Ba za mu manta da gwamnatin Buhari ba — Shi'a

Ibrahim Elzakzaky Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kama Elzakzaky ya janyo zanga-zanga a kasashen duniya

Wani mabiyin mazhabar Shi'a a Najeriya da aka fi sani da Islamic Movement of Nigeria, IMN karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky, ya ce ba za su taba mantawa da 'rashin adalcin' da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi musu ba dangane da al'amarin da ya faru tsakaninsu da sojoji a Zariya.

Ahmad Bawa Jalam ya ce da shi da sauran mabiya jagoran IMN ba za su gushe ba face suna addu'ar neman sakayya daga Ubangiji.

A ranar 10 ga watan Disambar 2015 ne dai sojojin suka yi zargin almajiran Sheikh Zakzaky da tsare wa babban hafsan sojin kasar, Janar Yusuf Tukur Buratai hanya da kuma kokarin hallaka shi.

Bayan nan ne kuma sojojin suka far wa gidan shugaban na IMN, sheikh Elzakzaky bisa dalilan bayanan sirri da suka samu da ke nuna mabiya mazhabar ta Shi'a na shirin daukar matakin kai hare-hare, al'amarin da ya janyo kisan mabiya mazhabar da dama sannan kuma aka kama shugaban kungiyar da har yanzu ke tsare a hannun gwamnati.

Sojojin dai sun ce mutum takwas ne suka mutu sakamakon samamen, a inda bakwai daga ciki 'yan Shi'a ne sannan kuma guda daya soja.

Sai dai kungiyar IMN ta musanta alkaluman a inda da farko ta ce an kashe mata 'ya'ya fiye da 500 sannan kuma daga bisani ta ce an kashe kusan mutum dubu daya.

To amma wani kwamitin bin bahasin hakikanin abin da ya faru da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya gano abubuwa da dama da suka hada da kisa da binne mabiya mazhabar ta Shi'a 347 a asirce.

Wannan ne ya sa mabiya jagoran na IMN, kamar Ahmad Bawa Jalam ke ganin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ba zai taba kubuta daga zarginsu ba.

Ku saurari hirar na yi da Ahmad Jalam:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ahmad Bawa Jalam, wani almajirin Sheikh Elzakzaky

Matsayin kotu kan Elzakzaky

A watan Disamban 2016, wata babbar kotu a Abuja ta nemi gwamnati ta saki Elzakzaky da matarsa tare da biyan sa diyya sannan kuma a gina masa gida, a duk garin da yake so a arewacin kasar, duk a cikin kwanaki 45.

To amma har yanzu gwamnati na ci gaba da tsare Elzakzakyn bisa wasu dalilai da ministan Shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya ce ta dogara da su.

"Idan irin wannan ya faru a kan rinjayar da bukatar al'umma fiye da ta mutum guda," in ji Malami.

Ya kara da cewa "Idan an bayar da oda ko kuma hukunci, ya zama an daukaka kara akwai bukata wadda doka ta amince da ita na ainihin wanda bai gamsu ba ya nemi dakatar da zartar da hukunci."

Ga dai yadda hirar tasa ta kasance da Editanmu na Abuja, Naziru Mika'ilu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami

Da man dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ba za su saki jagoran IMN ba duk da kotu ta ce a sake shi, bisa dalilan shari'a da na tsaro.

Me lauyoyi ke cewa?

Masana shari'a da dama dai na ganin ya kamata gwamnati ta yi adalci sannan kuma ta girmama kundin tsarin mulki sannan su kuma mabiya Shi'a su yi hakuri su bi doka tunda dai gwamnati ta ce za ta kalubalanci hukuncin kotu.

Barista Sunusi Musa, wani lauya mai zaman kansa a Najeriya ya ce, "Tunda dai gwamnati ta ce za ta daukaka kara sannan kuma ta gindaya batun tsaro, lallai ya kamata mabiya Shi'a su kwantar da hankalinsu su ci gaba da neman hakkinsu ta hanyar tsarin dokar kasa."

Sai dai kuma Barista Sunusi ya kara da cewa, "Ni a ra'ayina zan so a ce an saki Elzakzaky domin bin umarnin kotu."

