Adnan bin Mahmoud Bostaji: Jakadan Saudiyya a Najeriya ya rasu

Asalin hoton, AFP
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyar rasuwar jakadan Saudiyya a Najeriya, Adnan Mahmoud, ga Sarki Salman na Saudiyya, inda ya bayyana ta da "rashin babban aboki ga Najeriya".
Buhari ya ce jakadan yana daya daga cikin wakilai mafiya kwazo da ya taba yin aiki da su, a cewar mai magana da yawun fadar shugaban kasa malam Garba Shehu.
A ranar Talata ne ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya bayar da sanarwar mutuwar Ambasada Adnan bin Mahmoud Bostaji.
Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin bayani a kan abin da ya janyo mutuwar tasa ba.
Shugaba Buhari ya ce: "Jakadan ya sadaukar da rayuwarsa wurin gina alaka mai amfani tsakanin kasarsa da Najeriya.
"Saboda haka ba za mu iya mantawa da irin gudummawar da ya bayar ba game da yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu.
"A madadina da iyalina da gwamnatin Najeriya, ina mika ta'aziyya ga Mai Martaba Sarki Salman da kuma gwamnatin Saudiyya bisa wannan mummunan rashi."
Ambasada Adnan Mahmoud ya soma aiki da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya a shekarar 1991, a wannan shekara ne kuma aka nada shi a matsayin jakadan Saudiyya a Tehran wato babban birnin Iran, inda ya ci gaba da aiki har zuwa 1998.
Ya kuma taba zama wakili a majalisar hada kan kasashen Gabas Ta Tsakiya tun daga 1998 har zuwa 2000.
Ya zama jakadan Saudiyya a Denmark daga 2000 zuwa 2013, kafin daga bisani ya zama shugaban sashen kula da tattalin arziki na ofishin jakadancin Saudiyya a Landan daga 2003 zuwa 2005.
Daga bisani ya zama mataimakin jakadan Saudiyya a Landan har zuwa lokacin da aka sanar da shi a matsayin jakadan Saudiyya a Najeriya.