Ko jihohin Najeriya sun shirya wa coronavirus?

. Hakkin mallakar hoto @DSGovernment

Cutar coronavirus ta zama annoba a fadin duniya inda a halin yanzu sama da mutum 400,000 ke dauke da cutar a fadin duniya.

Masana lafiya sun bayyana cewa har yanzu cutar ba ta da wani riga-kafi ko kuma sannanen magani da za a iya amfani da shi domin kare kai daga annobar.

Manyan kasashen duniya irin su Amurka da China tuni suka dukufa wajen nemo maganin wannan annoba sakamakon su ma ba su tsira daga wannan cuta ba.

Kasar Italiya ita ce kasar da cutar ta fi yi wa katutu sakamakon yadda jama'ar kasar ke mutuwa inda aka taba samun sama da mutum 700 sun mutu a rana guda.

Kasashe da dama ciki har da na nahiyar Afirka sun tashi tsaye wajen daukar matakai na kariya domin kare kansu daga wannan annoba ganin yadda cutar ke yi wa jama'a dauki dai-dai a manyan kasashen duniya.

Najeriya wadda ake yi wa kirari da uwa ma ba da mama a Afirka, sakamakon yawan jama'arta da kuma karfin tattalin arzikinta na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da cutar ta bulla kuma a kullum ake samun sama da mutum biyu da ake samun rahoton cewa sun kamu da cutar.

Kasar ta fara daukar matakai tun bayan da ta ga alamar cewa cutar ta fara bazuwa matuka inda ta fara da rufe tashoshin jirgin sama.

Sai dai a wannan makala BBC ta yi duba kan ko matakan da gwamnatoci ke dauka sun isa, ko da sauran rina a kaba?

Kasar na da jihohi 36 kuma kusan ko wace jiha a kasar na cikin fargaba da dar-dar na tsoron bullar wannan cuta ganin cewa a fannin lafiya, akasarin jihohin kasar na cikin wani hali.

Sai dai a fadin Najeriya, dakunan gwajin cutar coronavirus guda biyar ne kacal inda jihar Legas ke da biyu sai daddaya a jihohin Edo da Osun, birnin tarayya Abuja na da daya, idan aka hada duka biyar kenan.

A halin yanzu akwai kayayyakin gwaji da suka iso Najeriya wadanda hamshakin mai kudin nan na China Jack Ma ya bayar da tallafinsu kuma ana sa ran cewa za a rarraba su wadannan wurare biyar.

Wannan na nufin duk wanda ya kamu da wannan cuta daga wata jiha sai dai a dauki samfurin abin da ake bukata na mara lafiyar domin kai wa daya daga cikin wadancan jihohi a gwada.

Hakkin mallakar hoto Presidency

Shirin Gwamnatin Tarayya na yaki da coronavirus

Tun kafin bullar wannan cuta ta coronavirus, gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya tsaf ko da a ce wannan cuta ta bulla a kasar ,domin dakile ta.

A wata hira da kafar yada labarai ta CNN, shugaban hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu ya yi ikirarin cewa ''kasar ta yaki manyan cututtuka kamar Ebola da cutar Lassa, akwai kwararru da za su yaki wannan cuta''.

Sai dai yayin da wannan cuta ta fara yaduwa gadan-gadan a Najeriya, jama'a da dama na kokawa kan wannan hukumar, inda suke ganin cewa ba ta da karfin da za ta iya yakar wannan cuta ganin yadda kasar ke da miliyoyin mutane a jihohi 36.

Hukumar na kokari wajen wayar da kan jama'a musamman a shirye-shirye na gidajen rediyo da kuma shafukan sada zumunta musamman Twitter.

Dakta Tasi'u Ibrahim, wanda likita ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya bayyana cewa a ganinsa gwamnatin tarayya ba ta shirya yaki da coronavirus ba, ''domin ko asibitin fadar shugaban kasa ma bai shirya tunkarar wannan cuta ba ballantana sauran manyan asibitoci na fadin kasar.''

Ya ce akwai bukatar na'urar da ke taimaka wa masu cutar wajen yin numfashi wato ventilator, wajen kula da masu dauke da cutar.

Ya bayyana cewa kasar ba ta da isassun irin wadannan na'urori don haka batun a ce kasar ta shirya bai taso ba.

Jihar da wannan cuta dai ta fara bulla a Najeriya ita ce Legas, wane irin shiri za a iya cewa jihar ta Legas ta yi domin yaki da wannan cuta da kuma hana yaduwarta?

Legas

Ganin cewa akasarin masu dauke da wannan cuta a Najeriya na jihar ta Legas kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana, jihar kan zama farko wajen daukar matakai wadanda daga baya sauran jihohi ke bi.

Tuni jihar ta bayar da umarnin rufe makarantu da jami'o'i da haramta taron jama'a da kuma bayar da tazara tsakanin jama'a na akalla mita daya zuwa biyu tsakanin mutane.

Hakkin mallakar hoto @LSMOH

Daga baya jihar ta kara tsaurara matakai na rufe kasuwanni da shaguna inda sai shagunan kayayyakin abinci kadai aka yarda su bude su ma da matakai.

