Shari’ar fyaden da Zainab Bulkachuwa ba za ta manta da ita ba

Bayanan bidiyo,

Kotu na yi wa wadanda aka yi wa fyade rashin adalci- Bulkachuwa

A yayin da ake shirin bikin Ranar Mata Ta Duniya, a Najeriya wata gwarzuwar mace ce ta yi ritaya daga aiki bayan shafe shekara 43 a fannin shari'a na kasar.

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa, ita ce mace ta farko da ta shugabanci Kotun Daukaka Kara a kasar, kuma ta sahida wa BBC cewa ba ta taba yanke hukuncin kisa ba a tsawon wadannan shekaru.

Kafin rike wannan matsayi, ta yi aiki a bangarorin shari'a daban-daban tare da rike mukamai da dama a jihohi da ma gwamnatin tarayya.

Sai dai a lokacin da ta cika shekara 70 a duniya ranar 6 ga watan Maris din 2020, a wannan lokacin ne kuma take ajiye aiki, amma kamar yadda aka sani, tafiya irin wannan na cike da dumbin nasarori da kalubale.

A wata hira ta musamman da Sashen Hausa na BBC kwanaki kadan kafin ritayar tata, Mai Shari'a Bulkachuwa ta bayyana mana irin matakan da ta hau masu dadi da masu tsauri, tare da fadin abin da za ta sa a gaba bayan ajiye aiki.

Shari'un da ba za ta manta da su ba

A tsawon lokacin da ta dauka tana aiki, Mai Shari'a Bulkachuwa ta yi shari'o'in da ita kanta ba ta san yawansu ba kamar yadda ta shaida mana, tun daga kotun majistare har zuwa ta Daukaka Kara a tarayya.

Asalin hoton, Court Of Appeal Facebook

Bayanan hoto,

Mutane da dama na yi mata kallon mace mai tsauri kuma mara son wargi, musamman yayin da take kotu

Sannan shari'a ta karshe da ta jagoranta ita ce wacce ta yi a shekarar 2019 a kan ikon da Majalisar Dokokin kasar take da shi kan yin dokokin zabe.

Ta ce: ''An kawo mani karar ne kafin daftarin ya zama doka, don haka sai da na zauna na fayyace yadda ya kamata a bi da dokokin da za a bi.''

Amma akwai wasu muhimman shari'o'i da ita Mai Shari'ar ta ce su ne wadanda suka fi tsaya mata a rai tsawon lokacin da take aiki, kuma ba za ta manta da su ba.

Ta ce cikin manyan shari'o'in da ta jagoranta da ba za ta manta da su ba, har da shari'ar tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark a 2008.

Akwai kuma shari'ar tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye a 2007, wacce mutum takwas daga majalisar dokokin jihar suka tsige shi, "amma na yanke hukunci cewa basu bi doka da tsari ba don haka abin da suka yin bai tabbata ba," in ji ta.

Cour Of Appeal
A ganina mafi yawancin shari'o'in fyade ana yi wa mata rashin adalci sosai.
Justice Zainab Bulkachuwa
Mace ta farko da ta shugabanci Kotun Daukaka Kara Ta Najeriya
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai babbar shari'ar da Bulkachuwa ta ce ta tsaya a kokon ranta ita ce ta wata yarinya da aka yi wa fyade a lokacin tana babbar mai shari'a ta Babbar Kotu a Bauchi.

Ta ce: "Shi wanda ya yi wa yarinyar fyaden wani matashin lauya ne, kuma na tabbatar da laifi a kansa har ma na yanke masa hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari.

"Daga nan ya daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara a Jos a lokacin Mai Shari'a Maryam Alooma na kotun; ita ma ta kara tabbatar da hukuncin nawa.

''Amma da aka kai batun Kotun Koli - da yake lokacin duk maza ne a wajen - sai suka ce a'a, ai don mu mata ne shi ya sa muke tausayin yarinyar amma ya kamata a duba lamarin lauyan tun da yaro ne, hukuncin na iya katse masa burinsa na daukaka a aikinsa.

"To gaskiya wannan abu ya kada ni sosai.

"Don haka a ganina, mafi yawancin shari'o'in fyade ana yi wa matan rashin adalci sosai, saboda rashin isassun shaidu ko rashin zuwa asibiti, da cewar yawanci lauyoyin da ke shari'ar fyade maza ne da kuma tsoron kyama da iyaye ke yi."

Ko Zainab Bulkachuwa ta taba yanke hukuncin kisa?

Da zarar mutum ya ji yawan shekarun da Mai Shari'a Bulkachuwa ta shafe tana aiki zai iya yin tambayar "ko a irin hukunce-hukunce da ta sha yankewa ta taba yanke na kisa?"

