Coronavirus: Mece ce annoba, kuma me ya sa ake amfani da kalmar?

A medical official with protective gear walks inside a plane while taking the body temperature of passengers, who arrived on a flight from New York City Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta bayyana barkewar cutar coronavirus a matsayin wata annoba da ta shafi kasashen duniya.

Wannan wata kalma ce da hukumar ta guji yin amfani da ita kafin yanzu.

Annoba tana bayyana wata cuta ce wadda ke yaduwa a tsakanin mutane a kasashen duniya da dama a lokaci guda.

Babban jami'in WHO, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, a yanzu hukumar na amfani ne da wannan kalma, saboda matukar damuwa game da ''gangamin da ake ta yi kan sakakcin da aka yi'' kan cutar.

Shin mece ce annoba?

An ware wannan kalma ce ga cutar da ke yaduwa, inda za a ga gagaruma da kuma ci gaba da yaduwar cutar tsakanin mutum da mutum a kasashe da yawa.

Lokaci na karshe da aka sami aukuwar annoba shi ne shekara ta 2009 lokacin da aka sami barkewar cutar murar aladu, wadda masana ke tsammanin ta kashe dubban mutane.

A kan sami annoba ce idan kwayar cutar wata sabuwar nau'i ce, da ke iya kama mutane nan da nan, kuma tana iya yaduwa daga wannan mutum zuwa wancan ta ingantacciyar hanya da dorewa.

Hakkin mallakar hoto BSIP

Ba tare da an sami wata allurar rigakafi da za ta iya magance kamuwa da cutar ba, kula yaduwar ta wani abu ne mai matukar muhimmanci.

Me ya sa ake amfani da wannan kalma a yanzu?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A karshen watan Fabrairu, Dokta Tedros ya ce, yayin da cutar Coronavirus take da yiwuwar zama annoba, ba ta kai ga hakan ba tukun, saboda ba mu ga yaduwarta yadda ba za a iya kula da ita a kasashen duniya ba.

Abin da ya sauya shi ne yawan kasashen suke fama da yawan matsalar cutar. A yanzu akwai mutum 118,000 da suka kamu a kasashe 114.

Sauya harshe ba sauya komai ba game da yadda cutar ke gudana, amma WHO tana fata abin zai sauya yadda kasashe ke kula da ita.

Dokta Tedros ya ce: ''Wasu kasashe suna fafutukar shawo kan matsalar, amma kuma ba su da kwarin gwiwa. Wasu kasashen kuma suna kokarin ne ba tare da wani kudiri ba''.

Ya kuma kara da cewa, WHO ta bukaci kasashe su:

*Farfado tare da karfafa hanyoyin kai daukin gaggawa

*Rika zantawa da jama'a game da hadurra da yadda za su iya kare kansu

*Gano da killace, da gwada, da kuma yin magani ga duk wani wanda ya kamu da cutar ta coronavirus, sannan a bi sawun duk wanda ya cudanya da mutumin da ake zargin ya kamu da cutar

''Ba za mu iya bambanta hakan da kara sosai ba, ko kuma yawaita ambatawar ba - dukkan kasashen duniya suna iya sauya hanyar shawo kan wannan annoba''.