Za a fara amfani da tashar ruwa a Nigeria

A Najeriya, hukumar da ke kula da harkokin jiragen ruwa, wato Nigerian Shippers Council ta kaddamar da shirye-shiryen fara amfani da tashoshin jiragen ruwa na kan tudu, wato Indland Dry Ports, a sassa daban-daban na kasar.

Hukumar ta ce za a bai wa 'yan kasuwa damar gina tasoshin a jihohin Kano da Katsina da kuma Borno.

A cewar hukumar, matakin zai rage cunkoso a tasoshin jiragen ruwan kasar da kuma saukaka wa 'yan kasuwa shigar da kaya daga kasashen waje.

Malam Hassan Bello, shi ne shugaban hukumar ta Nigeria Shippers Council, kuma ya shaida wa BBC cewa yanzu haka akwai tashoshi 6 da aka bude a kasar a johin Oyo, da Funtuwa, da Abia, da Kano, da birnin Jos na jihar Filato, da kuma Maiduguri:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti