Sauke Sarki Sanusi ya saba ka’ida- Lauyoyinsa

.

Lauyoyin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II sun kalubalanci matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tsige sarkin a ranar Litinin, inda suka ce majalisar zartarwar jihar ba ta da hurumin tsige sarkin.

Lauyoyin sun bayyana hakan ne karkashin jagorancin Abubakar B Mahmoud (SAN) a lokacin da suke ganawa da 'yan jaridu a yammacin Talata.

Sun bayar da hujjojinsu ne kan dokar kafa masarautu ta jihar Kano inda suka ce dokar ba ta ba gwamnan jihar ko kuma majalisar zartarwar jihar hurumin tsige sarkin.

Lauyoyin sun bayyana cewa ba su amince da duk wasu hujjoji da gwamnatin jihar ta bayar ba na tsige sarkin.

Kan batun hujjar da gwamnatin jihar ta bayar na cewa sarkin ya nuna rashin biyayya ga hukumomin jihar da kuma zargin sa da kin halartar tarurruka da gwamnatin jihar ta gayyace shi, lauyoyin sun bayyana cewa babu wata takardar tuhuma da aka turo wa sarkin ko kuma gayyatarsa da aka yi wadda bai amsa ba.

Lauyoyin sun bayyana cewa ba a taba bai wa Muhammadu Sanusi II dama ya kare kansa kan duk zarge-zargen da ake yi masa ba.

Sun kuma ambato wani sakin layi a tsarin mulki na jihar Kano wato sashe na 13, inda ya ce gwamna na da damar tsige sarki ne kawai bayan an gudanar da bincike da kuma tuntubar majalisar sarki ta jihar.

Sun bayyana cewa ba su da wata masaniya kan ko an gudanar da wani bincike kan sarkin ko kuma zama da majalisar sarki domin tattaunawa kan ko a tsige shi.

Lauyoyin sun ce al'adar nan ta dauke sarakunan da aka sauke zuwa wani waje daban ba ta cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

"Mun yi matukar mamaki da har yanzu ake gudanar da irin wannan al'ada a Najeriyar yau, musamman ga shugabannin siyasa.

"Kotun Daukaka Kara ta Najeriya ta bayyana haramcin wannan al'ada a shari'ar da aka yi tsakanin kwamishinan shari'a na jihar Kebbi da Sarkin Gwandu Alhaji Al Mustapha Jakolo, inda kotun ta bayyana hakan a matsayin haramcin da ba ya cikin kundin tsarin mulki, kuma keta hakkin sarkin ne."

Sanarwar lauyoyin ta ambato sakin layin shari'ar da ta bayyana haka: "Dauke sarki da gwamnan Kebbi da gwamnatin jihar suka yi zuwa garin Lafia a jihar Nasarawa daga baya kuma aka mayar da shi garin Obi na jihar ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ba ya kan ka'ida."

Lauyoyin sun kuma yi kira ga hukumomi musamman babban sifeton 'yan sandan kasar da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya kan cewa a bai wa sarkin 'yancin walwala domin komawa wurin iyalensa.

Labarai masu alaka