'Matar da ta kashe 'ya'yanta takwas ba ta da laifi'

Police officers at the crime scene where the eight children were found dead Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun garzaya inda aka samu yaran takwas a mace

Wata mata 'yar Australiya wadda ta kashe yara takwas ta hanyar chaka musu wuka a gidanta, ba za ta fuskanci shari'a ba saboda an gano cewa ba ta cikin hayyacinta a lokacin.

Raina Thaiday ta fice daga hayyacinta a lokacin da ta far wa 'ya'yanta maza hudu da mata uku da kuma 'yar dan uwanta daya a watan Disambar 2014.

Hukuncin - wanda aka yanke a watan da ya gabata, amman sai yanzu aka bayyanashi - yana nufin ba za a iya dora mata alhakin laifin ba.

Ana tsare da Thaiday, mai shekara 40, a sansanin Brisbane mai tsananin tsaro.

Babu tabbacin in za a sake ta ta koma cikin jama'a.

An rusa gidan aka kashe yaran, wadanda ke da shekaru tsakanin biyu zuwa sha hudu. An maye gurbin gidan da wani wurin tunawa da yaran Malili da Angelina da Shantae da Rayden da Azariah da Daniel da Rodney da kuma Patrenella.

'Mafarkin zaunemafi tsanani'

An tuhumi Thaiday, wadda aka sani da Mersane Warria, da laifin kashe yaran, amman kotun masu tabin hankalin ta Queensland ta yanke hukuncin cewar ba za a mata shari'a ba.

Kwararru sun ce kafin a yi kashe-kashen ba a taba yi mata maganin tabin hankali ba.

Wasu likitocin tabin hankali sun bayar da shaidar cewar mai yiwuwa lafiyar hankalin Thaidayya tabarbare watanni kafin aukuwar lamarin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashe-kashen sun girgiza alu'ummar Cairns
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane sun tsaya a bakin titi lokacin da ayarin garwawakin ke wucewa.

Thaiday ta yi imanin cewar ita ce 'zababbiya' kuma ta damu matuka da tsaftace kanta domin kare kanta da kuma iyalinta daga aljanu.

Wani kira - na gaske ko na tunani- shi ya tunzura ta.

Wata likita mai bincike kan tabin hankali, Jane Phillips, ta sanar da kotu cewar: "Ta ji sautin wata tsuntsuwa kuma ta yi imanin cewar daga jin sautin sako ne da ke cewar dole ta kashe yaran domin ta cece su."

Likitan tabin hankali, Frank Varghese, ya ce Thaiday tana fama da cutar mafarkin zaune na tashin duniya ne.

Ya ce: "Wannan wata irin cuta ce ta daban mai ban tsoro, irin wadda ban taba gani ba."

"Wannan cutar mafarkin zaune ne mafi zurfi da tsanani."

'Tabin hankali'

Babban dan Thaiday, Lewis Warria, shi ne ya samu gawarwakin. Kuma ya samu mamansa a gaban gidan da wurare 35 da ta caka wa kanta wuka.

Mai shari'a, Jean Dalton, ta ce kwararan hujjojin da ke nuna cewar Thaiday ba za ta iya iko kan ko kuma gane abubuwan da ta yi ba.

"Misis Thaiday ta samu wani tabin hankalin da ya hana ta mallakar kanta a lokacin da ta aiwatar da kashe-kashen ," in ji mai shari'a Dalton.

"Wannan na nuna cewar babu shakka a kan hakan bisa hujja da kuma hukuncin shari'a da ke cewa tana da kariyar tabin hankali."

Labarai masu alaka

Karin bayani