Lafiya Zinariya: Ciwon hanta a tsakanin mata
Lafiya Zinariya: Ciwon hanta a tsakanin mata
Latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:
Ciwon hanta cuta ce da ta rarrabu zuwa gida uku, daya kuma daga ciki ta sake rabuwa zuwa gida biyar.
Sai dai a cewar masana a fannin kiwon lafiya biyu daga cikinsu sun fi hatsari matuka ga bil’adama.
Haka kuma ita ce cutar da ake dauka da ke kisan mutane ta biyu mafi girma a duniya.
A shirin lafiya zinariya na wannan makon, likita ta yi cikakken bayani kan yadda ciwon hanta ke illa ga wasu muhimman kayan cikin mutum da kuma kwakwalwa.