"Wani lokacin akwai bukatar gyara a harkar shari'ar Najeriya saboda bai kamata a ce kotu ta bayar da umarni ba amma a ki bin sa," in ji Sunusi Musa.

Matsayin kungiyoyin 'yancin dan adam

Kungiyoyi masu fafutukar kare 'yancin dan adam a Najeriya da ketare kamar Amnesty International sun fito balo-balo suna zargin gwamnatin Najeriya da rashin mutunta 'yancin mabiya Shi'a.

Da man dai kungiyar Amnesty International ce ta fara fadin cewa ta gano wurin da aka binne 'yan Shi'ar da aka kashe a Zariya, a asirce.

A har ko yaushe kuma kungiyar tana ci gaba da sukar ci gaba da tsare shugaban IMN, Ibrahim Elzakzaky ba tare da gurfanar da shi a gaban kuliya ba domin ya fuskanci hukunci.

A baya-bayan nan ne kuma aka kara samun wasu kungiyoyin masu rajin kare hakkin dan adam da ke cikin Najeriya kamar Concerned Citezens suka yi ta gudanar da zanga-zanga iri-iri tare da mabiya Shi'a domin neman a saki Elzakzaky.

Zanga-zangar neman sakin Elzakzaky

Image caption Zanga-zangar Shi'a a Najeriya

Tun dai kama da tsare jagoransu a watan Disambar 2015, mabiya mazhabar Shi'a suke ta fama gudanar da taruka da zanga-zanga iri-iri domin a bi musu kadinsu da kuma sakin shugabansu da ma sauran 'yan kungiyar da suka yi zargin suna tsare.

Ma fi yawancin lokuta dai 'yan Shi'ar na haduwa da fushin jami'an tsaro a inda suke tarwatsa su bisa dalilin cewa 'yan Shi'ar ba sa neman izinin hukuma.

Sannan kuma suna shiga hakkin mutane ta hanyar tsare hanyoyi ga matafiya.

To amma Barista Sunusi Musa ya ce, "Duk da cewa ko wane dan Najeriya yana da hakkin gudanar da taro ko nuna damuwarsa ga wani abu idan dai har ba zai karya doka ba ko kuma ya take hakkin wani, ya kamata 'yan Shi'a su rinka sanar da jami'an tsaro kafin gudanar da zanga-zanga domin jami'an tsaron su ba su kariya."

Sai dai mai magana da yawun IMN, Ibrahim Musa ya ce, "Babu inda aka ce sai ka shaida wa jami'an tsaro za ka gudanar da taro ko zanga-zanga."

Ya kuma ce, "Batun a ce muna tare hanya wannan kuma ba haka ba ne kawai dai makiyanmu ne suke fada domin samun abin da za su soke mu da shi."

A baya dai shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira ga jami'an tsaron kasar da su yi taka-tsan-tsan wajen dakile ayyukan 'yan Shi'a.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga-zangar neman a saki Elzakzaky a kasashen waje

Gwamnatin jihar Kaduna da IMN

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bin bahasin hakikanin abun da ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya kasancewar garin na karkashin jihar.

Kwamitin kuma ya gano abubuwa da dama da suka hada da kisa da binne mabiya mazhabar Shi'a 347 a wasu wawaka-wawakan ramuka na bai daya.

Sannan kuma ya bayar da shawarwari masu yawa kan yadda za a guji afkuwar irin rikicin a gaba.

Shawarwarin dai sun hada da hukunta jami'an tsaron da suka aiwatar da kisan 'yan Shi'a a Zariyar da haramta kungiyar 'yan uwa musulmi ta IMN tare kuma da hukunta shugabanta, Elzakzaky.

Tuni kuma gwamnatin jihar ta haramta gudanar da ayyukan kungiyar sannan ta sha alwashin hukunta Elzakzaky, kamar yadda a baya-bayan nan gwamna Nasir Elrufa'I ya shaida wa wata kafar talbijin a Najeriyar cewa, "Muna jira gwamnatin tarayya ta miko mana Elzakzaky domin mu samu mu gurfanar da shi a gaban kotu."

To sai dai har kawo yanzu gwamnatin ba ta aiwatar da shawarar hukunta sojojin da suka kashe 'yan Shi'ar ba kamar yadda kwamitin ya bukata.

Hakan ne ya sa lauyan Elzakzaky, Femi Falana ya nemi da gwamnatin ta jihar Kaduna da hukunta jami'an tsaron.

A wata sanarwa da ya aike wa da BBC, Mista Falana ya ce, "Dole ne a hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kisan Zariya, idan kuma ba haka ba to za su gurfanar da su a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC."

Ya ya za a warware rikicin Shi'a da gwamnati?

Masana a fannin shari'a kamar Barista Sunusi Musa na ganin za a iya shawo kan rikicin gwamnati da 'yan Shi'a ta hanya biyu:

  • Sulhu
  • Shari'a

Dangane da sulhu, Barista Sunusi Musa ya ce, "Gwamnati za ta iya zama da Elzakzaky da mabiyansa a tattauna, kamar yadda aka yi da tsagerun Naija Delta. Idan abin ya kama a bayar da diyya sai gwamnati ta bayar tun da mun ga yadda aka yi kan kisan sirikin shugaban Boko Haram, Muhammadu Yusuf, a inda gwamnatin jihar Borno ta bayar da diyyar naira miliyan dari."

To amma Sunusi ya kara da cewa, "Ita ma gwamnati za ta iya zayyana wa jagoran Shi'ar irin bukatunta sannan dole ne Elzakzaky da mutanensa su martaba dokar kasa."

Abin kuma da ya shafi shari'a, Barista Sunusi ya ce, "Idan har sulhun bai yiwu ba sai a je ga matakin gurfanarwa a gaban kotu, idan kotu ta same shi da laifi ta hukunta shi, idan kuma ba shi da laifi ta sake shi."

Illar rikicin Shi'a da gwamnati ga tsaron kasa

Masana harkar tsaro a Najeriya sun ce idan dai har ba a bi matakan da masana shari'a suka zayyana ba wajen warware takaddamar Shi'a da gwamnati, to fa kasar za ta fada cikin wani hali.

Dr. Kabiru Adamu, wani masanin tsaro ne a Najeriya kuma ya zayyana matsalolin da Najeriya za ta iya fadawa idan har rikicin Shi'a da gwamnati ya ci gaba da wakana:

  • "Idan Elzakzaky ya mutu a hannun gwamnati, babu makawa 'yan Shi'a za su ce gwamnati ce ta kashe shi saboda haka Allah kadai ya san abun da zai faru."
  • "Rashin magance wannan rikici zai iya janyo mummunan rikicin banbancin akida tsakanin Shi'a da Sunna kamar yadda ake gani a wasu kasashen gabas ta tsakiya."
  • "Al'amarin zai iya sanya wasu kungiyoyin addini su fara shirin kare kai, kafin gwamnati ta zo kansu su ma."

Abin da 'yan Shi'a ke bukata

Mai magana da yawun Islamic Movement of Nigeria, Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa, "Muna da bukatu da yawa amma dai babbar bukatarmu yanzu haka ita ce a saki jagoranmu, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa da sauran 'yan uwan da ake tsare da su", a inda ya ci gaba da fadin, "alabashi idan aka sake shi to sauran bukatun shi ya san yadda za a yi da su."

Sharhi

Masana a fannin shari'a da tsaro dai sun daki jaki da kuma taiki kan rikici tsakanin 'yan shi'a da gwamnati.

Yayin da Dr Kabiru Adamu ya ke ganin, "Najeriya ta yi amfani da karfi fiye da kima wajen dakile ayyukan tsirarun mabiya Shi'a", shi kuwa Barista Sunusi Musa ya ce, "Dole ne 'yan Shi'a su san cewa bin doka dole ne a matsayinsu na 'yan Najeriya."

Sai dai kuma Barista Sunusi ya kara da cewa, "Gwamnatin Najeriya ita ma ya kamata ta san cewa 'yan Shi'a suna da 'yancin yin addinin da suka ga dama."

Image caption Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya kira Buhari kan kama Elzakzaky

A yanzu dai a iya cewa, al'ummar kasar ta zura ido ne don ganin ya ya za ta kaya tsakanin gwamnati da kungiyar IMN kan batun sakin jagoran nasu da sauran 'yan uwansu da aka kama, musamman a daidai wannan lokaci da Shugaba BUhari ya cika shekara biyu a kan mulkin kasar.

Labarai masu alaka