BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 13 Yuli, 2009 - An wallafa a 10:08 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Shirin Safe/Shirin Hantsi
 
Manuel Zelaya
Manuel Zelaya

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Honduras ta bada sanarwar kafa dokar hana yawo a daukacin kasar, bayanda hambararren shugaban kasar Manuel Zelaya yayi wani shigar ba zata cikin kasar.

An rufe dukkanin filayen jiragen saman kasar, saannan mahukunta sun sanya yan sanda da sojoji cikin shirin ko ta kwana. Shugaban kasar mai ci Roberto Micheletti ya bayyana cewa.

Me yasa Mr Zelaya ya dawo Honduras? shi kadai ya sani, ni dai babu abin da zan yanke illa, ya zo ne kawai domin kawo cikas a zabukan da za a yi a 29 ga watan Nuwamba, kamar yadda shi da magoya bayansa suka ta yi cikin makon da gabata.


Sakatariyar kula da harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta ce, komawar tsohon shugaban kasar Honduras Manuel Zelaya gida, bai kamata ya zama sanadin tashin hankali ba.

Ta ce dole ne bangaren Mr Zelaya da na gwamnatin rikon kwaryar, su zauna domin samun maslaha.

Ta ce, ya zama tilas, a fara shawarwari, a samar da wata kafar jibantar juna tsakanin shugaba Zelaya da gwamnatin rikon kwaryar a cikin kasar Honduras.


Masu bincike a kasar Amurka, sun ce dokar hana shan taba sigari a inda matattarar jamaa suke, ka iya rage cutar bugun zuciya.

Tawagar masu binciken daga jamiar Kansas, sun kafa hujja ne da nazarin da aka yi a kasashen nahiyar Turai da arewacin Amurka.

Sun kwatanta adadin masu fama da cutar bugun zuciya kafin sanya dokar da kuma bayan kafa dokar.

Cutar ta bugun zuciya ta ragu da kashi 25 bisa dari bayan kafa dokar hana shan taba sigarin.


Kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International, ta ce kashi daya bisa 8 na mata masu juna biyu na fuskantar barazanar mutuwa a kasar Saliyo, daya daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da mutuwar mata a lokacin haihuwa.

Wani sabon nazari da kungiyar ta gudanar, ta bayyana cewa, dubban mata ne suke zub da jini har sai sun rasu bayan haihuwa, saboda basu da halin biyan kudi, domin samun ingantacciyar kayan lafiya.


A yau ne ake sa ran shugaban Nigeria, Alh Umaru Musa Yaradua, zai tashi zuwa kasar Saudiyya.

Mahukunta a Nigeriar sun ce, ziyarar tasa za ta dauki tsawon kwanaki biyar ne, inda zai tattauna tare da Sarki Abdullah, sannan ya gana da wakilan alummar Nigeria dake zaune a kasar ta Saudiyya.

Shugaba Yaradua, wanda yake fama da cutar koda, ya ziyarci kasar Saudiyya a watan jiya domin a duba lafiyarsa.


A Jamhuriyar niger, a ranar lahadin da ta gabata ne alummar musulmin kasar kamar dai mafi yawancin takwarorinsu na duniyar Musulmi suka gudanar da shagulgullan sallar azumi wato karamar salla.

Kimanin kashi 98 daga cikin dari na alummar kasar musulmi ne, wanda ya sanya duk wadansu bukukuwan sallolin muslunci ke da matukar tasiri a kasar.

Tun ma kafin zuwan ranar sallar, jamaa kan kwashe kusan mako guda suna shirye shiryen tunkararta, sannan akan kwashe wadansu kwanakin biyu zuwa ukku musamman a yankunan karkara ana ci gaba da shagulgullan raya wannan salla.

Ko da ya ke sallar ta bana ta zo ne a daidai lokacin da jamaar ke kukan rashi, mafi yawancinsu sun yi hamdala da yanda lamurran suka gudana.

Wakilimmu a yamai gazali abdu tasawa ya gudanar da bincike kan yadda alummar musulmin kasar mazauna birnin yamai su ka gudanar da shirye shirye da ma shagulgullan sallar, ga kuma rahoton daya hada mana na musamman.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri