Yadda ƙungiyoyin asiri na jami'o'i ke firgita 'yan Najeriya

  • Daga Helen Oyibo
  • BBC Pidgin, Lagos
Illustration with axe, machete, beret and calabash insignia of a Nigerian cult

Roland yana shekararsa ta farko a jami'a lokacin da ya shiga ƙungiyar asiri ta Buccaneers a Najeriya. Daga baya an gudanar da wani biki na rashin tausayi a cikin daji da tsakar dare.

Manya daga cikin mambobin ƙungiyar na ta waƙe-waƙe da shaye-shaye yayin da suka yi musu zobe, inda su kuma aka rufe fuskokinsu da ƙyalle tare da lakaɗa musu duka har zuwa asuba.

An yi bikin ne domin wanke duk wata gazawa daga jikinsu tare da sanya musu jarumta.

Da zarar ka shiga wurin nan kuma ka fito to ka zama wani sabon mutum," Roland ya faɗa wa BBC.

Waɗannan ƙungiyoyin asiri na jami'a na da sunaye iri-iri kamar; Vikings, Black Axe, Eiye (kalma ce da ke nufin tsuntsu a harshen Yarabanci) da kuma Buccaneers.

Suna da tsarin shugabanci irin na ƙungiyoyin fafutika, suna amfani da zaurance da kuma alamomi da ke alamta babban makamin ƙungiyar da kuma alamarta.

Ana yi wa mambobi alƙawarin kariya daga abokan adawa, amma akasari ana shiga ne domin samun mulki da ɗaukaka.

Irin waɗannan ƙungiyoyi haramtattu ne a Najeriya kuma an kama mabobinsu da dama tare da gurfanar da su a gaban kotu. Amma duk da haka ba su saurara da ayyukansu ba a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami'o'i, inda suke ci gaba da samun sabbin mambobi.

Dabarun kai hari da yi wa jama'a fashi

An sha zargin waɗannan ƙungiyoyi da tayar da fitina iri-iri, ciki har da kashe-kashe a jami'o'in Najeriya. Wani lokaci sukan yi wa malaman jami'ar barazana domin ya ba su mamaki mai yawa.

Wani zubin sukan ruɗi ɗalibai cewa za su haɗa su da manyan mutane domin samun kuɗi.

A jihohi kamar Legas da Fatakwal da ke da arzikin man fetur, ƙungoyin kan nemi matasa, inda suke mayar da su ɓata gari sannan a horar da su kafin su samu damar shiga jami'a.

BBC
Kisan gillar da aka yi a jami'o'in Najeriya

  • An harbe 14 a University of Nigeria a shekarar 2002

  • An yanka mutum 13a Jami'ar Jihar Kogi a shekarar 2019

  • an daddatsa mutum 5a Jami'ar Jihar Ribas

  • An fille kan mutum2 aka mayar da su turakun ragar kwallo a Jami'ar Abia a 2016

  • An kashe mutum 2a yayin da suke barci a Jami'ar Jos a 2002

  • An kashe mutum 1a Jami'ar Fasaha ta Enugu a 1997

Source: BBC

A watan Afrilu, sa'o'i da mazauna Legas da Ogun suka kafa wasu ƙungiyoyin sa-kai domin kare kansu daga wata ƙungiyar asiri mai suna One Million Boys da ake zargi da kai wa mutane hari a unguwanninsu.

Duk da dokar hana fita a jihar domin daƙile yaɗuwar cutar korona, wasu mazauna sun yi ta kukan yi musu fashi.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun ce ana amfanin da saƙonni irin waɗannan domin tsorata jama'ar gari

'Yan sanda sun musanta batun fashi a jihar, inda suka bayyana lamarin da cewa "labaran ƙarya ne" da 'yan ƙungiyoyin ke yaɗawa domin su samu damar kai harin na gaskiya.

Sai dai kuma sun tabbatar da cewa sun kama mutum fiye da 200 da ake zargi da shiga ƙungiyoyin na asiri haramtattu bayan wata fafatawa da aka yi tsakaninsu da ya kai ga mutuwar shugaban wata ƙungiya.

Dalilinda ya sa Roland ya shiga ƙungiyar asiri ta Buccaneer

Roland ya yanke shawarar shiga ƙungiyar asiri ne domin ya samu kariya a jami'arsu da ke gabashin Najeriya.

'Yan wata ƙungiya ce daban suka yi wa abokinsa fashi, abin da ya jawo rigima. Roland ya shiga riugimar kuma sau biyu ana lakaɗa masa duka.

Bayanan hoto,

'Yan ƙungiyar Buccaneer, an san su da yin rayuwa ta ƙasaita

Ya kai ƙara wurin jami'an tsaron jami'ar amma ba su iya ɗaukar wani mataki ba.

Roland ya nemi ƙungiya mai "sauƙin tashin hankli" kuma daga ƙarshe ya samu Buccaneers bayan ya ƙi yarda ya shiga Black Axe - wadda ta yi ƙaurin suna.

Sai dai shigarsa ke da wuya, sai ya shiga cikin fargabar abokan gabar ƙungiyarsu.

Rawar da Wole Soyinka ya taka wurin kafa ƙungiyoyi

Tun asali dai ba a san ƙungiyoyi da tashe-tashen hankula ba a Najeriya.

An fara kafa iri-iriensu tun a shekarar 1952 lokacin Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, wasu matasa masu tunƙaho da tunani suka kafa su.