"Gaskiya a duk tsawon shekarun nan ban taba yanke hukuncin kisa ba. Iyaka dai da na zo Kotun Daukaka Kara nakan tabbatar da hukuncin idan an yanke a wata kotun, kuma ni ma shari'ata ta nuna haka din ne.

"Amma a Babbar Kotu kam ban taba ba gaskiya," in ji Bulkachuwa.

'Ba za ta yi adalci a shari'ar da ake da mijinta ba'

Alhaji Adamu Bulkachuwa - mijin mai shari'a Zainab Bulkachuwa - ya tsaya takarar neman kujerar dan majalisar dattawa a yankin Bauchi Ta Arewa a zabukan 2019, a jam'iyyar APC.

Bayan kammala zabukan 2019, an kafa kwamiti na sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, inda aka sa ta jagoranta, sai dai jim kadan da yin hakan ta sanar da murabus dinta.

Hakan ya faru ne bayan ce-ce-ku-cen da mutane suka yi ta yi ne, musamman 'yan bangaren jam'iyyar adawa ta PDP, cewar ba za ta yi adalci a lamarin ba kasancewar mijinta dan APC ne.

Ta bayyana mana cewa ta janye daga shari'ar ne saboda kokwanton da aka dasa mata a ranta, tana mai cewa "na jagoranci abin da zuciya daya amma da aka kawo korafi cewa mijina dan siysasa ne sai kawai na ga dacewar sauka [daga shari'ar] don kokwanton nan da aka sa.

"Amma da ba a yi haka ba ko dar ba zan ji ba, kuma zan jagoranci shari'ar tsakanina da Allah ba nuna bambanci kamar yadda na saba."

Asalin hoton, Court Of Appeal

Rayuwar Zainab Bulkachuwa a takaice

 • An haife ta ranar 6 ga watan Maris din 1950 a Bauchi
 • 'Yar asalin garin Nafada ne a jihar Gombe
 • Ta fara karatun firamare a Kaduna a 1957
 • Ta yi sakandare a Queen Elizabeth da ke Ilorin daga 1961 zuwa 1968
 • Ta kammala karatun koyon shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya a 1975
 • Makarantar Koyon Aikin Shari'a a 1976
 • Hidimar kasa a Kaduna a 1976
 • Ta zama Cif Majistare a 1985, sannan ta tafi Babbar Kotu a 1987
 • Babbar Mai Shari'a ta Babbar Kotun Gombe a 1997
 • A 1998 kuma ta zama mai shari'a a Kotun Daukaka Kara a Abuja
 • Sai a 2014 kuma aka nada ta shugabar Kotun Daukaka Karar
 • Ta sha karbar lambobin yabo kuma ta yi kwasa-kwasai da dama, sannan ta sha jagorantar kwamitin sauraron kararrakin zabe
 • Sunan mahaifinta Alhaji ABubakar Gidado El-Nafaty, mijinta kuma Sanata Adamu Bulkachuwa
 • Tana da aure da 'ya'ya shida.

Mace mai jawo ce-ce-ku-ce

Da zarar an ambaci Mai Shari'a Bulkachuwa abin da ke zuwa ran mutane da dama shi ne mace ce mai yawan jawo ce-ce-ku-ce.

Sai dai ta ce ambatar sunanta da ake yawan yi da alakanta ta da wasu abubuwa ba sa daga mata hankali, "don na san duk abin da na yi a kan hanya yake.

"Amma a gaskiya abin da ake yi din bai kamata ba, kuma mu ana hana mu mayar da martani. Don idan muka ce za mu mayar da martani za a koma waje ne ana wata shari'ar daban.

Asalin hoton, Court Of Appeal Facebook

Bayanan hoto,

Justice Zainab da mijinta Sanata Adamu Bulkachuwa (daga hagu) da Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe (daga dama) a yayin take bude Kotun Daukaka Kara a jiharta dab da ritayarta

"A hannu guda kuma ga rantsuwar da muka yi ta kama kanmu, don haka ko abu bai yi mana dadi ba haka za mu daure a tafi a haka," in ji shugabar Kotun Daukaka Karar.

Mutane da dama na yi mata kallon mace mai tsauri kuma mara son wargi, musamman yayin da take kotu.

Nasarori

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta samu nasarori da yawa a shekarun da ta shafe tana aiki a fannin shari'a.

Ta fara aikin shari'a tun daga matakin kasa inda ta yi majistare da cif majistare da babbar mai shari'a ta Babbar Kotu da alkalin alkalan jiha sannan ta je Kotun Daukaka Kara a matsayin mai shari'a a can.

Ta shafe shekara 21 a kotun, amma ta zama shugabar Kotun Daukaka Karar ne bayan shekara 16 da fara aiki a can.

"Sai dai ni ina ganin wadannan nasarori ne a matsayin kaddarar rayuwata, wato yadda Allah Ya tsara min haka na bi" in ji ta.

