Contagion: Shin an yi fim kan coronavirus shekara 10 da suka wuce?

Contagion movie poster Hakkin mallakar hoto Warner Bros

Fim din wanda aka saki a 2011 da bai shahara ba sosai sai bayan buular cutar coronavirus a 'yan kwanakin nan.

Duk da cewa akwai manyan 'yan fim da suka fito a cikinsa kamar su Matt Damon da Jude Law da Gwyneth Paltrow da Kate Winslet da kuma Michael Douglas, a wancan lokacin fim din shi ne na 61 cikin jerin fina-finan da suka fi samun kudi.

Amma Contagion ya bayar da mamaki a lokacin da ya fara shahara a manhajar Apple's iTunes Store inda aka yi ta sauke shi a Amurka, sannan kuma aka yi ta neman fim din a Google.

Kamfanin da ya yi fim din Contagion Warner Bros. - ya ce shi ne na 270 cikin fina-finansa mafi shahara a watan Disambar 2019, a lokacin da aka fara samun rahoton bullar cutar a China.

Wata uku bayan nan, sai ga Contagion ya zama cikin 10 na farko.

Duk dai saboda coronavirus ne, kuma kamanceceniyar da ke tsakanin cutar da fim din ta bayyana karara ne bayan shekara 10 da yin fim din.

Meke cikin fim din?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A cikin fim din, wata bakuwar cuta mai kisa ta kashe wata mata 'yar kasuwa (Paltrow), bayan matar ta samo cutar a yayin wata tafiya zuwa China.

Kasancewar sunan China da ya fito a fim dinne ya sa yake kara yin tashe a makonnin da suka gabata, inda masu kallo suke ta neman Contagion.

Wani abin sha'awa game da yadda fim din ke kara tashe shi ne yadda aka nuna Gwyneth Paltrow (jarumar 'yar Amurka) ta wallafa hotonta tana sanye da takunkumin rufe fuska a cikin jirgin sama ranar 26 ga watan Fabrairu.

Sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram ya ce: ''A kan hanyar zuwa Paris. Fargaba? Tsoro? Shiru? Annoba? Farfaganda? Haka Platrow za ta yi barci da wannan abin a fuskarta cikin jirgin nan.''

''Ina cikin jaruman fim din nan. Ku kula da kanku. Ban da musabaha. A dinga wanke hannu akai-akai,'' a cewar jarumar, wadda ke da fiye da mabiya miliyan shida a shafukan sada zumunta.

Kamanceceniya

Akwai kamanceceniya sosai da abin da ya faru a fim din Contagion.

Jaruma Paltrow ta kamu da cutar mai suna MEV-1, daga wani mai dafa abinci na Hong Kong bayan yin musabaha da shi, shi kuma ya samu cutar a jikin alade a lokacin da yake sarrafa namansa, shi kuma aladen ya samu da kwayoyin cutar ne a jikin jemage.

Bayan haka ne ta shiga jirgi ta dawo gida cikin tsananin rashin lafiya inda ta mutu ba da dadewa ba. Bayan nan ma danta ya mutu, amma mijinta bai kamu da cutar ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ko a gaske, masana lafiya suna ganin cewa cutar ta samo asali ne daga dabbobi a garin Wuhan na China a Disambar 2019.

Ana ganin cewa cutar ta samo asali ne daga jemagu kamar yadda aka yi a fim din Sars epidemic na 2002, daga haka sai ta fara yaduwa zuwa mutane da wasu hallitu.

Har yanzu ba a cimma matsaya ba kan ko wacce dabba ce ta fara yada cutar kamar yadda alade ya fara yada cutar a cikin fim din, sai dai hukumomi a China sun nuna wata kasuwar dabbobi da ke a garin Wuhan inda suka ce daga nan ne cutar ta samo asali.

Kamar yadda ake yada cutar a gaske ta hanyar gaisawa da hannu da kuma kusantar juna, a fim din Contagion ma ta haka ake yada cutar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Killacewa

A lokacin da ake zargin an samu barkewar cutar a cikin fim din, an ga ma'aikatan hukumar tattara bayanai kan cututtuka suna killace jama'a.

A cikin fim din, an killace jama'a a a garin Chicago na Amurka kamar yadda aka yi a China a halin yanzu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yanzu haka an killace jama'a da dama a arewacin yankin a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar ta Covid-19.

Fargaba da Tasiri

Tunawa da kuma dawo da fim din Contagion ya bai wa Scott Z Burns mamaki matuka wanda shi ne marubucin fim din.

Amma a wata tattauna wa da jaridar Fortune ta yi da shi, ya bayyana cewa ainahin abin da yasa ya rubuta fim din shi ne domin ya ankarar da jama'a cewa irin wannan cutar za ta iya barkewa a cikin al'ummarmu.

''Kamanceceniya tsakanin Contagion da coronavirus ba su da wani muhimmanci saboda ba da gangan muka yi ba,'' in ji Burns.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Barkewar cutar a wannan karon ya jawo yada labaran bogi inda wasu ke cewa an kirkiro wannan cuta ne a matsayin makami mai guba.

Shi kansa Burns, wanda shi ne marubucin fim din ya zama abin zargi.

A wata hira da ya yi da New York Times ya bayyana cewa wasu mutane na zarginsa kan cewa ya shiga kungiyar asiri ta wadanda ke kokarin juya akalar duniya.

''Na tuna a lokacin da na damu kan cewa yaduwar labaran bogi na da hatsari kamar cutar.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hujjoji a kimiyance

Za a iya yin bayani kan fim din Contagion kan yadda Mista Burns ya yi kokari wajen bayar da hujjoji a kimiyance.

Sai da ya tattauna da manyan likitoci da kuma jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, a lokacin da yake rubuta fim din.

Ya bayyana cewa sun ba shi shawarwari matuka.

Labarai masu alaka