Bibiyar Trump : Da-me-da-me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?

US President Donald Trump salutes as he walks to Air Force One prior to departing from Langley Air Force Base in Virginia - 2 March 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Donald Trump ya cika kwana 100 yana mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasar Amurka da kuma mayar da iko ga mutane .

Saboda haka menene ya cimma ya zuwa yanzu? Muna bibiyar cigaban shugaban kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Wanne matakan zartarwa Trump ya dauka?

Wata hanyar da Shugaba Trump zai iya aiwatar da ikon zartarwa a siyasa ita ce ta bayar da umarnin zartarwa wanda ya ba shi damar tsallake matakin doka a majalisar dokokin kasar kan wasu monufofi.

Bai bata lokaci ba wajen amfani da wannan ikon wanda ya yi amfani da shi wajen janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin kan gabansa da gina layukan bututun mai biyu.

Duk da cewar ana ganin ya yi amfani da umarni irin ta yadda ba a taba gani ba, Shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da umarni kusan irin hakan a makonninsa na farko a kan mulki duk da cewar Mista Trump ya zarce mishi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yakin neman zaben da ya yi, amman tasirin su na da iyaka.

Yayin da umarnin irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, ba zai iya bai wa wadannan hukumomin sabbin kudade ba ko kuma damar gabatar da sabbin dokoki- ikon yin hakan na hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan tsarin kiwon lafiya na ObamaCare ya yi shi ne domin ya rage tasirin tsarin, amman alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa zai iya kasancewa ne kawai da taimakon majalisar dokokin kasar domin yana bukatar sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa ta ke ga Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya sha rantsauwar hawa karagar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi hakan ne da mafi raunin karbuwa a kuri'un jin ra'ayin jama'a da aka taba samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri'ar jin ra'ayin jama'ar a matsayin wata kuri'a wadda aka murda, kuma karfin adawar da ya fuskanta ya fito fili a lokacin da dubban mutane suka fita zanga-zangar kinsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa'adinsu ne da gagarumar karbuwa, amman Shugaba Trump ya sauya wannan yanayin. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa a lokacin da suka cika kwanaki 100 kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karbuwar mutum sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaben ne da amincewar mutane kadan a kuri'ar jin ra'ayin jama'a. Saboda haka ba abun mamamki bane cewar wadanda suka amince da shi kadan ne har yanzu. Amman ce-ce-ku-cen da alakarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa 'yan wasu kasashe shiga kasar sun sa wadanda suka amince da shi na kara raguwa.

Duk da haka, yunkurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsatsaurar ra'ayinsa kan shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaba a matsayin daya daga cikin alkalan kotun kolin kasar, abin da ya dawo da rinjayen masu ra'ayin rikau. Karbuwarsa a bangaren masu ra'ayin rikau tana sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda ta ke da.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

'Yan jam'iyyar Republicans suna jagorantar majalisun wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata ace zai iya nemi cimma manufofinsa na dokoki ba tare da damuwa game da karbuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan 'yan jam'iyyarsa ta Republican.

Amman in har karbuwarsa ta tsaya kasa-kasa, sai a tsammanci wasu muryoyi masu kin amincewa da shi su bayyana a cikin jam'iyyar a daiden lokacin da 'yan jam'iyyar Republican ke fara nuna damuwa game da zaben tsakiyar wa'adi na shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin dakile shiga kasar ba bisa ka'ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali akai a lokacin yakin neman zabe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwarin.

Daya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu akai ya ayyana cewar Amurka za ta gina katanga kokuma wani shamaki wanda ba za a iya wucewa ba a kan bakin iyakan kasar da Mexico, wurin da ya ke da mil 650 na katanga.

Amman Mista Trump yana bukatar amincewar majalisar dokokin kasar kafin a fara ginin, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya hakikance cewar Mexico za ta biya kudin daga baya, duk da cewar shuwagabanninta sun fadi akasin hakan.

Duk da cewar Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa biyu wadanda suka umarci jami'an shige da ficen kasar su dau tsatsaurar matakai kan aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamun da ke nuna cewar wannan sauyin yin aiki da dokar shige da fice -da kuma kakausar kalaman Shugaba Trump- za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka'ida ba.

A watan Maris, yawan mutane da aka kama a lokacin da suke neman ketarawa zuwa Amurka ya fadi zuwa mataki mafi karanci cikin shekara 17, in ji Sakataren ma'aikatar tsaron cikin gidan kasar.

Mista Kelly ya ce faduwar yawan mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen kasar ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Maganar sabon shugaban na dakile kwararar bakin haure ya sa ana tunanin bakin haure sun samu yadda suke so a karkashin Shugaba Obama, amman akwai dalilai da dama da ke nuna akasin hakan.

Tsakanin shekara 2009-2015 gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5- yanwacinsu wadanda aka samu da nau'o'i na manyan laifuka ko kuma basu dade da zuwa kasar ba abin da ya sa wasu suka yi wa shugaba Obama lakabi da "shugaba mai korar baki."

Amman kimanin bakin haure miliyama 11 ke zama a Amurka, yawancinsu daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da ta hana fasa kauri ta kaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zabi Mista Trump, amman lokaci bai yi ba da za a iya yanke hukunci kan ko korar bakin haure ya karu ko bai karu ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin gwamnatin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin kariyar arziki mafi muni wanda ba taba samun irin sa ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ta rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amman bayan faduwa kadan a shekarar, tattalin arzikin Amurka ta samu lokacin mafi tsawo na ci gaba inda ta fi samar da ayyukan yi. An samar da jumullar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da wadannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan kaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin a matsayin abin da cikin rikici.

Amman a lokacin da aka fitar da wani rahoton wata-wata a watan Maris wanda ya nuna cewar an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer ya ce babban labari ne ga ma'aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma "zama shugaba mai samar da aiki mafi yawa da aka taba yi."

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna satan miliyoyin ayyuaka kuma ya sha alwashin "kawo ayyukan mu gida." Amman abincike ya nuna cewar yawancin ayyukan kere-kere da suka salwanta a shekarun baya-bayannan an yi asararsu ne sabili da mashunan masana'antu kara samu kwarewar iya aiki da kansu, sabanin cewar hakan ya faru ne domin ayyuka sun fita waje ne.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habaka irin wadanda ba a taba samu ba a makonnin farkon Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu kwarin guiwa kan ayyukan ababen more rayuwar da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da ya ke son yi.

Amman habakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris a lokacin da aka fara tunanin garambawul din harajin ba zai faru da wuri ba yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya 'yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra'ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga 'yan jam'iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam'iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta "fashe."

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da 'yan jam'iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa'adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

'Yan Jami'yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam'iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri'u damin ya zama doka.