Yakin Libya: Abin da ya sa Masar za ta iya aika dakaru don goyon bayan Haftar

  • Daga Magdi Abdelhadi
  • Mai sharhi kan Masar
Islamist fighters in easern Libya- archive shot

Asalin hoton, AFP

Ka yi tunanin gidan makwabcinka ya kama da wuta sannan babu 'yan kwana-kwana a kusa da za ka kira su zo kashe gobarar da ke neman ci har gidanka da shafar iyalanka.

Haka Masar take kallon Libya tun bayan murkushe Shugaba Kanar Muammar Gaddafi da kawo karshen gwamnatinsa ta kazamar hanya a 2011.

Libya ba ta da wata takamaimiyar cibiya da ke aiki a yanzu, babu jami'in soja da na tsaro da ke da karfin fada a ji, abu mai muhimmanci, babu masu kula da tsaron iyakoki. Sannan makamai sun yadu sosai a kasar.

Gobarar da ke cin Libya ta soma yaduwa ne lokacin da kasar ta gaza amincewa da bin tafarkin ci gaba, mayaka sun samu damar yaduwa a kasar, an samu bullar mayakan jihadi da ke kokarin kafa daularsu ta Musulunci a Libya da wasu makwabtanta.

Masar - da sojojinta suka kifar da Shugaba Mohammed Morsi a 2013, da daure shi a gidan kaso da sauran shugabannin kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood - sun kasance wadanda ake hara:

  • A Yuni 2014, masu fasa kauri sun kashe masu gadin iyakar Masar shida
  • A 2017, tawagar mayakan Jihadi sun kutsa kai yankin Masar, su ka kai hari a shingen jami'an tsaro tare da kashe sojoji 16 da jikkata 13
  • A cikin Libya ita kanta, an kai wa leburorin Masar hari. A 2015 mayakan IS sun sace tare da fille kan wasu kiristocin Masar din 21, wadanda ake dangantawa da martani kan cire Shugaba Morsi daga mulki.

Libya bayan kifar da Gaddafi ta fada cikin kazamin yanayi da ya kassara siyasar kasar, wannan yanayi ya yadu a kusan duk yankunan Gabas Ta Tsakiya da arewacin Afirka.

Gwagwarmaya ce tsakanin masu siyasar addini, wadda Muslim Brotherhood ke kan gaba wajen dabbaka hakan da sauran masu gwama addini da ta su salon siyasar.

Yarjejeniyar da aka cimma karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta kafa gwamnatin wucin-gadi a Tripoli ta gaza kwace makamai a hannun mayaka ko cimma hadin-kan kasa ko sulhun da aka kafa ta a kai.

Turkiyya, kokarin ja da baya

Yayin da aka samu rabuwar kawuna a Libya tsakanin masu tsattsauran ra'ayin Musulunci da suka mamaye yamma da masu adawa da tsattsauran ra'ayi a gabashi - ba bakon abu ba ne a Masar, kasar da ta ayyana Muslim Botherhood a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, ta juya bayanta ga mutumin da ya kaddamar da yaki kan masu tsattsauran ra'ayin Musulunci a Libya, Kanar Khalifa Haftar.

Ya yake su ya kuma kakkabe su daga Benghazi da sauran manyan yankunan birane da ke gabashi da kudanci da mayaka suka mamaye.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Erdogan na yakar dakarun Janar Haftar a Libya

Sama da shekaru shida, burin Masar shi ne ta tsayar da rikicin Libya tsakanin iyakokin kasar, ta hanyar bai wa Janar Haftar goyon-baya.

Amma abubuwa sun sauya a karshen shekarar da ta gabata lokacin da Turkiyya - kasar da ke kan gaba wajen nuna goyon baya ga masu siyasar addini a yankin -yanke hukuncin goyon bayan gwamnati da aka kafa karkashin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

Ta ba da gudunmawar fasaha da sojoji wanda hakan ya taimaka wajen hana dakarun Janar Hafta ci gaba da kutsa wa don mamaye Tripoli.

