Coronavirus: Wace ce matar da Buhari ya amince ta bai wa 'yan Nigeria agaji?

Sadiya Umar

Asalin hoton, Twitter

Tun bayan da cutar numfashi ta Covid-19 ta fara yaduwa a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana zirga-zirga tsawon kwana 14 a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja babban birnin tarayya inda da cutar ta fi yawa a kasar.

Haka kuma, wasu jihohin kasar sun sanya dokar hana fita na wani lokaci duk don a takaita yaduwar coronavirus.

Wannan doka na nufin baya ga ma'aikatan lafiya da masu sayar da kayan abinci da masu shagunan sayar da magunguna babu wanda ke da izinin fita ko bude wajen sana'arsa.

Shugaba Buhari ya sanar da matakin gwamnatinsa na bayar da agajin kudi da na abinci musamman ga masu karamin karfi a fadin kasar don rage masu radadin rashi da annobar za ta iya jefa su a ciki.

Shugaban ya umarci ministan harkokin noma, Sabo Nanono ya mika wa Ministar Agaji da Ci Gaban Al'umma Sadiya Umar Farouk rumbunan kasar da ke jihar Neja don rarraba kayan abincin ga mabukata.

Haka kuma, ya umarci Hukumar Kwastam ta mika kayan da ta kwace daga hannun masu saba dokar fasa kwabri don rabawa masu karamin karfi.

Hukumar Kwastam ta ce ta mika kayan da kudinsu ya kai Naira biliyan uku da miliyan dubu dari biyu da hamsin da daya da dubu dari takwas da dubu shida.

Kayan sun hada da shinkafa trailer 158 da man gyada jarkoki 36, 495 da man ja jarka 3, 428 da tumatirin gwamgwani kwali 136, 705 da taliya kwali 2, 951 da taliyar yara leda 1,2253 da atamfofi turmi 828 da leshi turmi 2,300.

Gwamnatin ta dora wa Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma karkashin jagorancin Minista Sadiya Umar Farouk alhakin raba kayan agajin a fadin kasar kuma tuni aka fara raba kayan.

Wace ce Sadiya Umar Farouk?

Asalin hoton, Twitter

Ba wannan ne karon farko da nauyin raba kayan agaji ya hau kan Sadiya Umar Farouk a Najeriya ba, duk da cewa ita ce ta farko da ta zama minista a sabuwar ma'aikatar da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kafa ta Agaji da Ci Gaban Al'umma a Najeriya.

Kafin ba ta sabon mukamin, Sadiya Farouk ce shugabar Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci rani da wadanda rikici ya raba da muhallansu.

Don haka, ana iya cewa ta dade tana aiki da masu karamin karfi da gajiyayyu.

A lokacin da take shugabar Hukumar, Sadiya Farouk ta kware a bangaren bincike da tattara bayanai da tsarawa da gyara rayuwar mutanen da suka fuskanci rikici ko yaki.

Sai dai a lokacin an yi ta ce-ce ku-ce kan zargin karkatar da dabino da Najeriya ta samu gudunmuwa daga kasar Saudi Arabia don rabawa musulmai a lokacin azumi. To sai dai Sadiya Umar ta sha musanta zargin aikata ba daidai ba.

Asalin hoton, Twitter

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sadiya Umar Farouk ta taba yin Jami'ar Kula da ke Asusun Jami'iyyar APC ta kasa daga watan Yunin 2013 zuwa watan Yunin 2014.

Daga nan ne kuma ta zama mamba ta majalisar kamfe din shugaban kasa a jam'iyyar ta APC, inda ta rike mukamin shugabar kwamitin tsarawa da sa ido da kaiwa-da komowa da samar da kudi.

Sadiya Farouk ta jagoranci tawagar da ta shirya zaben 2015 a jam'iyyar APC wadda kuma ta yi nasara.

Tsakanin shekarar 2011 da 2013, Sadiya Farouk ta rike mukamin Mai Kula da Asusun Jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), jam'iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2011

Jam'iyyar CPC na daya daga cikin jam'iyyu hudu a Najeriya da suka hadu suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2013.

Sadiya Umar Farouk 'yar asalin karamar hukumar Zurmi ce a jihar Zamfara kuma tana da digirin farko a bangaren Kasuwanci sannan digirinta na biyu a bangaren Diflomasiyya.

Ita ce mafi karancin shekaru a ministocin Shugaba Muhammadu Buhari inda take da shekara 45 da haihuwa.

Daga Karshe

Asalin hoton, Twitter

'Yan Najeriya da dama sun nuna tantama kan tsarin da za a bi wajen bayar da kayan agajin da kuma tantance su waye ainihin masu karamin karfi a kasar.

Akasari na ganin cewa Najeriya kasa ce da ba ta fiye ajiye alkalumma ba don haka zai yi wuya ma'aikatar agajin ta iya sanin adadin mutanen da ke cikin halin rashi a kasar.

Sai dai Sadiya Umar Farouq ta yi watsi da wannan zargi da 'yan kasar ke yi.

A hirarta da BBC ta ce "maganar ba mu da alkaluma ba gaskiya ba ce. Muna da hukumomi daban-daban a gwamnati wadanda aikinsu shi ne fitar da alkaluma kamar Hukumar Kididdiga ta Kasa da Hukumar NIMC kuma mu ma ma'aikatarmu na da nata alkaluman da rajistar wadannan mutane."

Ta ce kuma tun a shekarar 2016 ma'aikatarta ke amfani da wadannan alkaluma wajen bayar da agaji a Najeriya.

Ta ce akwai iyalai kusan miliyan biyu da dubu dari shidda a rajistar ma'aikatarta da ake bai wa agaji sannan akwai mutane kusan miliyan 11 a rajistar.

Batun tantance mabukata kuwa, Sadiya Farouk ta ce ma'aikatarta na aiki da masu unguwa da dagatai wajen zakulowa da tantance iyalan da ke fama da rashi.

"Muna mafani da shugabannin addini da shugabannin al'umma wajen fitar da wadannan mutanen daga nan kuma sai mu sa su a cikin rajista" a cewarta.

Ta kuma ce kullum suna bunkasa rajistar.

Asalin hoton, Twitter

Gwamnatin Najeriya dai ta ce baya ga wannan agaji da za a bayar don rage radadin annobar Covid-19, za ta ci gaba da shirye-shiryenta na rage radadin talauci wanda dama can take yi wa 'yan Najeriya masu karamin karafi.

Cikin irin wadannan shirye-shiryen har da na ciyar da dalibai abinci da bayar da tallafin kudi Naira dubu biyar da ake bai wa matan da mazajensu suka mutu da marayu da matan da mazansu ke da karamin karfi da dai sauransu a fadin kasar.

Asalin hoton, Twitter

Karin labaran da za ku so ku karanta