Shin coronavirus na shiga tsakanin mutane da addinansu?

Adadin masu kai ziyara Masallacin Makkah ya ragu tun bayan bullar coronavirus Hakkin mallakar hoto ABDEL GHANI BASHIR
Image caption Adadin masu kai ziyara Masallacin Makkah ya ragu tun bayan bullar coronavirus

Yayin da ake ci gaba da nuna fargaba kan bazuwar cutar coronavirus, mutane a fadin duniya na sauya yadda suka saba gudanar da wasu harkokin rayuwarsu.

Wasu sun rage yawan tafiye-tafiye sannan suna kauracewa tarukan jama'a. Wasu kuma sun daina musabaha da hannu da rungumar juna inda suka koma yin gaisuwa da kafa.

Masallatai da majami'u da wuraren bauta su ma sun sauya wasu tsare-tsarensu a kokarin dakile yaduwar cutar.

To ta yaya za ka ci gaba da yin ibada yadda ka saba daidai lokacin da abubuwa ke sauyawa?

Musulunci

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu ibada na sallah a gaban Masallacin Makkah bayan an rufe domin tsaftace shi

Masallacin Makkah da a ko yaushe yake cike da mutane, a baya-bayan nan an samu raguwar mutanen da ke ziyara a masallacin.

Duk da cewa a yanzu an bude masallacin bayan rufewar da aka yi masa tun farko domin tsaftace shi, an sa shinge a Dakin Ka'aba da ke tsakiyar masallacin domin hana mutane taba bangon Dakin Allah.

Har yanzu dokar dakatar da baki zuwa biranen Makkah da Madina tana nan.

Musulmai daga sassan duniya suna zuwa Umrah wadda sabanin aikin Hajji, ake iya gudanar da ita a kowane lokaci.

Kimanin mutum miliyan takwas ne suke zuwa Saudiyya duk shekara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A mafi yawan lokuta miliyoyin maniyyata ne ke zagaye Ka'aba domin yin addu'o'i

Hadiza Tanimu Danu, wata mai kamfanin shirya tafiye-tafiye ce a Najeriya wadda take safara zuwa Makkah. Ta ce tana mayar da martani game da hana baki zuwa birnin.

"Mutane ba su ji dadi ba". "Umrah ce kuma kowa yana son zuwa domin yin ibada."

Ba wai kawai Umrah lamarin zai shafa ba.

"Wasu na cikin damuwa saboda 'idan aka tsawaita dokar zuwa watan azumi ko kuma har zuwa lokacin aikin hajji, me zai faru?" a cewarta.

Hukumomin Saudiyya sun ce matakan na wani dan lokaci ne sannan ba su fito sun bayyana shirye-shiryen soke aikin Hajjin ba.

Ana ci gaba da gudanar da wasu ayyukan ibadun da ke iya yada cutar.

Fargaba ta barke cikin 'yan kwanakin nan bayan fitar da wasu hotunan bidiyo da suka bazu a shafukan sada zumunta da ke nuna Iraniyawa suna lasar wani humbare.

A daya daga cikin bidiyon, an ga wani mutum a humbaren Masumeh da ke Qom yana fadin "Ba na tsoron coronavirus" kafin ya lasa tare da sumbatar kofofin shiga humbaren.

Wasu mutane na ganin humbaren yana iya warkar da cututtuka.

Biyu daga cikin mutanen na fuskantar hukuncin zaman gidan yari saboda abin da suka yi amma wasu Iraniyawa sun ce kamata ya yi a rufe wuraren ibadar baki daya.

Ga akasarin Musulmai, an mayar da hankali ne kan 'yan sauye-sauye na yadda suka saba gudanar da ibadarsu.

Misali, yayin da Afirka Ta Kudu ke kai-kawo game da cutar da ta bulla a kasar, shugabannin addini sun shawarci masallata kan su dauki matakan kariya.

Wakilin BBC a Afirka Mohammed Allie, ya ce an shawarci masu ibada a masallatai su guji gaisawa da hannu ko rungumar juna.

Ya ce "za a dauki dan lokaci kafin mutane su saba da sauyin."

"Har yanzu mutane suna gaisawa bayan sallah a masallaci ba wai saboda sun ki amfani da shawarar da aka ba su ba amma saboda wani abu ne da sun saba da shi."

Ya ce wasu mutane sun fara taba kafafunsu a maimakon gaisawa da hannu wasu kuma na dunkule hannayensu suna jinjina a matsayin gaisawa.

"Mutane dai na kokarin yin sauye-sauye," inda ya ce an shawarci mutane su taho da dardumansu zuwa masallaci ranar Juma'a kamar yadda masallata a Singapore suke yi.

Hindu

Hakkin mallakar hoto SANJAY KANOJIA
Image caption Daukan matakai kan COVID-19 yayin bukukuwan Holi a Uttar Pradesh

Ga mabiya addinin Hindu wannan ne lokacin gudanar da bikin Holi da ake baje-kolin launuka.

Ana gudanar da bikin domin samun sauki daga sharri da neman sauyin rayuwa. A wani bangare na bukukuwan, mutane suna watsa hoda mai launuka iri daban-daban a iska sannan su shafawa junansu a fuska.

Fira Ministan Indiya Narendra Modi ya ce ba zai halarci bukukuwan ba, inda ya shawarci mutane su guji zuwa taron jama'a.

