Maiduguri: An daure 'barayin' shinkafar 'yan gudun hijira

Gudun hiriar Boko Haram Hakkin mallakar hoto .
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin 'yan Najeriya da muhallansu inda suke rayuwa a sansani da tallafin abinci daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya, na cewa an daure wasu jami'ai biyu na kananan hukumomi bayan an same su da laifin satar shinkafar 'yan gudun hijira.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwato cewar wata babbar kotu ce a brinin na Maiduguri ta yanke wa mai'akatan kananan hukumomin hukuncin zaman gidan kaso na shekara biyu da tarar Naira miliyan daya ko wannensu saboda sun yi sama da fadi da buhun shinkara 180.

Mai shari'a Fadawu Umar ya same su da laifi a tuhuma ukun da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta yi musu a lokacin da ta gurfanar da su a gaban kotun.

Jaridar intanet ta Preimum Times ta ce sunan wadanda aka dauren ne Umar Ibrahim da Ali Zangebe.

Labarai masu alaka