NUC ta soke shaidar horar da malamai ta NTI

A Najeriya, bisa dukkan alamu malaman makarantu musamman na arewacin kasar za su rasa takardun cancantarsu ta koyarwa bayan da hukumar kula da Jami'o'i ta kasa, NUC ta soke shirin bayar da shaidar Digiri da cibiyar horas da malamai ta kasa, NTI ke yi a kasar.

A wata sanarwa da NUC ta fitar ta bayyana cewa NTI ba ta da izinin bayar da Digiri ko shaidar karatu ta bayan Digiri wato PGDE domin Cibiyar ba Jami'a ba ce, haka kuma ba ta da huldar karatu da wata Jami'a a kasar.

Sanarwar ta NUC ta kuma haramta neman aikin malanta da shaidar takardar kammala karatu ta NTI, sannan kuma ta haramta wa wadanda suka samu shaidar zuwa hidimar kasa.

Kakakin hukumar NUC Ibrahim Usman Yakasai ya shaida wa BBC cewa NTI ba ta da izinin bayar da shaidar Digiri ko Dipiloma.

Ya ce sun jima suna gargadin NTI da ta daina bayar da irin wadannan shaidu na karatu.

Matakin dai bai yi wa malamai masu irin wannan shaidar dadi ba.

Shugabar kungiyar malaman makaranta a jihar Kaduna, Kwamrade Audu Amba, ya ce batun ihu ne bayan hari, yana mai cewa NUC ta san an jima ana neman takardar shaidar malanta ta NTI amma, a cewarsa, ba ta dauki mataki ba sai yanzu.

Wani sabon tsari na ilimi na Najeriya ya bukaci malamai da su daga darajar iliminsu, hakan ya sanya malamai da dama rijista da Cibiyar ta horas da malamai NTI domin samun takardar shaidar Digiri.