Shan farfesu na maganin coronavirus? Labaran karya da ake yadawa kan cutar

  • Daga Reality Check team
  • BBC News
Wata mata ana gwada yanayin zafin jikin danta a filin jirgin saman Lagos, Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yanzu haka, kasashe 33 cikin 47 da ke Afirka kudu da hamadar Sahara ne suke da na'urorin gwajin coronavirus, daga guda biyu da ake da su a watan Janairu

A yayin da coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya, haka kuma ana samun karuwar wurin watsa labaran karya kan cutar.

An samu tabbacin bullar cutar a wasu kasashen Afrika, amma hukumomin wasu kasashen na ci gaba da yaki da labaran karya kan cutar ta coronavirus.

1. Ba a bukatar aske gemu saboda tsoron cutar coronavirus

An rika watsa wani hoton zane-zane da hukumomin lafiya a Amurka suka kirkiro kan bukatar aske gemu ana cewa ya kamata masu gemun su rika askewa saboda tsoron cutar ta coronavirus.

Amma hakan ba gaskiya ba ne.

Jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriya ta buga wani labari mai take: "Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta yi kira a rika aske gemu don kauce wa kamuwa da coronavirus."

Mun kara alamar "karya" wato "false" da kuma "tsohon hoto" a kan labaran karya ko tsoffin hotunan da aka sake amfani da su.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Zane-zanen da Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka ta fitar sun nuna misalan hotuna daban-daban kan yadda mutum zai aske gashin fuskarsa da kuma irin askin da mutum bai kamata ya yi ba idan yana so ya sanya takunkumin fuska, wato respirator mask. An amince mutum ya yi aski nau'in Side Whiskers da the Zappa amma ba a yarda mutum ya yi aski nau'in Garibaldi da French Fork ba saboda ba za su bar mutum ya yi numfashi cikin yalwa ba.

Zane-zanen na gaske ne - amma an yi su ne a 2017 (kafin barkewar cutar coronavirus) ga ma'aikatan da ke sanya takunkuman da ke hana su yin numfasi sosai. Kuma sabanin labaran da aka bayar, Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka bata wallafa zane-zanen kwanan nan ba kuma bata bayar da shawara mutane su aske gemu ba.

Kafafen watsa labaran wasu kasashe sun bayar da wannan labari, inda dubban mutane suka yi ta watsa su.

Kafar watsa labaran 7News ta kasar Australia ta wallafa labari a shafinta na Twitter da ke da taken: "Yadda gemunka zai iya taimaka wa wurin yada coronavirus ba tare da ka sani ba."

Shawarar da hukumomin lafiyar Birtaniya suka bayar a yanzu ita ce ko da yake sanya takunkumi yana da amfani ga ma'aikatan lafiya a asibiti, "amma babu wata shaida da ke nuna cewa yana amfani ga sauran jama'a".

2. Fasto yana yaki da coronavirus

Ikirarin da wani fasto ya yi cewa yana maganin coronavirus ba gaskiya ba ne.

Labarin fasto David Kingleo Elijah, daga Cocin the Glorious Mount of Possibility ya soma watsuwa a shafukan intanet bayan wani bidiyo da ya wallafa a YouTube da wasu shafukan sada zumunta inda yake cewa zai koma kasar China domin "dakile" cutar ta coronavirus.

A cikin bidiyon ya ce: "Zan je na dakile coronavirus ta hanyar amfani da mu'ujiza. Zan tafi China, Ina so na wargaza coronavirus."

Kwanaki kadan bayan haka, wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet sun yi zargin cewa faston ya tafi China amma an kwantar da shi a asibiti sakamakon kamuwa da coronavirus. Amma shafukan na intanet sun ambato shi da suna na daban - Elija Emeka Chibuke.

A zahiri, hoton da ya nuna shi a asibiti, hoto ne na Adeshina Adesanya, fitaccen dan wasan kwaikwayon Najeriya wanda aka fi sani da suna Pastor Ajidara, wanda ya mutu a asibiti a 2017.

3. Labarin karya kan direban tasi

An wallafa labarin karya na wani direban tasi wanda aka ce ya kamu da coronavirus a shafukan sada zumunta - inda masu amfani da WhatsApp suka yi ta watsa shi.