Karin labarai kan rikicin Libya:

Bayanan bidiyo,

Mene ne boyayye a kan rikicin Libya?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A ci gaba da karfafa mata gwiwa a filin daga, Turkiyya da ke goyon-bayan gwamnatin Tripoli ta alkawarta jajircewa wajen ganin an kwato sauran yankunan kasar da murkushe Janar Haftar baki daya.

Wasu rahotanni masu ankararwa na cewa Turkiyya ta aike dubban mayakanta na Syria zuwa Tripoli da kuma kafa sansaninta a yammacin Libya, Masar ta shiga wani yanayi na ba ta da zabi dole ta tanka.

A Yuni, bayan sa ido kan yadda sojoji ke sarrafa makaman yaki da atisaye a sansaninsu da ke kuda da iyakar Libya, Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya yi wata sanarwa da ta janyo ce-ce-ku-ce.

'Jan daga'

La'akari da yanayin da kasashen Labarawa suka tsinci kansu, ya ce idan aka koma tarihi domin nazarin kan alaka tsakanin mutanen Libya da Masar, gwamnatin Masar na da izinin shiga tsakani domin kare kasashen biyu daga 'bata garin ketare''.

Bai ambaci wani abu kan Turkiyya ba, amma kowa ya fahimci inda ya dosa. Tawagar Libya daga shugabannin kabilu da ke sauraronsa lokacin da ya ambato haka sun ta yin sowar karfafa masu gwiwa.

Map: Libya and Egypt

Shugaba Sisi ya shata layi a kasar - tsakanin Sirte a Tekun Mediterranean da yankin da ke kewaye da sansanin Jufra a tsakiyar Libya - a matsayin inda Masar ta ''ja daga''

Duk wani kokarin tsallake wannan wuri da sojojin da ke biyaya ga Tripoli suka yi tamkar haifar da barazana ce ga tsaron kasa, a cewarsa.

Bayan 'yan kwanaki, 'yan majalisar Masar sun tilasta wa shugaban, wanda kuma shi ne hafsan hafsoshin sojojin kasar, ya tura dakaru karin dakaru.

Gwamnatin Tripoli ta mayar da martani a fusace ga barazanar Shugaba Sisi na amfani da karfin soji, ta bayyana hakan a matsayin ''kaddamar da yaki''.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Sisi ne Hafsan hafsoshin sojin Masar

Wannan babbar barazana ce ko kuma kumfar baki?

Masu sa ido daga wajen Masar sun yi saurin diga ayar tamabaya a kan dakarun sojin Masar da irin karfin da suke da shi.

A cikin kasar tattaunawa a bainar jama'a kan dakarun soji da ayyukansu ya haramta.

Kafofin yada labaran cikin gida sun yabawa shugaban da dakarun Masar a matsayin mafi karfi a duniya, inda suke kwantanta karfinsu da na Turkiyya, da aike sakon caccaka kan shugaba Recep Tayyip Erdogan da wadanda yake marawa baya a Tripoli.

Tsaka mai wuya

Sai dai akwai masu kira da babbar murya, gargadi da fargabar cewa Masar na iya dulmuyawa cikin mummunan yanayi irin na Libya.

Asalin hoton, Getty Images

Ana iya aminta da hujojjin da ke misali da cewa dakarun Masar na kaffa-kaffa da shiga tsakani, saboda gudun abin da zai je ya dawo tsakanin kasar da Libya.

Akwai kuma damuwar da ke nuna mai yiwuwa shiga wannan yaki ya assasa ko bude kofa ga bata garin da ke Libya su kwarara cikin Masar.

Sannan akwai rahotanni da ke nuna cewa tun shekarar 1973 rabon dakarun Masar da fita filin daga, yakin da ta yi na karshe shi ne da Isra'ila a Mashigin Suez da Hamadar Sinai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Masar Anwar Sadat da masu tsatsauran ra'ayin addini suka hallaka kusan shekaru 40 a lokacin da ya kai wa sojoji ziyara a inda suka ja daga a 1973

Yanayi da darussan da ta dauka daga yakin da ta yi da mayakan Jihadi a arewacin Sinai ba ta tabuka wani abin yabo ba.

Kaddamar da yaki a Libya da dakarunta ba lallai ya zo mata da sauki ba.

Duk da haka fitar da sanarwar jan daga, tamkar Masar ta samu kanta a cikin tsaka mai wuya ne.