Mene ne ya fusata ASUU ta soma yajin aikin sai baba-ta-gani?

Bayero University Kano Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ranar Lahadi 13 ga watan Agusta, Malaman jami'a a Najeriya suka fara yajin aiki a dukkan jami'o'i mallakin gwamnati.

Malaman sun yi haka ne a karkashin kungiyarsu ta malaman jami'o'i, ASUU, inda shugaban kungiyar, Biodun Ogunyemi, ya bayyana wa maneman labarai wannan matakin nasu.

Kuma kungiyar ta ce ta yanke wannan shawarar ce bayan da ta tattaro ra'ayoyin mambobinta da ke dukkan jami'o'in kasar, inda ta sha alwashin daina koyarwa da shirya jarrabawa, da kuma halartar dukkan tarurrukan da suka shafi koyarwa.

Ko mene ne dalilin daukar wannan matakin na yajin aiki da kugiyar malaman ASUU ta fara a wannan lokacin?

Kungiyar ta fitar da wasu korafe-korafe guda shida da ta ce su ne dalilanta na bazama wannan yajin aiki na sai-baba-ta-gani.

1. Rashin biyan albashi ko bangaren albashi

ASUU ta koka da yadda ta ce gwamnatocin kasar ke kasa cika alkawurran biyan malaman jami'a albashinsu na wata-wata akan lokaci.

Kuma a wasu jihohin kasar, gwamnatin kan biya jami'an rabin albashin malaman ne.

2. Kudaden alawus

Wannan batun ya shafi wasu alawus-alawus da ake biyan malaman jami'a ne idan sun yi wasu ayyukan koyarwa da suka wuce na ka'ida.

Misali, wasu malamai kan koyar da daruruwan dalibai, wasu kuma su kan dauki adadin ajujuwan da suka zarce wadanda aikinsu ya bukata domin yawan daliban.

3. Batun Fansho

Malaman jami'o'i na bukatar gwamnatin Najeriya ta cire su daga tsarin fansho na kasa, kuma a mayar da su karkashin wani shiri na musamman wanda malamai ne kawai ke cikinsa.

Kawo yanzu, gwamnatin tarayya ba ta amince da wannan bukatar tasu ba.

4. Alawus ga Farfesoshi

Akwai wata yarjejeniya tsakanin ASUU da gwamnati da suka kulla a shekarar 2009 game da wasu kudaden alawus da za a rika biyan farfesoshin da suka kai shekara 10 suna koyarwa bayan sun zama farfesa.

ASUUn ta koka da cewa ba a biyan wadannan kudaden ga farfesoshin da suka cancanta.

5. Ilimin 'ya'yan malaman jami'a

ASUU ta ce gwamnati ta janye hannayenta daga tallafa wa makarantun firamare da na sakandare da ke cikin jami'o'i.

A da gwamnati kan bayar da wasu kudade na musamman ga wadannan makarantun, inda yawancin 'ya'yan malaman jami'a ke halartar azuzuwan karatu.

6. Tsarin NEEDS na tallafa wa jami'o'in Najeriya

Gwamnatin tsohon shugaba Obasanjo ta fitar da wani shiri na tallafa wa ilimin jami'a ta hanyar zuba naira triliyan daya domin inganta yanayin koyarwa a jami'o'in kasar.

ASUU ta ce tun wancan lokacin gwamnati ta watsar da batun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Abin da gwamnati ke cewa

Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya kare gwamnati daga zargin yi wa ilimin jami'a rikon sakainar kashi.

Ya kuma ce yana fatan wannan yajin aikin ba zai zarce na kwana biyu ba.

A wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Guardian a birnin Abuja, ministan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce kawai ke da tsarin fuskantar matsalolin da suke damun kungiyoyin ma'aikata, wanda ya hada da ASUU, ba kamar gwamnatocin da suka gabace su ba.

