An yi wa amarya kisan-gilla a Kano

Image caption A baya ma an kashe wasu amaren a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria ta ce tana ci gaba da bincike a kan kisan-gillar da aka yi wa wata amarya da ke unguwar Sha'iskawa cikin karamar hukumar Dambatta a jihar.

Wasu mutane ne da ba a san ko su wane ba suka haura gidan aurenta inda suka yi mata yankan rago bayan sun yi mata fyade a karshen makon jiya.

Mai magana a yawun runuduna 'yan sandan jihar ta Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce an yi wa amaryar fyade, sannan aka yanka ta da wata wuka da aka dauka a gidan.

Lamarin dai ya faru ne kwana uku bayan tafiyar mijin amaryar zuwa babban birinin Nigeria Abuja, inda yake fatauci.

'Yan sanda sun ce kofar gidan amaryar ba shi da kyaure, sannan katangar gidan ba ta da tsawo.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yi wa amare kisan-gilla a birnin Kano ba.

A bara an yi wa mata uku a unguwanni daban-daban irin wannan kisa, dukkan su a gidajen mazajensu, daya a Bachirawa, daya kuma a unguwar Dorayi, yayin da dayar kuma aka kashe ta a unguwar Sharada, dukka a cikin birnin Kano.