Kotu ta tura Bala Mohammed zaman waƙafi

Ana zarginsa da karbar cin hancin N550 million, zargin da ya musanta.
Bayanan hoto,

Ana zarginsa da karbar cin hancin N550 million, zargin da ya musanta.

Wata babbar kotun Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta tura tsohon ministan birnin Bala Mohammed zaman gidan wakafi a gidan yarin Kuje saboda zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya a kan zarge-zarge shida da suka shafi cin hanci a lokacin da yake kan mulki.

Ana zarginsa da karbar cin hancin N550 million, zargin da ya musanta.

Kazalika ana zargin Bala Mohammed da laifin kin bayyana yawan kadarorin da ya mallaka.

Tsohon ministan ya ce ba shi da laifi.

Alkalin kotun Abubakar Talba ya dage zamanta zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan belinsa.

Daga nan ne ya umarci a kai Bala Mohammed zaman gidan wakafi a gidan yarin Kuje.