A cewar sakon, direban tasin shi ne ya dauko dan kasar Italiya wanda ya kamu da coronavirus ya kai shi wurin da aka killace shi. Daga nan ne gwamnatin jiar Ogun ta bukaci direban ya tafi asibiti.

An yi ikirarin cewa direban ya kamu da coronavirus - amma ya tsere daga asibiti kuma ya yi barazanar yada cutar idan ba a ba shi Naira miliyan 100 ba.

Hukumomi sun karyata labarin.

Gwamnatin jihar Ogun ta yi watsi da wannan labari a wata sanarwa da ta fitar, tana mai cewa babu wani mutum da ya tsere daga cibiyar da ta ware domin kebe mutanen da suka kamu da coronavirus.

An soma wallafa labarin ne a shafin bogi na gidan talbijin din Africa Independent Television (AIT), wanda ya fitar da sanarwar da ta ce shafin na Facebook ba nasu ba ne.

Labarin na dauke da hoton direban wanda aka ce sunasa Adewale Isaac Olorogun. Amma shafin Buzzfeed ya taba wallafa wannan hoto a cikin wata makala kan kasar Libya inda ya bayyana shi da wani suna na daban - Jude Ikuenobe.

Mr Ikuenobe ya shaida wa wakiliyar BBC, Yemisi Adegoke cewa ya yi matukar kaduwa da ganin yadda aka yi amfani da hotonsa a labarin kuma ya damu sosai kan sakonnin da wasu suke aike masa, ciki har da wadanda ke barazana ga rayuwarsa.

"Na daina yawo ko fita daga gida ni kadai. Duk inda zan je yanzu ina tafiya da abokai ko 'yan uwana."Na shiga mawuyacin halin tun lokacin da aka wallafa hotona."

Mutumin na farko da aka tabbatar ya kamu da coronavirus a Najeriya, wani dan kasar Italiya ne da ya koma Lagos daga Milan ranar 25 ga watan Fabrairu.

Hukumomi sun ce sun tuntubi kusan mutum 100 wadanda suka shiga jirgi ko kuma suka hadu da mutumin.

4. Wani sakon murya kan atisaye a Kenya ya jefa mutane cikin fargaba

A Kenya, sai da gwamnati ta fitar da wata sanarwa inda ta karyata "labaran karya" a kan coronavirus, ciki har da wata murya da ta karade manhajar WhatsApp, inda ta yi ikirarin cewa sako ne na gwamnati da ta aike wa 'yan jarida.

Sakon muryar ya yi ikirarin cewa an gano mutum 63 da suka kamu da cutar a kasar, amma ba gaskiya ba ne. A halin da ake ciki babu wanda ya kamu da cutar a Kenya.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce muryar wani bangare ne na atisaye kan sadarwa amma bata bayyana dalilin da ya sa aka fitar da muryar ga kowa da kowa ba.

Dokokin Kenya sun tanadi tarar $50,000 ko daurin shekara biyu a gidan yari kan duk mutumin da aka samu da laifin watsa labaran karya a kan coronavirus.

5. Maganin coronavirus

A Najeriya, wani Fasto ya wallafa sakon bidiyo inda ya yi ikirarin cewa shan farfesu yana maganin coronavirus. An yi ta watsa wannan batu a manhajar WhatsApp.

Babu wani magani ko rigakafin coronavirus kuma ikirarin da faston ya yi bai yi cikakken bayani kan amfanin farfesu a fannin lafiya ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce barkewar cutar coronavirus ya haddasa watsuwar labaran karya sosai.

A Cape Verde, kasar da ke Yammacin Afirka, an watsa labarai a shafukan sada zumunta wadanda ke ikirarin cewa wani likita dan kasar Brazil ya bayar da shawara a rika shan wani nau'i na ganyen shayi mai suna fennel domin kauce wa kamuwa da coronavirus. Nan da nan farashin ganyen shayin ya tashi a kasuwanni, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.

Ma'aikatar Lafiya ta Brazil ta gargadi mutane su guji watsa labarin da ke cewa ganyen shayin na fennel yana rigakafin coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wanke hannu a kai a kai na cikin manyan abubuwan da ke hana kamuwa da cutar ta coronavirus.