Amma mutane da dama sun halarci bukukuwan da aka yi a karshen mako cikin matakan kariyar da aka dauka kamar sanya takunkumin fuska.

Wasu kuma na ganin hadari ne da ba za su shirya masa ba.

Nicky Singh na zaune a Amritsar a jihar Punjab da ke Indiya. Ya ce ya zauna a gida inda ya zabi gaisawa da mutane ta waya.

Ya fada wa BBC cewa "yin atishawa kadai na iya ankarar da mutane game da cutar ta coronavirus.

"Ina jin dadi, da na zabi kare kaina a kan zuwa bukukuwa," a cewarsa.

Yahudanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Many Jews traditionally touch or kiss when they enter a building or room

Ta yaya za ka fadawa mutane su guji rungumar juna lokacin jana'iza? Wani abu ne da Jackie Tabick, daga wajen ibada na Yammacin London take tunani a kai.

"Ba abu ne mai sauki ba," a cewarta.

"Ina ganin zan iya cewa 'na san cewa kowa yana son ya nuna kauna ga matar da ta rasa mijinta amma hanyar da ta fi dacewa ka nuna kauna a 'yan kwanakin nan - kuma na san za ta iya fahimta - shi ne yi mata magana ko daga mata kai saboda abin da ya fi dacewa a yi kenan a wannan lokaci,"

Wani babban malami a Isra'ila David Lau, ya fitar da wata sanarwa inda ya shawarci mutane su guji tabawa ko sumbatar wani abu da ke cikin kube.

Taron malaman addinin Isra'ila na Turai ya shawarci mutane da su guji sumbatar irin abubuwan da ake makala ayoyin littafin Attaura.

Amma Tabick ta ce rashin sumbatar abun ba wai wani abu ba ne muhimmi a rayuwar Yahudawa.

"Watakila zai yi kyau a sake duba salon yadda muke gudanar da ayyukan ibada. Kila hakan ya taimaka mana wajen sake tunanin abin da za mu maye gurbinsu. Babban muhimmin abu shi ne mu tabbatar da cewa mun taimaki juna, kuma mu dinga jadda hakan wajen kusancinmu da Ubangiji.''

Addinin Kirista

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yayin da aka hana shiga da fita a baki dayan Italiya, akwai wasu mutane da aka karfafa musu gwiwa wajen fita don su yi ziyara.

Fafaroma Francis ya nuna wa malaman addinin kirista muhimmancin "zuwa ziyarar mara lafiya'' da kuma raka jami'an lafiya wajen taya su aikin sa kai yayin da suke gudanar da aikinsu.

Fafaroman ya zabi ya bayar da sakonsa na ranar Lahadi ta intanet a yunkurin rage taron mutane a fadar Vatican.

Coci-Coci a Ghana da Amurka da Turai sun sauya yanayin yadda suke taruwa domin gudanar da bauta domin rage bazuwar cutar.

A maimakon su rinka gaisuwa tsakaninsu da ke alamta zaman lafiya, an bukaci mambobin cocin da su rinka yi wa mutumin da ke zaune kusa da su cikin cocin addu'a.

Amma duk da wasu na ganin cewa wadannan matakan na da muhimmanci, wasu na ganin hakan ba daidai bane.

Alexander Seale wani dan jarida ne da ke zaune a Landan.

''Babu jin dadi kamar lokacin da,'' ya bayyana mani, '' rashin gaisuwa kamar hana taruwa da kuma shan tumi tamkar hana taruwa a coci ne.''

''A gare ni, shan tumi babban abu ne, tamkar jikin Yesu ne - abu ne mai daraja.''

''Abin kunya ne amma na gane cewa an dauki wadannan matakai.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An umarci daruruwan mutane da suka halarci cocin Georgetown da ke birnin Washington D.C da su killace kansu da kansu bayan shugaban an tabbatar da shugaban cocin a matsayin mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar ta coronavirus.

An gano cewa Rabaran Timothy Cole na dauke da cutar a ranar Asabar kuma a yanzu haka an killace shi.

Rahotanni kuma sun bayyana cewa kusan mutum 550 ne suka halarci zaman cocin da aka gudanar a ranar 1 ga watan Maris kuma an gudanar da shan tumi a lokacin.

Ana ganin cewa nuna kin bayar da goyon baya domin adaina halartar wuraren ibada ya sa aka kara samun bazuwar cutar a Kudancin Korea.

Sama da rabin wadanda aka samu da cutar a kasar na da alaka ne da wata Kungiyar Kiristoci da ake kira Shincheonji Church of Jesus.

Ana ganin cewa zama kusa da juna na taimakawa wajen baza cutar cikin sauri ga mambobin cocin, kuma suna tafiya kasashen duniya su saka wa wasu cutar.

Ana zargin shugabannin coci da kin bayyana sunayen mutane, wanda hakan yake kawo cikas ga hukumomi a kokarinsu na gano masu dauke da cutar kafin ta bazu.

Saukin abin shi ne wannan cutar ta fita daban, kuma coci-coci a fadin duniya na neman hanyoyin za sa su bi wajen aiki da ka'idojin da gwamnati ta gindaya na kare kai daga yaduwar cutar.

Labarai masu alaka