Daga cikinsu akwai Wole Soyinka na Jami'ar Ibadan da ke Jihar Oyo ta kudu maso yammacin Najeriya.

Wole Soyinka
Getty Images
Ban taɓa tsammanin komai zai iya taɓarɓarewa ba"
Wole Soyinka
Pyrates founding member

Ɗaliban sun saka wa ƙungiyarsu suna National Association of Seadogs ko Pyrates domin yin kafaɗa-da-kafaɗa da wasu 'yan Najeriya masu hannu da shuni.

Waɗanda suka fara kafa ƙungiyar ana kiransu Magnificent Seven, suna ikirarin cewa su 'yan fashin teku ne, har ma suna ɗaura ƙyalle a kansu tare da ɗaukar gatari.

"Mun yi nishaɗi lokacin da muke tsaka da tsara yadda al'umma za ta kasance," Soyinka ya faɗa wa BBC.

Ya siffanta ƙungiyoyin na yanzu da cewa "'yan daba ne, marasa imani".

"Ban taɓa tsammanin wata ƙungiya ta jami'a za ta iya kashe mutum ba ko fashi ko fyaɗe ko kuma garkuwa da mutane.

"Ban taɓa zaton abin zai ɓaci haka ba. Amma me ya sa abin ya lalace haka? Maimakon a hukunta su a matsayin miyagu kamar yadda suke amma sai suke samun kariya daga iyayensu da 'yan uwansu," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matashin Wole Soyinka lokacijn da yake malamin jami'a a Jamai'ar Ibadan a shekarun 1960

Ƙungiyar Pyrates wadda har yanzu Soyinka yake cikinta, a yanzu ta mayar da hankali kan ayyukan jin ƙai da taimakon al'umma.

Yadda ƙungiyoyin suka zama na tashin hankali

Samun ɓaraka a ƙungiyar Pyrates a shekarun 1960 ya jawo fitar wasu ɗalibai, inda suka kafa Buccaneers da sauransu.

An samu kakkausar hamaayya a tsakaninsu, inda suke rige-rige wurin neman iko da mata da neman shiga a wurin 'yan siyasa, waɗanda suka fara daukar 'yan kungiyar aiki domin kai wa abokan hamayyarsu hari.

Wasu ƙungiyoyin sun fi wasu rikici amma dukansu suna firgita 'yan Najeriya.

Black Axe na cikin waɗanda suka fi gawurta. Sun fito ne a shekarun 1970 sannan kuma ana kiransu da Neo Black Movement. Waɗanda suka kafa ta sun ce sun yi hakan ne domin su 'yanta mutane baƙar fata.

Ana yawan zargin Black Axe da aikata kashe-kashe da kuma cin zarafi ta hanyar lalata a jami'o'i.

Ana zargin sojoji da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin asiri

A shekarar 1999, sun kashe mambobin ƙungiyar ɗalibai ta Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a Jihar Osun.

Su ma mambobin Black Axe sun fuskanci hare-haren rashin imani.

A Jami'ar Port Harcourt, an fille kan wani shugaban wata ƙungiyar asiri a shekarun 1990 sannan aka rataye kan bakin ƙofar shiga jami'ar a matsayin alamar nasara.

An sha zargin sojoji da ɗaukar nauyi tare da bai wa 'yan ƙungiyoyin asiri don su kai wa ɗalibai hari masu zanga-zangar neman a gudanar da zaɓe.

Omoyele Sowore
Getty Images
Sun caka min wuƙa a kaina, suka bar wuƙar a wajen suka kuma yi min tsirara''
Omoyele Sowore
Tsohon shugaban ɗalibai a jami'a

Ɗan jarida Omoyele Sowore ya san waɗannan ƙungiyoyi sosai lokacin da yake shugaban ƙungiyar ɗalibai a Jami'ar Legas.

A matsayinsa na shugaba, sai ya yi ƙoƙarin ya yi maganinsu.

"Na kusa rasa raina," Sowore ya shaida wa BBC.

A watan Maris na shekarar 1994 aka tsare shi da bindiga sannan aka yi masa allura da wani abu da ba a sani ba.

"Da yawansu suka far mani, suka caka mani wuƙa a ka sannan suka yi mani tsirara," in ji Sowore.

Daga baya wasu ɗalibai suka cece shi kuma suka kai shi asibiti.

Ba a iya Najeriya suke ayyukansu ba, an sha zargin ƙungiyar The Eiye da aikata laifuka a Nahiyar Turai.

'Yan sanda sun taɓa kama wasu mutum 23 a yankin Catalonia na ƙasar Spaniya da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar, inda aka ce sun yi safarar mutane da kuma ƙwayoyi da fasfo na boge.

Kazalika an zarge su da safarar ɗanyen man fetur zuwa Turai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsageru da aka fi sani da Area Boys na ayyukansu a titunan Legas

Ba kasafai mambobin ƙungiyar ke fita daga cikinta ba yayin da suke jami'a - waɗanda suka sake suka fita kuma ana iya halaka su.

Roland ya ce ƙungiyoyin na yi wa mutane alƙawarin tsaro ko iko duka na boge. Mambobi na cikin zulumi a ko da yaushe saboda ba su san lokacin da abokan hamayyarsu za su kawo hari ba.

"Za ka kasance cikin tsoro a mafi yawan lokaci ko da kuwa me ƙungiyar za ta ce, ko yaushe suna cikin tsoro."

Sunan Roland ba na gaskiya ba ne, an ɓoye ne saboda tsaron lafiyarsa.