Tarihin Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II

Sanusi

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 9 ga watan Maris din 2020 ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II daga sarautar Kano, bayan daukar lokaci da aka yi ana zaman 'yan marina.

Sai dai idan aka yi waiwaye kan lokacin da ya zama sarkin Kano a watan Yulin 2014, nadin Sarki Muhammadu Sanusi na II ya jawo ce-ce ku-ce sosai ba ma a jihar Kano ba har da Najeriya baki daya.

Mutane da dama sun yi tsammanin cewa sarautar za ta koma gidan marigayi Ado Bayero ne, wanda ya shafe fiye da shekara 50 yana rike da sarautar Kanon, amma sai ga shi Sarki Sanusi wanda ya gaji kakansa Sarki Sanusi na I ya haye gadon.

Kano ta dauki dumi a lokacin, saboda shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya nuna baro-baro baya so Sanusi Lamido Sanusi ya hau kujerar, yayin da Gwamna Kwankwaso tare da jam'iyyar adawa ta APC a a lokacin suke goyon bayan Sanusi.

A karshe dai ta tabbata Sanusi ya zama sarkin Kano, yayin da Sanusi Ado Bayero kuma da suka yi takara a lokacin, wanda kuma PDP ke mara wa baya ya yi murabus daga Ciroman Kano tare dan barin garin kacokan.

Daga baya farin jinin Sanusi ya kara karuwa a tsakanin Kanawa da 'yan Najeriya, saboda yadda yake nuna tausayin mata da kuma son kawo gyara a al'umma.

Wannan tafiya dai ba ta yi wani nisa ba sai wa'adin Kwankwaso a matsayin gwamna ya kare, inda mataimakinsa Ganduje ya hau.

Sai dai bai dade da hawa ba sai aka fara samun takun saka tsakanin tsohon gwamnan Kwankwaso da sabon gwamnan Ganduje.

Wannan sabani shi ne ake gani ya rikide ya zama takun sakar da aka yi ta yi tsakanin Sarki Sanusi da Abdullahi Umar Ganduje.

Wane ne Sarki Muhammadu Sanusi II?

  • An haife shi a zuriyar sarakunan Fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.
  • Jika ne ga sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.
  • Ya samu digiri a fannin tsimi da tanadi da fannin addini Musulunci.
  • An nada shi mukamin gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN) a watan Yuni 2009.
  • Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.
  • An dakatar da shi a watan Fabrairu bayan sun samu sabani da shugaban kasa.
  • An kuma nada shi a matsayin Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yuni 2014.
  • Sunansa ya canja daga Sanusi Lamido Sanusi zuwa Muhammad Sanusi II.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A irin wasikun da muke samu daga 'yan jaridun nahiyar Afirka, a watan Ylin 2014 Mannir Dan Ali ya yi nazari kan ko sabon Sarkin Kanon zai zama mai iya kawo sauyi kamar yadda ya yi a lokacin yana Gwamnan Babban Bankin Nigeria watau CBN.

Sanusi Lamido Sanusi wanda ya jawo ce-ce ku-ce lokacin yana gwamnan CBN, ya samu nasarar cimma burinsa na rayuwa.

Al'umma da dama sun yi matukar mamaki ganin yadda aka zabe shi a matsayin sarkin Kano, saboda girman matsayin a tsakanin Musulmi Hausa-Fulani, maimakon babban dan margayi sarkin Kano, Lamido Ado Bayero.

Dama Malam Sanusi bai taba boye anniyarsa ba ta son zama Sarki a birni mai dimbin tarihi da kyawun gani a Afirka ta yamma.

'Sauyin Zamani'

Kakansa, Muhammad Sanusi ya yi mulkin Kano har lokacin da aka tunbuke shi a 1963.

Bayan zamansa sarkin an fara kiransa da Muhammed Sanusi II, abin da ke bayyana shi a matsayin magaji.

Gwamnonin arewacin Najeriya sun yi taya sabon sarkin murna.

A tsakiyar shekarar 1990, Malam Sanusi Lamido ya ajiye aikin da yake a banki inda yake karbar albashi mai tsoka ya tafi kasar Sudan domin neman ilmin Qur'ani da wasu bangarori na Addinin Musulunci.

Amma sabon sarkin bai taba boye ra'ayinsa na yin muhawara ba saboda haka a karshen mulkin soji cikin shekarar 1999, ya kalubalanci dabbaka Shari'ar Musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Ya kuma bayyana ra'ayinsa a wata jarida inda ya ce akwai wasu matsaloli da a ganinsa ya kamata a magance su.

'Cece-kuce kan Shari'a'

Kalubalantar shari'a da ya yi ya jawo bambamcin ra'ayi tsakanin sa da malamai masu tsatstsauran ra'ayi a arewacin Najeriya.

Wasu masu dauke da makamai sun yi yunkurin hallaka Marigayi Sarki, Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a watan Yuni yana da shekara 83 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

A lokacin sai mutane suka yi ta sa ido don ganin matakin da sabon sarkin zai dauka kan batun ta'addanci.

Asalin hoton, Getty Images

Dubban magoya bayan sabon Sarkin

Wata matsala da sabon sarkin mai shekaru 53 ke fuskanta ita ce ta bayyana ra'ayinsa sakamakon rawanin da ya rufe masa baki.

Hakazalika, sabon sarkin ya fara yin huduba a Sallar Juma'a da ake yi mako-mako a babban masallacin cikin garin Kano sabanin wanda ya gaji sarautar daga hannunsa wanda yin hakan watakila wata hanya ce ta bayyana manufofinsa.

Sarkin wanda ba ya jin tsoro, ana sa ran zai yi amfani da matsayinsa wajen magance matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram, rashin aikin yi da rashin saka yara a makaranta, ta hanyar samar da daidaito a tsakanin 'yan siyasa da sauran talakawa wadanda a koda yaushe su ke zargin manufofin gwamnati.

Jonathan ya ki taya shi murna

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta yi riga malam masallaci inda ta yi gaggawar bayyana wani wanda za a nada a sarautar Kano kafin daga bisani Gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da nasa zabin.

Sai dai shugaban kasa na wancan lokacin, Goodluck Jonathan wanda ya dakatar da sabon sarkin daga shugabancin Babban bankin Nigeria bai taya shi murna ba.

Asalin hoton, Getty Images

Mr Jonathan yana yawan ziyartar tsohon Sarkin Kano marigayi Ado Bayero.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin-CBN din ya fallasa batun badakalar kudi dala biliyan 20 da suka yi layar zana a kamfanin mai na kasa.

Sai dai alamu na nuni da cewa matukar sabon sarkin na son tafiya tare da gwamnati to lallai sai ya janye wannan mataki nasa.

Amma kamar yadda ake hasashen cewa babu wani dan siyasa da zai fito takarar shugabancin kasa ba tare da neman kuri'ar al'ummar jihar Kano ba, a don haka watakila dole Mr. Jonathan ya cire hularsa tare da ajiye gwiwarsa a fadar ta Kano don girmama al'adunsu kafin samun kuri'arsu.