Coronavirus: Yaushe annobar za ta zo karshe kuma rayuwa ta dawo daidai?

Coronavirus Hakkin mallakar hoto Getty Images

Al'amura na ta tsayawa cak a duniya. Wuraren da a baya ke cike da 'yan adam masu kai kawo a yanzu sun zama kufai saboda yadda aka takaita zirga-zirgar jama'a, kama daga rufe makarantu zuwa hana tafiye-tafiye da kuma dakatar da taruka.

Wani mataki ne da ba a taba dauka a duniya ba kan wata cuta. Amma yaushe za ta zo karshe kuma yaushe za mu dawo muna rayuwarmu kamar baya.

Fira Minista Boris Johnson ya ce ya yi amanna Burtaniya za ta iya shawo kan lamarin a cikin mako 12 kuma kasar za ta fatattaki coronavirus daga cikinta.

Amma ko yawan masu cutar ya fara raguwa nan da wata uku masu zuwa, to hakan fa ba yana nufin an kawo karshen matsalar ba ne.

Za a dauki tsawon lokaci kafin annobar ta gama tafiya - watakila ma shekaru.

Sai dai a bayyane take cewa wannan matakin da aka dauka na dakatar da dukkan al'amura ba zai dore ba. Hakan zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya da mu'amalar mutane.

Abin da kasashe ke bukata shi ne ''daukar matakin fita daga wannan kangi'' - hanyar da za a dage wadannan matakan a koma rayuwa yadda aka saba.

Amma ga alama coronavirus ba ta shirya tafiya ba a yanzu.

Idan aka dage matakan takaita walwalar jama'a da ke dakile yaduwar cutar, to kuwa lallai za a samu karin mutanen da za su kamu.

"Muna da babbar matsala kan yadda sabon matakin fita daga kangin zai kasance, da kuma yadda za mu fita din,'' a cewar Mark Woolhouse, wani farfesa kan cutuka masu yaduwa a Jami'ar Edinburgh.

''Ba Burtaniya ba ce kawai, babu kasar da ta tanadi matakin fita daga wannan kangi.''

Babban kalubale ne ga fannin kimiyya da zamantakewa.

Akwai hanyoyi uku na fita daga wannan balahira.

  • riga-kafi
  • mutane da dama su samu garkuwar jiki mai inganci da za ta iya yakar cutuka
  • ko kuma mu sauya yadda muke mu'amala a cikin al'umma

Kowanne daya daga cikin hanyoyin nan zai iya rage yaduwar cutar.

Riga-kafi - akalla wata 12-18

Riga-kafi na iya bai wa mutane kariya ta yadda ba za su kamu da rashin lafiya ba ko da sun yi mu'amala da mai cutar.

A yi wa mutane da dama riga-kafi, kusan kashi 60 cikin 100 na al'umma, kuma cutar ba za ta zamo annoba ba.

An yi gwajin riga-kafin kan wani mutum na farko a Amurka a wannan makon, bayan da aka bai wa masu bincike izini ba tare da bin al'adar da aka saba ta fara yin gwaji kan dabbobi ba.

Cibiyar binciken tana aiki ba kakkautawa, amma babu tabbas kan ko za a dace, sannan dole sai an yi riga-kafin a duniya baki daya.

Ana dai kyautata zaton za a dauki wata 12 zuwa 18 kafin a kammala samar da riga-kafin. Wannan kuwa lokaci ne mai tsawo ganin irin halin takurar da mutane ke ciki na dakatar da mu'amala da juna.

Farfesa Woolhouse ya shaida wa BBC cewa "Ba zai yiwu a ci gaba da bin wannan matakin ba a lokacin da ake jiran kammaluwar riga-kafi, wannan ba matakin bi ba ne.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tari na daya daga cikin alamun cutar Covid-19

Karfin garkuwar jiki - akalla nan da shekara 2

Matakin da Burtaniya ta dauka na gajeren zango don takaita yaduwar cutar ne, ta yadda asibitoci ba za su tumbatsa a rasa yadda za a yi da marasa lafiya ba - saboda idan asibiti ya cika da masu bukatar kulawar gaggawa, to ana iya samun mace-mace da yawa.

Idan masu fama da cutar suka ragu, hakan zai bayar da damar sassauta wasu matakan - sai dai idan an samu karuwar masu cutar to dole a sake sanya wasu matakan na takaita zirga-zirga.

Sai dai babu tabbas kan hakan. Babban mai ba da shawara kan harkar kimiyya na Burtaniya Sir Patrick Vallance, ya ce "sanya takamaimai lokaci na faruwar wasu abubuwa ba zai yiwu ba.''

Amma kuma hakan zai iya sa garkuwar jikin mutane da dama ta inganta.

Ko da yake, za a dauki tsawon shekaru kafin tabbatar hakan, a cewar Farfesa Neil Ferguson na Kwalejin Imperial da ke London: ''Muna magana ne a kan rage yaduwar cutar a matakin da muke fatan cewa kaso kadan na al'ummar kasar ne za su kamu.

''Don haka a karshe, idan muka ci gaba cikin wannan hali nan da shekara biyu ko fiye, to ba mamaki a wannan lokaci kaso mai yawa na al'ummar kasar na iya kamuwa.''

Amma akwai wata tambaya a kan ko garkuwar jikin wanda ya kamu na iya raguwa.

Akwai wasu cutukan da ke jawo mura da suke rage karfin garkuwar jiki don haka sai a ga mutane na yin cuta su kuma ci gaba da maimaita yin ta a rayuwa.

Zabi - babu tabbas kan ranar wucewar ta

Farfesa Woolhouse ya ce "Zabi na uku shi ne a tabbatar da samun sauyi kan yadda muke mu'amalarmu don hana cutar ci gaba da bazuwa.

Hakan zai hada da barin wasu matakan su ci gaba da aiki. Ko kuma a dinga yin gwaji akai-akai da kuma killace marasa lafiya don su fi karfin annobar.

''Mun yi ta yin gwajin farko-farko da bin diddigin wadanda ake zargin sun kamu amma bai yi aiki ba,'' in ji Farfesa Woolhouse.

Samar da maganin da zai magance Covid-19 zai taimaka wajen bin sauran matakan.

Za a iya amfani da su da zarar mutane sun nuna alamar cutar don hana su yada wa wasu.

Ko kuma yi wa marasa lafiya magani a asibiti don hana cutar yin muni. Wannan zai bai wa kasashe damar shawo kan kula da dumbin mutanen da ke da cutar kafin a bukaci takaita zirga-zirga.

Kara yawan gadaje a dakunan jinya na musamman zai taimaka wajen shawo kan cutar idan ta zamo annoba.

Na tambayi babban mai ba da shawara kan harkar lafiya na Burtaniya Farfesa Chris Whitty, mene ne matakinsa na fita daga wannan kangi.

Ya shaida min cewa" ''Matakan dogon zango, kamar dai samar da riga-kafi na daya daga cikin hanyoyin fita daga wannan hali kuma muna fatan hakan zai samu nan kurkusa.''

Kuna iya bin James a shafinsa nao Twitter

Labarai masu alaka