Coronavirus: An sake kebe mutum uku a Najeriya

A

Asalin hoton, Getty Images

Kwamishinan Lafiya a jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da killace wasu mutum uku da ake zargi sun kamu da Coronavirus.

An kebe su ne a wani asibiti da ke Yaba a matsayin rigakafi ga yaduwar cutar, kamar Farfesa Abayomi ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Nan gaba ake sa ran za a saki sakamakon gwajin da aka yi wa mutanen.

Najeriya ta tabbatar da bullar cutar a karon farko a kasar ranar 27 ga watan Fabrairu - kasa ta farko a yankin kudu da hamada da aka samu bullar cutar.

Farfesa Akin Abayomi ya ce daya daga cikin mutanen uku dan Najeriya ne da ya dawo kasar ranar Litinin bayan shafe mako daya a Faransa.

Daga baya kuma ya nuna alamun ciwon kai da matsalar numfashi.

Sauran mutanen kuma matafiya ne daga Ingila da kuma China.