Coronavirus ta sa kasuwar kanana jiragen sama na haya ta bude

kananan jiragen haya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanonin masu kananan jiragen sama na alfarma a Najeriya sun bayyana cewa karin bukatar shiga kananan jiragen cikin makwanni biyu da suka gabata ta karu.

Hakan ya faru ne tun bayan da aka gargadi jama'a da su nesanta kansu da cudanya da mutane a sakamakon takunkumin zirga-zirga a tsakanin kasashe.

Karin da aka samu daga masu bukatar shiga kananan jiragen alfarmar dai na zuwa daga ciki da wajen Najeriya - duk dai saboda mutane da ke ta kokawar komawa gida ga iyalansu.

ExecuJet, wanda shi ne wani reshe na kamfanonin zirga-zirgar kananan jiragen sama na alfarma masu zaman kansu a Najeriya, ya ce bukatar jigilar fasinjoji na kasa da kasa ya ninka fiye da na makwanni biyu da suka gabata, yayin da ma'aikatansa ke kiyaye matakan kare lafiya da jami'an kiwon lafiya na tashar jiragen saman Najeriya ke samarwa.

Babban jami'in zirga-zirgar kamfanin ExecuJet Victor Mbachi, ya ce mafi yawan masu bukatar amfani da jiragen saman 'yan Najeriya ne da ke kokarin dawowa gida, a yayin da wadanda ke bukatar jiragen daga Najeriya ba 'yan kasar ba ne da ke niyyar komawa kasashensu.

Haka yake ga kamfanin Stargate Jets, da ke a Legas shi ma wani kamfani ne mai zaman kansa da ke zirga-zirga a ciki da wajen kasar.

Wani jami'in kamfanin ya shaida wa BBC cewa kamfanin ya samu "karuwar masu bukatar daukar hayar jiragen.

A lokuta da dama a baya, ana daukar hayar jiragen kamfanin sau daya ko sau biyu a cikin mako.

A wasu lokuta kamfanin yana samu a dauki hayarsa sau uku a cikin makonni biyu. Amma a makwanni biyun da suka gabata, ya samu kari tsakanin 10 zuwa 12.

Amma wadanda ke shigowa cikin kasar ta jiragen sama masu zaman kansu ba a kebe su daga daga bincikensu ba, bisa la'akari wannan shi ne tsarin nauyin da aka dorawa dukkanin kamfanonin jiragen sama a kasar.

A cewar Mbachi, an fada wa fasinjoji cewa su aika da hanyar tantance su ta na'urori ko wayoyin salula kafin isowarsu, wanda ganawa ta farko da fasinjoji za su yi ita ce ta haduwa da jami'an lafiya da ke tashar domin duba koshin lafiyarsu, kafin ma su tarbarsu su karbe su.

Zai yi wuya a ce ko hanzarta yin hakan ya zama wani yunkuri na kaucewar dokar hana hana zirga-zirgar shiga kasar da gwamnatin Najeriya ta sanya a baya-bayan nan kan kasashe 13 da suke fama da cutar COVID-19.

A bayyane yake cewa iyalai da yawa suna son su kasance tare da iyalai. Ga wadanda suke da karfin yin haka, suna ganin tafiya ta daidaiku wata farar dabara ce domin kaucewa kamuwa da cutar.

Dokar hana zirga zirga jiragen sama a kasar dai ta fara aiki tun a ranar 20 ga wannan wata.