Ministan ya kuma ce a watan Janairun da ya gabata, ya kaddamar da wani kwamitin mutum 16 domin sake duba yadda za a gudanar da yarjejeniyar da ke tsakanin gwamnati da ASUUn na shekarar 2009.

Shi wannan kwamitin da ministan ya ambato, zai tattauna da kungiyar ASUU da wasu kungiyoyin malamai da lamarin ya shafa domin kawo kwanciyar hankali a cikin manyan makarantun kasar.

Har ia yau, ministan ya ce gwamnati ta tashi tsaye domin magance matsalar yawan yajin aiki da rufe jami'o'in kasar, inda ya ce, "Ina fatan wannan yajin aikin ba zai wuce na kwana daya ko biyu ba.

Wannan ne karon farko cikin shekara biyu da ASUU ta tafi yajin aiki."


Yadda yajin aikin ya shafi karatun jami'a

Yawancin mutane sun fahimci cewar yajin aiki zai shafi malamai da dalibai ne kawai. Amma batun ya wuce haka, domin iyayen yaran da sauran ma'aikatan jami'o'in ma suna fuskantar cikasa cikin al'amuransu.

A misali, iyayen daliban na kokawa da yadda yajin aikin ke shafarsu, suna cewa 'ya'yansu kan zama musu kayan wanki har sai an koma makaranta. Su kuma ma'aikatan jami'ar da basa koyarwa suna kokawa da yadda ayyukansu ke tsayawa cik duk da cewa su basa yajin aiki.

Batun jarabawa ma yana cikin abubuwan da kan jawo cikas musamman ga dalibai. A halin da ake ciki, yawancin daliban jami'o'in kasar sun shirya tsaf domin fukantar jarabawa, kafin kwatsam suka ji an fara yajin aikin.

"Bamu ji dadin wannan yajin aikin ba, domin mun zage mun yi karatu kawi sai muka ji an fara yajin aiki", inji Salim Sani, wani dalibi dake karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Kowa ya san cewa akwai dalibai 'yan asalin Najeriya a kasashen Afirka da Turai da kuma kasashen Asiya wadanda suka tafi can domin neman ilimi. Daga Uganda zuwa Malaysia da Ghana da China zaka taras da dubban 'yan kasar suna karatu.

Hatsarin wannan shi ne Najeriya na asarar kudade masu yawa domin biya wa 'yan kasar kudaden makaranta a can.

Wannan lamarin ba a kan iyaye kawai ya tsaya ba, domin gwamnatocin jihohin Najeriya da dama kan tura wasu daga cikin dalibansu zuwa kasashen waje domin yin karatu.

A misali, jihar Kaduna ta tura dalibanta da yawa zuwa Uganda domin yin karatun likita, bayan tana da jami'a mallakinta a Kaduna wacce ta shiga sahun jami'o'in dake wannan yajin aikin.

Jihar Kano ma ta tura dalibai da yawa zuwa Masar domin karo ilimi, bayan tana da jami'o'i biyu wadanda ke bukatar a inganta su wajen samar da kayan aiki ga malamai da daliban dake karatu a can.

Batutuwa masu tasowa

Baban sakataren kungiyar shugabannin jami'o'in Najeriya, Farfesa Michael Faborede, ya bayyana cewa wannan yajin aikin ya taso ne sabili da "rashin daukar matakan da suka kamata da kuma rikon sakainar kashin da wannan gwamnatin ta ke yi game da halin da ilimi yake ciki tun daga matakin firamare zuwa na jami'a."

Faborode ya kara da cewa tun bayan wani kokari da aka yi na sake duba tsarin nan na NEEDS a shekarar 2012, inda aka gano yadda lamarin ilimi ke kara tabarbarewa, babu wani mataki da gwamnatocin da da na yanzu suka dauka game da gwara lamarin.

Malaman jam'ia sun koka cewa tun shekarar 2013 da gwamnatin Najeriya ta bai wa jami'o'in kasar Naira biliyan 200 cikin Naira Tiriliyan daya da tayi alkwarin bayarwa, gwamnatin ta yi watsi da lamarin mutanen duk da cewa sun tafi wani yajin aiki a lokacin.

