Bibiyar Trump : Me da me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?

US President Donald Trump salutes as he walks to Air Force One prior to departing from Langley Air Force Base in Virginia - 2 March 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Donald Trump ya cika kwana 100 a kan mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasa a Amurka da kuma mayar da iko hannun mutane .

Don haka me shugaban ya cim ma zuwa yanzu? Muna bibiyar ci gaban shugaba Trump kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Waɗanne matakan zartarwa Trump ya ɗauka?

Wata hanya da Shugaba Trump zai iya aiwatar da iko a siyasance ita ce bayar da umarnin zartarwa, abin da ya ba shi damar tsallake majalisar dokokin kasar wajen fitar da wasu manufofi.

Bai ɓata lokaci wajen amfani da wannan iko ba, ta hanyar janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin gaban kansa wajen shimfiɗa bututan mai guda biyu.

Duk da yake, ana ganin ya yi amfani da umarnin zartarwa ta hanyar da ba a taɓa gani ba, shi ma shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da irin wannan umarni a makonninsa na farko a kan mulki amma dai Mista Trump ya zarce shi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi, amma tasirinsu na da iyaka.

Yayin da umarni irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, amma ba zai iya bai wa waɗannan hukumomin kudaden gudanar da harkokinsu ba, ko ma damar gabatar da sabbin dokoki - wannan iko yana hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan shirin kula da lafiya na ObamaCare ya yi shi ne domin rage tasirin tsarin, amma alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa, zai iya tabbata ne kawai da taimakon majalisar dokokin Amurka domin yana bukatar sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa take awajen Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya karɓi rantsauwar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi haka ne da mafi ƙarancin karɓuwa a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a da aka taɓa samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri'ar jin ra'ayin jama'ar a matsayin wadda aka yi murɗiya, kuma ƙarfin adawar da ya fuskanta, ya fito fili a lokacin da dubban mutane suka fita zanga-zangar nuna ƙin jininsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa'adinsu ne da gagarumar karɓuwa, amma Shugaba Trump ya sauya wannan tarihi a Amurka. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa a lokacin da suka cika kwana 100 a kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karɓuwar sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaɓe ne da amincewar mutane kaɗan a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a. Saboda haka ba abin mamamki ba ne cewa waɗanda suka amince da shi tsiraru ne har yanzu. Amma ce-ce-ku-cen da alaƙarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa 'yan wasu ƙasashe shiga Amurka sun sa waɗanda suka amince da shi na ƙara raguwa.

Duk da haka, yunƙurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsattsauran ra'ayinsa kan harkokin shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaɓa a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan kotun ƙolin Amurka, abin da ya dawo da rinjayen masu ra'ayin riƙau. Karɓuwarsa a tsakanin masu ra'ayin riƙau ta kai sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda a baya.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

'Yan jam'iyyar Republicans suna jagorantar majalisar wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata a ce zai iya neman cim ma manufofinsa na dokoki, ba tare da damuwa game da karɓuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan 'yan jam'iyyarsa ta Republican.

Amma idan har karɓuwarsa ta tsaya ƙasa-ƙasa, ana tsammanin wasu muryoyi masu ƙin amincewa da shi, za su bayyana a cikin jam'iyyarsa, a daidai lokacin da 'yan Republican ɗin ke fara nuna damuwa game da zaɓen tsakiyar wa'adi da za a yi a shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin daƙile shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali kanta a lokacin yaƙin neman zaɓe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwari.

Ɗaya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu a kai, shi ne ayyana cewar Amurka za ta gina katanga ko kuma wani shamaki wanda zai hana tsallako iyakar ƙasar daga Mexico. Nisan iyakar ya kai mil 650.

Amma Mista Trump yana buƙatar amincewar majalisar dokokin Amurka kafin ya iya fara wannan gini, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya haƙiƙance cewa Mexico za ta biya kuɗin daga baya, duk da yake, hukumomin ƙasar sun ce ko kusa ba za ta saɓu ba.

Ko da yake, Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, amma dai ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa guda biyu waɗanda suka nemi jami'an shige da ficen kasar su ɗauki tsauraran matakai wajen aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamu da ke nuna cewar sauyin yin aiki da dokar shige da fice - da kuma kausasan kalaman Shugaba Trump - za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka'ida ba.

A watan Maris, yawan mutanen da aka kama a lokacin da suke ƙoƙarin shiga Amurka ya ragu zuwa adadi mafi ƙaranci a cikin shekara 17, in ji Sakataren ma'aikatar tsaron cikin gida.

Mista Kelly ya ce raguwar mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen Amurka ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Batun sabon shugaban na dakile kwararar baƙin haure ya sa ana tunanin baƙin haure sun samu yadda suke so a ƙarƙashin Shugaba Obama, amma akwai dalilai da dama da ke nuna akasin haka.

Tsakanin shekara ta 2009 - 2015, gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5 - yawancinsu wadanda aka samu ne da aikata wasu manyan laifuka ko kuma waɗanda ba su daɗe da shiga Amurka ba, abin da ya sa wasu suka riƙa yi wa Mista Obama laƙabi da "shugaba mai korar baƙi."

Kimanin baƙin haure miliyan 11 ne ke zaune a Amurka, yawancinsu kuma daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da hana fasa-ƙwauri ta ƙaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zaɓi Mista Trump, amma lokaci bai yi ba, da za a iya yanke hukunci a kan ko korar baƙin haure ya ƙaru ko bai ƙaru ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin karayar arziki mafi muni wadda ba ta taɓa samun irinta ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ya janyo rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amma bayan ɗan koma-bayan da ya samu a shekarar, tattalin arzikin Amurka ya samu lokacin mafi tsawo yana bunƙasa, inda ya janyo samar da ayyukan yi masu ɗumbin yawa. An samar da jimillar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da waɗannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan ƙaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin ƙasar a matsayin abin da ke cikin rikici.

Sai dai, wani sabon rahoton wata-wata da aka fitar a watan Maris da ke nuna cewa an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, ya sa Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer cewa matakin, babban labari ne ga ma'aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma "zama shugaba mai samar da aikin yi mafi yawa da aka taba samu a tarihi."

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna sace miliyoyin ayyuka don haka ya sha alwashin "kawo ayyukanmu gida." Amma wani bincike ya nuna cewa yawancin ayyukan ma'aikatun ƙere-ƙere da suka salwanta a shekarun baya -bayan nan, an yi asararsu ne saboda ƙwarewar da na'urorin masana'antu ke kara samu wajen iya aiki da kansu, sabanin iƙirarin cewa hakan ta faru ne saboda ana kai ayyuka ƙasashen waje.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habakar da ba a taba samu ba a makonnin farko na mulkin Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu ƙwarin gwiwa a kan ayyukan ababen more rayuwa da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da yake son yi.

Amma haɓakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris lokacin da aka fara tunanin garambawul ɗin harajin ba zai samu da wuri ba kamar yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya 'yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra'ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga 'yan jam'iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam'iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta "fashe."

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da 'yan jam'iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa'adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

'Yan Jami'yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam'iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri'u damin ya zama doka.