Duk da cewa gwamnatin jihar ta ce tana iyakar bakin kokarinta wajen ganin cewa ta shawo kan wannan matsala, masana harkokin yau da kullum a Najeriya irin su Dakta Abubakar Kari na ganin cewa babu wata jiha a Najeriya da za a iya cewa ta shirya tsaf domin tunkarar wannan matsala.

Ya ce ''Asibitocin koyarwa da kuma asibitocin kwararru na Najeriya na cikin wani hali na kusan babu komai a cikinsu''.

Ya ce akasari asibitocin babu isassun likitoci. ''Ko akwai isassun likitoci za a ga babu gadajen kwantar da marasa lafiya ko kuma na'urorin gwajin cututtuka.''

Ogun

Bayan jihar Legas, jihar Ogun ce jiha ta biyu da coronavirus ta bulla kuma kamar takwararta jihar Legas, jihar Ogun ta haramta duk wasu taruka da suka wuce mutum 50 da zuwa coci-coci da masallatai da kuma kulle makarantu.

Kamar sauran jihohi, gwamnatin jihar ta samar da wurin killace masu dauke da cutar ta coronavirus, kuma ta ce tana iya bakin kokarinta wurin yaki da wannan annoba.

Hakkin mallakar hoto @OGSGofficial

Jihar ta dauki matakai kan masana'antu da wuraren ayyuka kamar bankuna inda ta ce kada a samu sama da mutum 20 a cikinsu a lokaci guda.

Hakazalika, masu mota tasi an hana su daukar sama da mutum uku a cikin mota duk a yunkurin hana yaduwar wannan cuta

Duk da cewa wannan jiha ta Osun ta nuna alamun shiri na tunkarar wannan cuta, Dakta Tasi'u Ibrahim wanda likita ne a jihar Kaduna ya yi wa jihohin Najeriya kudin goro inda ya ce ''ba da gaske suke yi ba wajen yaki da cutar.''

''An bar shiri tun rani sakamakon yadda aka yi watsi da bangaren lafiya na kasar tun tuni. Ko a makonnin da suka gabata ganin yadda wannan annoba ke illa ga manyan kasashen duniya, ya kamata a ce kasar ta dauki mataki da wuri amma hakan bai yiwu ba.

Hakkin mallakar hoto @NCDCgov

Jihohin Kaduna da Kano da Neja

Duk da cewa har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba a samu bullar cutar cornavirus ba, wadannan jihohin sun dauki matakai tsaurara domin guje yaduwar coronavirus.

Jihohin sun rufe makarantun firamare da sakanadare da jami'o'i, sun hana duk wasu taruka na biki ko na addinai, da kuma takaita ma'aikata masu zuwa aikin gwamnati da kuma rage cunkoso a kasuwanni.

Jihohi da dama a Najeriya sun dauki irin wadannan matakai, sai dai masana lafiya da dama na ganin cewa ya kamata jihohin su kara mayar da hankali wajen yaki da wannan cuta, domin duk yadda ake tunanin wannan cuta ta wuce nan.

Cikin matakan da gwamnatin jihar Kano ta dauka, gwamnatin ta haramta wa manyan motoci kirar luxurious da suka taso daga jihar Legas zuwa Kano ganin cewa jihar Legas na daga cikin jihohin da cutar ta fi yaduwa a kasar.

Ita kuma jihar Kaduna ta rufe kasuwanni tare da neman gwamnatin tarayya ta dakatar da jirgin kasa da ke hada-hada daga Kaduna zuwa Abuja kusan sau hudu a rana.

Gwamnatin jihar Neja kuma ta saka dokar takaita zirga-zirga a jihar ganin cewa jihar na da kusanci da Abuja babban birnin Najeriya

Ya ce wannan ishara ce ga ma'aikatan gwamnati ganin cewa idan suka ki aikata abin da yakamata bayan sun samu dama, abin na iya dawowa kansu.

Wasu daga cikin wuraren killace jama'a na jihohin Najeriya

Ga misali wajen killace jama'a a Kano guda uku ne. AKwai daya a garin 'Yar Gaya mai gado 14.

Sai daya a Kwanar Dawaki wanda kamfanin Pfizer ya gina wa jihar tuntuni. Sai kuma an ware wani bangare a asibitin koyarwa na Aminu Kano wanda idan bukata ta taso za a iya amfani da shi.

A Jigawa kuma akwai cibiya mai daukar mutum 20, sannan gwamnatin jihar ta ce za su bude wasu cibiyoyin a yankunan masarautun jihar.

Hakkin mallakar hoto @RotimiAkeredolu
Image caption Wajen killace masu coronavirus na jihar Osun
Hakkin mallakar hoto @GovNiger
Image caption Gwamnatin jihar Neja ta samar da wajen killace masu dauke da cutar a babban asibitin jihar da ke Minna
Hakkin mallakar hoto @DSGovernment
Image caption Wurin killace masu coronavirus kenan na jihar Delta
Hakkin mallakar hoto @RealAARahman
Image caption Wurin killace masu coronavirus da aka kafa a asibitin kwararru na Sobi a jihar Kwara
Image caption Wurin killace masu coronavirus da gwamnatin Kano ta tanada wanda aka kafa a asibitin 'Yargaya.

Labarai masu alaka