Mai Shari'a Bulkachuwa ta ce daga cikin manyan nasarorinta a Kotun Daukaka Karar har da yadda ta hada kan alkalan kotun, "kuma na gyara musu dokokin aikinsu, yanzu suna da wasu kotuna, wajen zamansu na da kyau don su ji dadin aikin.

"Haka kuma na tarar da bangarori na kotun 16 amma yanzu zan tafi na bar musu 20," a cewar ta.

BBC
Abu daya da zan tafi da shi a zuciyata shi ne tausayin matanmu da yaranmu wadanda ba su san hakkokinsu yadda ya kamata ba.
Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa
Mace ta farko da ta fara shugabantar Kotun Daukaka Kara

Matsaloli

Baya ga nasara, a kowacce irin tafiya a kan kuma samu kishiyarta - matsala. Ta wannan bangare ma ba a bar Bulkahuwa a baya ba, domin kuwa ta ce ta yi ta cin karo da su a tsawon shekarunta na aiki.

A Kotun Daukaka Kara dai ta ce matsalolin ba su wuce "rashin ba da isassun kudi da za a yi aikin da ya kamata ba a wasu lokutan.

Wata matsalar da Mai Shari'a Bulkachuwa ta bayyana ita ce "'Yan jarida", inda ta koka cewa ba sa yi musu adalci wajen bayyana gaskiyar lamari a kansu kafin su fada.

"Sannan bai kamata lokacin da ake shari'a a dinga yada maganganu ba, ya kamata a bari sai an kammala," in ji ta.

Da na sani?

A lokacin da wasu mutanen ke barin aiki, ba a rasa su da da na sani kan wani abu da suka yi ko kuma wasu burika da ba su kammala cimma ba.

Amma ga Mai Shari'a Bulkachuwa ta ce babu wani abu da take da na sanin yin sa, babu kuma wani buri da ba ta cika ba.

"Abu daya kawai da zan tafi da shi a zuciyata shi ne tausayin matanmu da yaranmu wadanda basu san hakkokinsu yadda ya kamata ba, wadanda kuma ba a basu dama su yi abin da ya kamata."

Fatanta ga Kotun Daukaka Kara

Fatan nata bai wauce ta ga kotun ta ci gaba ta kara bunkasa ba. "Ba ni da haufi a kan alkalan da suke wajen don na san za su iya, ina so su dinga yin shari'a da gaskiya," in ji ta.

Wata kila kasancewar ta mace zai sa a yi tunanin Bulkachuwa za ta so a samu karin mata da za su rike mukami irin nata a Kotun Daukaka Karar bayan ta tafi.

Sai dai ga dukkan alamu burinta ya wuce batun cewa a samu mace don kawai tana mace, "Zan so mace ta kara hawa wannan matsayin amma idan har ta cancanta ba wai kawai don tana mace ba."

Bayan ritaya sai me?

Mai shari'ar ta ce abin da za ta sanya a gaba bayan barin ta aiki shi ne taimako tare da tallafa wa yara da mata kan yadda za a inganta rayuwarsu a kuma ba su ilimi.

Ta ce za ta kafa wata kungiya da za ta dinga aiki a karkashinta don cimma wadannan manufofi.

A bar alfahari ga jama'arta?

Asalin hoton, Court of Appeal Facebook

Bayanan hoto,

Ta bude Kotunan Daukaka Kara a jihohi da dama a Najeriya ciki har da jiharta ta Gombe

Justice Zainab Bulkachuwa na daga cikin wadanda suka yi sa'ar samun ilimi mai zurfi tun fiye da shekara 40 da suka gabata, kuma ta yi karatun shari'ar zamani ne a lokacin da ake ganin cewa irin wannan karatu 'haramun ne, kuma duk lauya dan wuta ne,' ba ma ga mata ba kawai har da mazan.

Amma a yau ta kammala aikinta ana matukar alfahari da ita, in ji da aywa daga mutanen da na ji yo ra'ayoyinsu.

Alhaji Abuabkar El-Nafaty wani tsohon babban ma'aikacin Hukumar Sadarwa Ta Najeriya ce NItel, kuma ya fito ne daga gari daya da Justice Bulkachuwa inda ya ce min: "Adda Zainabu (sunan da suka fi kiranta da shi) ta kawo ci gaba matuka a duk matakan da ta taka na aiki.

"Ta kasance abar alfahari ba ma ga 'yan Nafada ba (asalin garin da ta fito, har da jihar Gombe da Bauchi da arewacin Najeriya baki daya.

"Ta kawo tsare-tsare da dama shekarun aikinta sannan ta bude Kotunan Daukaka Kara a jihohi da dama a Najeriya a lokacin da take shugabantar wajen," in ji shi.

Alhaji Abubakar ya kara da cewa "Bamu taba jin wani abin assha a tattare da ita ba. Hakika a yau muna mata murna da fatan alheri a rayuwa ta gaba."