Nigeria: An samu baraka a kungiyar CAN

Hakkin mallakar hoto Getty

Bisa ga dukkan alamu dai barakar da ta kunno-kai cikin kungiyar Kiristocin Nijeriya, CAN, na kara girma bayan wasu mabiya addinin Kirista daga yankin arewacin kasar suka yi barazanar ballewa daga kungiyar domin su kafa tasu kungiyar.

Mutanen sun yi barazanar ce saboda zargin da suka yi cewa an yi magudi a zaben da aka yi na shugaban kungiyar, suna masu cewa maimakon a bai wa dan arewa mukamin, an sake mika shi ga kudancin kasar.

A watan jiya ne dai aka zabi sababbin shugabannin kungiyar ta CAN.

Rabaran Luka Shehu, shi ne mai magana da yawun kungiyar Concerned Christians, da suka yi wani taron manema labarai a Jos, jihar Filat, kuma ya ce an yi zaben nan ne dan a tauye hakkin wasu mambobin CAN.

Ya kara da cewa a ka'ida ya kamata a yi karba-karbar shugabancin kungiyar ne, kuma a yanzu dan arewa ne ya kamata ya jagorance ta amma kuma 'yan kudancin Najeriya sun yi kane-kane a kan mukamin.

Sai dai sakatare janar na kungiyar CAN Rabaran Musa Asake ya ce barazana ce kawai su ke yi, yana mai cewa hasali ma ba su amincewa 'yan kungiyar CAN ba ne, domin kuwa su kawunansu a hade suke.