Dalilin da ya sa mata da matasa suka damu da cire Sanusi

Muhammadu Sanusi II yana da mata hudu da kuma 'ya'ya Hakkin mallakar hoto Maigaskiya Photography
Image caption Muhammadu Sanusi II yana da mata hudu da kuma 'ya'ya

"Na dauki kaddarar da Allah Ya tsara mani."

Tun bayan sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II 'yan Najeriya ke ta mayar da martani, da masu murna da masu bakin cikin abin da ya faru.

A wannan makala mun yi duba kan dalilan da suka sa mata da matasa suka fi kowa jin zafin sauke sarkin.

Har yanzu mata da matasa ba su gama farfadowa daga rudun da suka shiga ba sakamakon faruwar lamarin, don kuwa bakinsu bai yi shuru a shafukan sada zumunta ba har yau.

Suna hakan ne don ganin yadda tsohon sarkin ke da abubuwa da dama da suke kauna.

Hakkin mallakar hoto Maygaskeya

Ga dai abubuwan da ya sa matasan da ba su wuce shekara 30 ba suke jin sarkin a ransu.

Ba kowace al'ada yake bi ba

Tun bayan zamansa sarki a watan Yunin 2014 zuwa sauke shi da aka yi a ranar 9 ga watan Maris din 2014, Sanusi ya bambanta kansa da sauran sarakuna ta hanyar yin abubuwan da bisa al'ada ba a saba gani ba.

A matsayin sarki, ya taba sa 'yarsa ta wakilce shi a wani taro a Abuja, lamarin da yasa mutane da dama daga arewacin kasar suka dinga sukar sa da cewa yana son bata al'ada da addini.

Sannan shi bai yarda da tsarin zama da kwarkwara ba sabanin sarakunan da suka gabace shi.

Hakkin mallakar hoto Kano Emirate
Image caption Sarki Sanusi a wata tafiya da ya yi kasar waje a farkon shekarar 2020 kafin a sauke shi

Sarki mai tafiya da zamani

Tun da fari, daya daga cikin abubuwa da suka sa Sanusi ya shiga ran matasa da mata shi ne saboda suna ganin sa a matsayin wani da ke wakiltar su da zamaninsu.

Yana da tarin ilimi, ya yi tafiye-tafiye da dama sannan yana da wayewar kai, kuma mutum ne wanda ba ya barin wasu su juya shi.

Ga mata da yawa a arewacin Najeriya, daya daga cikin abubuwa na farko da suka ja hankalinsu game da lamarin Sanusi ne wata waka da Naziru Ahmed (sarkin Wakar Sarkin Kano) ya yi masa ta ''Mata Ku Dau Turame Ya yi.''

Wakar mai taken 'Dan Lamido' ta yi wani irin farin jini kuma har a yanzu ba a daina yayin ta ba a arewacin Najeriya, inda kusan duk gidan biki sai an buga ta.

Hakkin mallakar hoto KANO EMIRATE COUNCIL
Image caption Sanusi Lamido ya zama Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yunin 2014

Mai kare hakkin mata

Wani abin da ya kara jawo wa Sanusi farin jini wajen mata shi ne yadda yake fafutuka da kiran a kai 'yan mata makaranta, a hana bara da hana auren wuri, da kuma hana karin aure ga wanda ba shi da hali.

Duka wadannan na daga cikin abin da yasa matasa da mata suke son Sanusi.

Mutanen yanzu suna son fadin abin da ke ransu. Kuma Sanusi na II mutum ne da ke fadin ra'ayinsa a ko da yaushe.

Kuma Kano jiha ce ta Hausawa da Fulani sannan ba abu ne mai sauki ba mutum ya bayyana wani tunani sabanin na al'ummar yankin, sai dai haka Sarki Sanusi yake.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Sarki Sanusi

An haifi Sarki Sanusi a zuriyar Sarakunan Fulani a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, kuma shi ne sarki na 14da ya hau mulki bayan mutuwar Ado Bayero a 2014.

Daman ya sha fadin cewa burinsa a duniya shi ne ya zama Sarkin Kano.

Kuma ya zama gwamnan babban bankin kasar a 2009 sai dai an sauke shi daga kan mukamin gwamnan bankin na CBN bayan da ya ce kimanin dala biliyan 20 sun yi batan dabo.

Mujallar Time Magazine ta sanya shi cikin jerin mutanen da suka fi fada a ji a 2011.

Hakkin mallakar hoto Kano Emirate Council
Image caption Sanusi ya yi karatun jami'a a fannoni biyu - ilimin tattalin arziki da ilimin addinin Musulunci

A 2013 ya karbi wata lambar yabo kan yadda ya taimaka wajen bunkasa tsarin Bankin Musulunci.

Ya zama Sarkin Kano na 14 kuma jikan sarki Muhammadu Sanusi na I ne wanda kuma shi ne sarki na 11.

A shekarun 1990, ya ajiye wani babban aiki a lokacin inda ya tafi Sudan domin karo ilimin addini da na Arabiyya.

Tun kafin Sanusi ya zama sarki, ya ce ra'ayinsa ya shan bamban da na wasu mutanen arewa da ke son kafa shari'a, ra'ayinsa shi ne akwai abubuwa da dama da ya kamata a mayar da hankali a kansu.

Bayan ya yi maganar batan kudaden man ne shugaban kasa na lokacin Goodluck Jonathan ya dakatar da shi.

Sanusi ya kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu amma duk da haka ba a janye dakatarwar da aka yi masa ba kuma daga baya Sanusi ya janye karar.

Hakkin mallakar hoto Fadar Kano

Bayan gwamnan Kano ya sanar da Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano, lauyan tsohon Sarki Sanusi ya ce 'yan sanda sun kama sa.

BBC ta samu bayanan cewa mai magana da yawun gwamnan Kano ya ce za a mayar da Sanusi wani gari a Nasarawa kuma za a yi masa talala.

Amma lauyan Sanusi ya ce sun shigar da batun gaban kotu.

Me ya sa a ka cire Sanusi?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muhammadu Sanusi II tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne

Gwamnatin ta ce ta cire Sanusu domin martaba al'ada da addini da kuma masarautar Kano," sun zargi sarkin da nuna rashin biyayya ga dokokin jihar Kano.

Ikon da sarakuna ke da shi

  • Suna da karfin iko kafin zuwan Mulkin Turawan Mallaka
  • Sun zama a karkashin Mulkin Turawan Mallaka
  • Kundin tsarin mulkin kasa ya dan ba su iko tun bayan samun 'yancin kai
  • Ana ganinsu a matsayin wadanda suke rike da addini da al'ada
  • Ana martaba su sosai musamman a Arewa da ake da yawan musulmi

Ko me mutane suke cewa game da cire Sarki Sanusu II a kafafen sada zumunta?

Wasu na cewa cire Sanusi bai dace ba.

Sai dai kuma ra'ayin wasu ya bambanta.

Labarai masu alaka