BBC Africa Eye: An gano yadda ma'aikatan asibiti ke sayar da kayan kare mutane daga cutar korona a Ghana

Bayanan bidiyo,

Yadda ma'aikata lafiya ke sayar da kayan kare mutane daga cutar Korona a Ghana

Wani bincike da sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya gudanar ya nuna cewa wasu ma'aikata a asibitocin ƙasar Ghana suna sayar da kayan kariya daga cutar korona don samun makudan kuɗaɗe.

Fiye da ma'aikatan kiwon lafiya 2,000 ne a ƙasar suka kamu da cutar korona, tun bayan ɓarkewar cutar.

Ghana ta fuskanci ƙarancin kayan aikin kariya kamar takunkumi fuska.

Ɗan jarida Anas Aremeyaw Anas ya yi shigar burtu don gano yadda wasu ke saka rayuwar abokan aikinsu cikin haɗari domin samun kuɗi.

Anas Aremeyaw ya shaida jana'izar wani likita da ya mutu sakamakon cutar korona a kasar Ghana kuma mutane sanye da kayan kariya tun daga sama har ƙasa su ne ke aikin binne gawar, sannan kuma masoya da 'yan uwa ɗauke da furanni sun tsaya daga nesa.

Dr. Adu wani abokin aikin mamacin ne. Ya ce: "Babban likita ne mai ƙwazo. Mutuwarsa babbar hasara ce sosai ga asibitin da kuma Ghana baki ɗaya."

Fiye da likitoci 200 ne a Ghana suka kamu da cutar korona. Kullum ma'aikata na cikin kukan rashin isassun kayan kariya.

Lokacin da cutar korona ta ɓulla a kasar, gwamnati ta umarci asibitoci da su nemi kayan kariya daga cutar ta korona adadin da suke buƙata.

Ƙasar ta dogara ne wajen samun dubban kayan aiki daga masu bayar da tallafi, ciki har da tsohon shugaban kasar John Mahama.

A wani jawabi, John Mahama ya ce: "Muna gabatar muku da ɗaruruwan manyan rigunan kariya da kuma ɗaruruwan takunkumin fuska. Ku ne kan gaba wajen kare lafiyar jama'a daga cutar korona. Kuma dole ne mu goyi bayanku don ku iya kare mu."

To shin ko waɗannnan kayayyakin sun isa ga waɗanda suke buƙatarsu?

Wata tawaga ta yi shigar burtu a ɗaya daga cikin asibitocin Ghana mafi kyau.

Mun samu rahotanni daban-daban daga asibitin cewa wasu abokan aikinsu na fakewa da wannan annobar suna sayar da kayan kariya daga cutar korona a asirce.

Sun ambaci wani Mista Thomas Osei da ke aiki a sashen bayar da magani na asibitin.

Asalin hoton, Getty Images

A cikin mako biyu, mun yi shigar burtu inda muka ɗauki hoton bidiyon lokacin da ake sayar mana da tufafin kariya na ɗaruruwan daloli waɗanda Thomas ya sayar mana.

Ɗaya daga cikin hotunan da muka ɗauka ya nuna Thomas yana ciniki tare da miƙa wasu dogayen riguna.

Ya bayyana mana a fili cewa wannan su ne waɗanda ma'aikatan asibiti ke amfani da su.

A wata ranar daban, makarin fuska aka sayar mana, abin da ba a cika samu sosai a lokacin ba.

Wasu likitocin ma na ƙoƙarin samar da nasu da kansu. An ga Mista Osei a hoton bidiyon yana gwada wa wakilinmu yadda ake amfani da makarin fuskar.

Sanya takunkumi yana taimakawa wajen hana bazuwar cutar korona musamman ga likitocin da suke yaƙi da cutar. Makarin fuska yana da matukar mahimmanci.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A tsakiyar wannan annoba da ake ciki, hankalin Thomas ya kwance yana sayarwa 'yan tawagarmu tufafin kariya yana zuba kudin a aljihunsa.

Dr. Hadi Abdullah ɗaya ne daga cikin likitocin fiɗa mafi shahara a Ghana. Ya taɓa fuskantar matsalar rashin kayan kariya lokacin da yake aikin kula da masu cutar korona. Mun nuna masa hoton bidiyon da muka dauka lokacin da muka yi shigar burtu.

Dr Hadi Abdallah ya ce: "Makarin fuska ake sayarwa, abin mamaki wannan abin babu kyau sam. Wannan haɗamar ta yi yawa. Wannan fa shi ne zai kare su da su da abokan aikinsu."

Anas Aremeyaw: "Idan suka samu dama, za su iya yin irin wannan aikin rashin imanin duk da cewa suna sane idan m'aikatan lafiya ba su da waɗannan tufafin kariyar, suna saka rayukansu da kuma na iyalansu cikin haɗari.

"Ina ganin ba su cancanci su yi aiki a nan ba. Kuma ina ganin ya kamata a ɗauki tsattsauran matakin doka a kansu."

Mun tuntuɓi Mista Thomas kan waɗannan zarge-zarge, inda ya amsa cewa lalle ya sayar da kayan kariyar.

Ya shaida mana cewa ya sayar da su ne don harkar kasuwanci na ƙashin kansa.

Asalin hoton, MICHAEL TEWELDE

Ya ce kayayyakin ba na asibiti ba ne - har ma ya nuna mana rasitin kayan.

To amma ko da muka gudanar da bincike, kamfanin da ya rubuta rasitin ya bayyana mana cewa Thomas ne ya jagoranci cike rasitin, inda aka canza kwanan watan rasitin.

Wani babban jami'i a Asibitin Greater Accra Regional ya bayyana mana cewa bayan wani bincike na cikin gida, an dakatar da Mista Thomas daga aiki saboda sayar da kayan kariya a asirce, abin da ya saɓa wa dokokin asibitin.

Dukkan kayan kariya daga cutar korona da aka saya, an bai wa ma'aikatan lafiya da ke kan gaba wajen yaƙi da cutar.

Tambayar a nan ita ce, nawa ne yawan adadin kayan da suka ɓata kuma rayukan mutane nawa ne za su iya cetowa?