Sudan Ta Kudu ta gargadi Tarayyar Afirka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikici na cigaba da kamari a Sudan Ta Kudu

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Sudan Ta Kudu, ya gargadi kungiyar Tarayyar Afirka AU, da kada ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya ba tare da iznin gwamnati ba.

Lul Ruai Koang ya ce gwamnati ba za ta yarda da duk wani yunkuri na kai sojoji kasar ba tare da lamuncewar ta ba.

A ranar Laraba ne mambobin kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa suka yi wata zanga-zanga ta nuna adawa da kai sojojin kasashen waje babban birnin kasar na Juba.

Daruruwan mutane sun yi tattaki na musamman a Juba, domin nuna adawa da shirin kungiyar Tarayyar Afrika na tura dakaru domin kawo karshen rikici tsakanin masu goyon bayan shugaba Salva Kiir, da abokin hamayyarsa Riek Machar.