Abin da ya sa ake dauke sarakuna daga garinsu bayan cire su

June 1934: British diplomat Lord Lugard (Frederick John Dealtry Lugard) with a group of West African chiefs at London Zoo. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Yunin 1934 aka dauki hoton nan na gwamnan arewacin Najeriya Lord Lugard da wasu sarakunan kasar a wani Gidan Zoo a Landan

Tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta cire Sarki Muhammadu Sanusi na II ta kuma mayar da shi jihar Nasarawa a matsayin sabon matsuguninsa, 'yan Najeriya da dama suka dasa ayar tambaya kan dokar da ta ce a dinga yi wa sarakuna irin wannan talalar.

BBC ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen binciko ainihin wannan al'ada. Shin doka ce? Idan doka ce waye ya assasa ta? Tana cikin kundin tsarin mulki?

Wani masanin tarihi a Kano Malam Ado Kurawa ya shaida mana cewa a shekarar 1930 ne Turawan mulkin mallaka suka fara kirkirar dokar da ta ce duk wani sarki da aka sauke daga mulki ko aka ci shi a yaki ko ya sauka don radin kansa, to za a dauke shi daga garin da yake zuwa wani matsuguni daban da zai samu mafaka.

Dokar ta ce sarkin ba shi da izinin zabar wajen da zai zauna sai inda aka zabar masa, sannan ba zai sake shiga garin da ya mulka din ba har bayan rai.

Ado Kurawa ya ce: "Sun kirkiri wannan doka ce don gudun yin sarakuna biyu a gari daya, wato tsoho da sabon sarki, da kuma gudun samun sabanin ra'ayi.

"Sannan suna jin tsoron kar a samu matsala a harkokin mulki ta yadda bangarori biyu na tsohon sarki da sabon sarki za su dinga adawa da juna ko nuna karfin iko," in ji masanin tarihin.

Yadda aka yi wa Sarki Alu

Sai dai tarihi ya nuna cewa tun kafin Turawan mulkin mallaka su sanya ta zama doka, sun fara aiwatar da wannan tsari a lokacin da suka shigo arewacin Najeriya.

A Kano a misali, a shekarar 1903 Turawan sun shiga garin don yakar Sarki Aliyu Babba da aka fi sani da Alu, amma a lokacin yana Sakkwato.

Bayan sun ci Kano da yaki sai suka bazama neman Sarki Alu wanda shi kuma tuni ya samu labari har ma ya yi niyyar wucewa Gabas don gabatar da aikin Hajji. Sai dai sun cim masa a jihar Neja suka kuma kama shi.

Da farko sun kai shi Yola ne don ya yi mafaka a can, amma daga bisani Sarkin Yola na lokacin ya kasa samun nutsuwa da jin tsoron cewa za a samu sarakuna biyu a kasarsa, saboda irin kwarjini da karfin mulkin Alu da yawan jama'arsa.

Don haka sai ya nemi Turawan da su dauke Alu daga garinsa, daga nan sai aka mayar da Sarki Alu Lokoja inda ya zauna har mutuwarsa a shekarar 1926.

Bayan Sarki Alu an yi sarakuna da dama da wannan doka ta shafa suka kuma bar garuruwansu, tafiya ta har abada.

Wasu sarakunan da aka fitar daga garuruwansu

Daga cikin su akwai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na I kakan Muhammadu Sanusi na II, wanda shi ma Gwamnatin Yankin Arewa ta sauke shi a shekarar 1963 bisa binciken Muffet kan harkokin kudi na Masararutar Kano.

An kai Sarki Muhammadu Sanusi na I garin Azare da ke jihar Bauchi don samun mafaka, kuma daga cikin 'ya'yansa ma akwai wadanda ya haifa zamanin zamansa a Azare.

A lokacin da Abubakar Rimi ke takarar neman kujerar gwamnan Kano a 1979 ya yi alkawarin mayar da Sarki Sanusi Kano idan ya ci zabe.

