Alakar tsaftar wurin aiki da halayyar ma'aikaci

Wasu teburan sun kasance tsaf-tsaf
Bayanan hoto,

A kan samu tarkace masu yawa a kan teburin ma'aikata

Akan iya fahimtar wane irin mutum ne kai walau ƙazami ko kuma mai tsafta ta hanyar kula da wurin da kake.

Ka na shan wahala wajen lalubo kwamfutarka daga cikin tarkacen da ka tara a ofishinka?

Kowane ma'aikaci yana da irin tsarinsa daban kan yadda yake son teburinsa ya kasance.

Akwai nazarce-nazarce da dama da suke nuna cewa yanayin ofishin mutum yana shafar yadda yake gudanar da aikinsa.

Wasu na ganin cewa barin wurin aiki hargitsatsa yana haifar da tunanin yadda za a yi aikin, a inda wasu kuma ke ikrarin cewa hakan ka iya haifar da karancin nutsuwa wajen gudanar da ayyuka.

Bayanan hoto,

Yadda teburin ma'aikaci mai son tara shirgi yake

Yadda ofishin mai son tara shirgi yake

Ofishin mutum wanda yake da shauni yana kasancewa hargitsatsa.

Wani sa'in kuma za ka gan shi gwanin sha'awa cike da abubuwa marasa amfani.

Hakan ne ya sa Bernheimer, wata mai nazari a jami'ar Surrey da ke Ingila ta siffanta yawancin masu shaunin tsaftace muhallinsu da mutane masu haba-haba kuma a koyaushe suna maraba da abokan aikinsu.

Irin wadannan mutanen sun kasance a koyaushe a cikin yanayin aikin da ba zai bar su har su samu damar tsaftace teburinsu ba, sabanin abokan aikinsu da ba su da haba-haba.

To amma duk da kazantar teburin aikin nasu, sun fi na abokan aikinsu masu tsafta samu ziyarar mutane saboda su koyaushe kofarsu a bude take.

Masu ajiye abubuwa kadan

Bayanan hoto,

Yadda teburin ma'aikata masu kaffa-kaffa yake

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tana iya yiwuwa mutum ya zama mara son tara tarkace a teburinsa, amma bai zama lallai ba ace kuma ba shi da haba-haba da jama'a.

Kawai dai za a iya cewa shi mutumin da ba ya son tara tarkace yana da halayyar sanin ya kamata sannan kuma yana da kaffa-kaffa.

Irin wadannan mutanen suna da kwazo a wurin aiki. Sai dai kuma ka kula cewa idan har ba ka yin wani katabus a wajen aiki, to fa hakan na nuni da cewa ba za ka dade a sabon mukamin da aka ba ka ba.

Masu mamaya

Akwai mutanen da suke da halayyar mamaye wuri a ofis.

Idan tafiya ta yi tafiya, irin wadannan mutanen suna iya mamaye teburin abokan aikinsu.

Sukan dora rigarsu ta kwat a kan kujerar da ba tasu ba ko kuma su ajiye shara a kan teburin abokan aikinsu.

A koyaushe " suna kokarin mamaye tebur-teburin da ba nasu ba ta hanyar dora kofinsu ko kuma kayan makulashen da suka ci, a kan teburan mutane." in ji Bernheimer.

Masu mamaya suna kaunar samun wuri a tsakiyar ofis kuma sukan iya zama masu tsauri wajen fidda iyakokinsu.

Za ka ji dadi idan akwai shinge tsakaninka da mutum mai mamaya wadda kake makwabtaka da shi. Amma idan kuna aiki da irin wadannan mutanen a wurin da ba a rarraba shi ba, to za ka gane halin masu mamayar na kokarin cin iyakarka.

Masu kaffa-kaffa

Bayanan hoto,

Ana ganin dai yawan tara tarkace yana hana nutsuwar aiki

Tana iya yiwuwa kai mutum ne mai son yin kaffa-kaffa da abubuwa.

Bernheimer ta bayyana masu kaffa-kaffa da "wadanda suke yin komai bisa tsari sannan suna da alamun karbar sabbin abubuwa abin da ke nufin za su iya zama masu basira kuma suna son rungumar abubuwan da ba su sani ba."

Bernheimer ta ce masu kaffa-kaffa mutane da suke da zakuwa wajen sanin abubuwan da ba su sani ba kuma suna da haba-haba da mutane sannan suna da basira.

Ta kara da cewa su masu irin wannan halayyar suna iya zma masu godiyar Allah ga irin aiki da suke yi kuma masu kwanciyar hankali sannan kuma sun kasance masu lafiya.

Irin wannan yanayin dai ya kan zama riba ga ma'aikaci da ma iyayen gidansa.

Masu zaben wuri

Akwai dalilin da yake sanya ma'aikata zaben wurin da suke son su zauna a ofis.

"A al'adance, muna son zama a wurin da za mu iya ganin wani abu mai hadari da zai same mu." In ji Bernheimer.

Masu zaben wuri suna son su samu wuri da za su kadaita saboda yawan hayaniya ko surutu ka iya hana su mayar da hankali kan abin da suke yi.

Su kan fi son zama a wurin da bayansu zai zama yana kusa da bangon ofis sannan kuma sun fi son yin aiki su kadai. Wani lokacin ma sukan zama masu kunci.

Sai dai kuma bai kamata ace an yi gaggawar yanke hukunci ba kan halayyar ma'aikatan.

Ma'aikata masu zaben wuri ka iya zama marasa son hulda da jama'a kuma masu hazaka da kwazo, in ji Bernheimer.

Abin da ya fi dai shi ne kawai ka da ka shiga shirginsu idan suna aiki.

Idan kana son karanta wannan labarin na turanci to za ka iya latsa nan What the state of your desk says about you