrin Hakkin mallakar hoto other
Image caption Honorabul Abdulmumini Jibrin na daga cikin na hannun damar kakakin majalisar

An cire shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya daga mukaminsa, saboda zarginsa da hannu a badakalar da ta dabaibaye kasafin kudin kasar na bana.

An zargi Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, da hannu wurin sanya wasu bayanai da suka janyo cece-kuce tsakanin gwamnati da majalisar.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ya sallame shi ne daga shugabancin kwamitin a zauren majalisar.

Sannan ya maye gurbinsa da Mustapha Bala Dawaki daga Kano, wanda a baya shi ne shugaban kwamitin gidaje na majalisar.

Majiyar ta kara da cewa Mista Dogara bai ji dadin yadda dan majalisar, wanda na daga cikin na hannun damarsa, ya "jefa shi cikin rikici da bangaren zartarwa ba".

An kuma zargi Honorabul Jibrin da ware makudan kudade a kasafin kudin ga mazabarsa.

To ssai dai dan majalisar ya ce ya sauka ne dan kashin kan sa.

'Yan majalisar da dama sun koka kan rawar da suka ce ya taka a badakalar, inda suka nemi da ya sauka daga mukaminsa.