Kuma sun tuhumi gwamnatin da bada fifiko ga bude sabbin jami'o'i a kasar maimakon tallafa wa wadanda suka dade da kafuwa.

Amma Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige, ya tuhumi kungiyar ASUU da kin bin dokokin kasa wajen neman hakkokinsu a wajen gwamnati. Ya ce sashe na 41 na dokar kwadago ta shekarar 2004 kasa ya bukaci a ba da wa'adin kwana 15 kafin wata kungiya ta fara yajin aiki.

Wasu masu nazari suna cewa idan bera na da sata, daddawa ma na da wari. Suna ganin lallai ASUU bata bi dukkan ka'idojin da doka ta tanadar ba kafin tafiya wannan yajin aikin. A misali, shugaban ASUU na kasa, ya bayyana kudurinsu na fara yajin aiki ne bayan kwana daya cur da fara yajin aikin, ba kamar yadda doka ta tanada ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ina mafita?

Ban da kotuna na musamman da aka tanadar domin sasantawa tsakanin ma'aikata da masu daukan ma'aikata, akwai kungiyoyin kasa-da-kasa kamar hukumar kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya, ILO wacce ita ma ta samar da wasu hanyoyi da kasashe ya kamata su bi wajen sasantawa idan matsalolin kwadago sun taso.

Cikin hanyoyin da hukumar ILO ta tanadar akwai na hawa teburin tattaunawa kafin a dauki duk wani mataki kamar na shigar da kara a kotu.

Wasu masana sun soki yadda gwamnatin Najeriya ke yin gum idan irin wannan lamarin ya faru, inda suke ganin ya kamata da ta rika ilmantar da jama'a game da shirinta da tanade-tanaden da tayi game da al'amari mai muhimmanci kamar wannan na ilimi.

Suna ganin ta wannan hanyar ma wasu malaman zasu iya fahimtar inda gwamnatin ta nufa har ma su iya mata uzuri.

Wasu kuma na ganin cewa ita ma kungiyar malaman jami'ar, ASUU tana da nata laifin, domin shuwagabanninta basa ba mambobinsu damar samun bayanin ainihin lamarin da ake ciki.

Wani malami a jami'ar Bayero ya ce shugaban ASUU ne kawai zai iya magana akan batun yajin aikin. Kuma da alama babu tsarin demokradiyya a yadda ake gudanar da harkokin kungiyar, inda wasu rahotanni ke nuna cewa wasu rassa na kungiyar ta ASUU a wasu jihohi na tunanin janyewa daga yajin aikin.

Mayar da ruwa rijiya

A karshe, 'yan Najeriya da dama sun koka da yadda yajin aiki ya zama ruwan dare gama duniya a halin kasashen da basu kai Najeriyar ba ne ke cin gajiyar wannan lamarin.

Daga kasar Benin zuwa Ghana har zuwa Sudan zaka taras da daruruwan daliban Najeriya suna karatu domin a can babau irin wannan takaddamar ta yankewan karatu.

Huzaifa Aliyu, wani dalibi ne dake karatu a Jamhuriyyar Benin, wacce makwabciyar kasa ce ga Najeriya.

Ya bayyana takaicinsa ga yadda tilasta masa ya bar Najeriya zuwa kasar ta Benin domin neman ilimi, lamarin da ya ce tamkar mayar da ruwa rijiya ne.

"Jami'o'in Benin ba su kai na Najeriya ba, kuma ingancin ilimin bai taka kara ya kai ba, amma dole ta sa mun taho nan. Dalilina bai wuce samun tabbacin cewa zan gama karatuna na jami'a cikin lokacin da aka kayyade ba.

Yanzu kaga sauran shekara guda na kammala karatuna a nan, amma ka ga a Najeriya tsarorina na iya kwashe shekara biyar ko shida kafin su kammala karatun digiri na shekara uku."

Labarai masu alaka