Hanyoyi biyar da coronavirus ta shafi Bollywood

Jaruman Bollywood Hakkin mallakar hoto Filmfare
Image caption Jaruman Bollywood

Yayin da cutar coronavirus ke ci gaba da yaduwa a duniya, masana'antar Bollywood ta tanadi matakan kariya daga kamuwa da ma yaduwar cutar.

Daga cikin matakan, Bollywood ta dakatar da daukar duk wani fim da ake yi a yanzu har zuwa 31 ga watan Maris 2020.

Matakin ya biyo bayan tattaunawar da masu ruwa da tsaki a masana'antar suka yi.

An umarci dukkan masu shirya fim da su dawo daga inda suka je daukar fim ko a cikin kasar ko kuma a wajen kasar.

Masana'antar ta ce ta dauki wannan matakin ne domin kauce wa kamuwa da yaduwar cutar.

Hanyoyi biyar da coronavirus za ta shafi Bollywood

1. Dage ranakun fitar da fina-fianai

Kasancewar coronavirus na saurin yaduwa, hakan babbar barazana ce ga rayuwar al'umma a ko ina.

Wannan dalilin ne ya sa yawancin masu gidajen kallo a India wato sinima suka rufe gidajen kallonsu saboda tsoron yaduwarta a wajen jama'a.

Rufe gidajen kallon kuwa ya janyo ala tilas aka dage sakin wasu fina-finai da ya kamata a ce an sake su a wannan watan.

Fina-finai kamar Baaghi 3 da Angrezi Medium da Sooryavanshi da Sandeep Aur Pinky Faraar, an dage fitar da su zuwa wani lokaci saboda abin d ake faruwa a duniya na annobar coronavirus.

Bisa al'ada dai idan mai shirya fim zai fitar da fim dinsa sai an fara haska shi a sinima kafin daga bisani a fitar da shi ko ina.

To a dalilin rufe gidajen kallon ko sinimun dole masu shirya fim suka dage fitar da fina-finansu har sai abin da hali ya yi saboda gudun yaudwar cutar coronavirus tun da mutane da dama ne za su hadu a gidan kallon domin kallon fim din.

2. Dage daukar fim

Hakkin mallakar hoto Filmfare

Bisa la'akari da yadda cutar coronavirus ke yaduwa a kasashen duniya, masu fada a ji a masana'antar Bollywood suka tattauna inda suka tsaida matsaya a kan dage daukar duk wani fim a ciki ko a wajen kasar.

Akwai fina-finai da dama da aka shirya daukarsu a wajen kasar Indiya, amma sakamakon yaduwar cutar, yanzu an soke

Haka fina-finan da ake dauka ma a cikin kasar an soke har zuwa 31 ga watan Maris 2020.

Wannan mataki ya zama dole saboda kaucewa kamuwa da yaduwar cutar coronavirus a tsakanin 'yan fim.

3. Kasuwar gwanaye masu daukar hoton jarumai a India ta yi kasa

Saboda yaduwar da cutar coronavirus ke yi a duniya, ya sa da yawa daga cikin jaruman Bollywood sun kasance a gida ba sa fita.

Hakan kuwa ya shafi irin gwanayen nan ma su daukar hoton jarumai a kasar, wanda ke bibiyar yadda jaruman ke tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Irin wadannan masu daukar hoton idan sun dauka su kan wallafa shi a shafukansu na sada zumunta domin masu bibiyarsu.

Ta haka ne kuma suke suna, sannan kuma suke samun masu bibiyarsu da dama.

To yanzu jaruman ba sa fita suna zaune a gida, don haka irin wadannan masu daukar hoton ba su da abin dauka balle su wallafa a shafukansu na sada zumunta.

4. An dakatar da wasu manyan taruka da suka shafi jarumai da fina-finan Bollywood

An dakatar da gudanar da duk wasu manyan taruka da aka shirya yi kamar na tallata fim da bikin bayar da kyautuka da dai makamantansu.

Yaduwar da coronavirus ke yi ya sa ala tilas an dakatar duk wasu manyan taruka saboda gudun kamuwa d aita.

5. Yaduwar cutar coronavirus a duniya ya sa da yawa daga cikin jaruman Bollywood sun daina fita kasashen waje

Hakkin mallakar hoto Filmfare

Tuni da dama daga cikin jaruman Bollywood suka soke fita wajen kasar domin yawon bude idanu ko shakatawa.

Jarumi Hrithik Roshan ya shirya zuwa Amurka a wata mai zuwa domin ya je ya gaisa da masu sha'awar kallon fina-finansa, amma yanzu ya soke wannan tafiya.

Haka shi ma Salman Khan akwai tafiyar da ya yi niyyar yi zuwa Amurka da Canada amma ya fasa.

Shima Varun Dhawan, ya dage wata tafiya da ya yi niyyar yi zuwa wata mai zuwa.

Labarai masu alaka