Duk da cewa Rimi bai samu cika alkwarin yadda ya so ba saboda Khalifa Sanusin ya ki yarda ya koma cikin birnin Kano, amma dai ya samu ya mayar da shi garin Wudil wanda ba shi da nisa sosai da Kanon.

Kuma Khalifa Sanusi bai sake taka birnin Kano ba har ya mutu.

Ibrahim Dasuki shi ne Sarkin Musulmai na 18 a Sokoto, kuma gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha ta cire shi a shekarar 1996.

Hakkin mallakar hoto Idris Sanusi
Image caption Sarki Sanusi I a karshen rayuwarsa bayan ya koma Wudil da zama

Gwamnan Sokoto na wancan lokacin Yakubu Mu'azu ya sa an mayar da shi jiharTaraba don samun mafaka, amma daga baya Ibrahim Dasuki ya koma Kaduna har zuwa mutuwarsa a wani asibiti a Abuja a 2016.

Kazalika irin wannan ta faru da Sarkin Gwandu Almustafa Haruna Jokolo a 2005. Inda shi kuma aka kai shi birnin Lafia a jihar Nasarawa.

Sai dai Jokolo ya shigar da kara kotu yana kalubalantar zamansa a Lafia, kuma ya yi nasara inda daga baya aka bar shi ya koma Kaduna har zuwa yanzu.

Baya ga su akwai irin su Sarkin Bauchi Yakubu da fi sani da Maje Wase da aka cire shi aka kuma kai shi garin Wase na jihar Filato.

Sai kuma Sarkin Bauchi Umaru da shi kuma aka kai shiLokoja daga baya aka mayar da shi Ilorin inda ya kare rayuwarsa a cann, kamar yadda Alhaji Ado Danrimi Garba, Wakilin Tarihin Bauchi yaa shaida min.

Sannan akwai wani Sarkin Biu da aka taba cire shi aka mayar da shi Bauchi. Haka kuma akwai hakimai da dama da irin haka ta taba faruwa da su a arewacin Najeriya.

Me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce?

Masana shari'a da dama na cewa ya kamata zuwa yanzu a daina amfani da duk wata doka ta Turawan Mulkin mallaka idan dai har ba ta cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ko su lauyoyin Sarki Sanusi sun ce al'adar dauke sarakunan da aka sauke zuwa wani waje daban ba ta cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Sashe na hudu, karkashin sashe na 41 a dokar 'Yancin walwala na kundin tsarin ya bayyana cewa: ''Kowane dan Najeriya yana da damar zama a duk inda yake so a fadin kasar, kuma babu wani dan kasar da za a kora daga cikinta ko a hana shi dawowa bayan ya fita daga cikinta.''

Lauyoyin Sunusin sun ma sun kara kafa hujja da cewa "Mun yi matukar mamaki da har yanzu ake gudanar da irin wannan al'ada a Najeriyar yau, musamman ga shugabannin siyasa.

Hakkin mallakar hoto Dasuki Family
Image caption An fitar da marigayi Ibrahim Dasuki daga Sakkwato bayan sauke shi

"Kotun Daukaka Kara ta Najeriya ta bayyana haramcin wannan al'ada a shari'ar da aka yi tsakanin kwamishinan shari'a na jihar Kebbi da Sarkin Gwandu Alhaji Al Mustapha Jokolo, inda kotun ta bayyana hakan a matsayin haramcin da ba ya cikin kundin tsarin mulki, kuma keta hakkin sarkin ne,"

Shi ma Malam Ado Kurawa yana ganin lokaci ya yi da za a daina irin waccar al'ada da Turawan Mulkin Mallaka suka kawo.

"Sarki yana da damar zabar duk garin da yake so ya zauna kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Amma siyasa da ke shiga cikin lamarin ba ta bayar da wannan damar ba.

'Yan Najeriya da dama na ganin kamata ya yi a yi dokar da za ta soke waccar ta Turawan Mulkin Mallaka baro-baro ta yadda idan an sauke sarki ba za a tursasa masa zama a inda ba ya so ba.

Labarai masu alaka