Annobar cutar korona ta sa wanda ya kammala jami'a ya zama mai yasar kwata a Kenya

People working as part of government scheme to clear open sewers in Kibera, Kenya

Asalin hoton, Jeroen van Loon

Don taimaka wa daruruwan 'yan Kenya da suka rasa ayyukansu saboda annobar cutar korona, gwamnati na biyan mutane su wanke kwatocin da ke unguwanninsu kamar yadda 'yar jarida Andrea Dijkstra ta rubuta.

'Yan kasar, sanye da riguna masu ruwan rawaya da takunkumin fuska da takalma sau ciki, na tsaye cikin ruwan kwata wanda ke gudana tsakanin dakunan da aka gina da langa-langa a unguwar Kibera, unguwar marasa galihu kuma wadda aka gina ba a bisa ka'ida ba da ta fi ko wacce girma a Nairobi, babban birnin kasar.

Suna amfani da shebur wajen kwashe robobin ruwa da lalatattun takalma da kunzugun yara da bahaya daga cikin kwatocin.

"Aikin na da ban ƙyama," a cewar Abdul Aziz mai shekaru 33, wanda ke fargabar kamuwa da wata cuta kamar kwalara saboda yanayin aikin da yake yi marar tsafta.

"Amma wannan aikin ya fi zama a gida cike da yunwa da rashin aikin yi," a cewar mahaifin mai 'ya'ya biyu, wanda ya rasa aikinsa na direba a farkon annobar.

A cewar Hukumar Kididdiga ta Kenya (KNBS) sama da 'yan kasar miliyan 1.7 ne suka rasa ayyukansu a watanni ukun farko na annobar.

Wuraren shakatawa da otal-otal sun kasance a kulle saboda rashin masu yawon bude ido.

Sana'o'i da yawa sun durkushe kuma shagunan sayar da barasa sun rufe saboda dokar haramta sayar da barasar da dokar hana fita.

Don hana manyan matsaloli aukuwa, kamar karuwar aikata manyan laifuka da sace-sace a shaguna, gwamnati ta kaddamar da wani shiri mai fadi a kasar don samar da ayyukan yi ga 'yan kasar 200,000 da shekarunsu ba su haura 35 ba.

A Nairobi, shirin ya samar da ayyukan yi ga mutum 55,000 da aka kasa gida biyu, ko wane bangare na aiki kwanaki 11 duk wata.

Bashi

Mista Aziz wanda ke zaune a Kibera na farin ciki da shirin na gwamnati da ya samar masa aiki a karshen watan Yuli.

Duk da cewa albashin da ake biyansa na shilling 455 (kwatankwacin $4.15) a rana ya yi kadan, ya amince ya ci gaba da aikin.

A baya yana karbar $13 a rana a matsayinsa na direba.

Yana amfani da rabin kudin da yake samu a yanzu wajen biyan bashin da ya karba a wajen abokansa da shaguna a lokacin da aka kore shi daga aiki a watan Afrilu.

Abin da ke ragewa a hannunsa da kyar yake isarsa biyan kudin haya da sayen abinci. A dalilin haka, sau daya a rana iyalinsa ke cin abinci.

Ana wullo bahaya

"Wannan annobar ta lalata mana rayuwa," a cewar Sharon Sakase mai shekaru 23, wadda kuma ke aiki a shirin na kwashe kwata a Kibera inda take zaune da mahaifiyarta da ƙannenta mata uku da ƙaninta namiji daya da 'ya'yanta biyu duk a cikin ɗan ƙaramin gidan da aka gina da kwanon rufi.

Asalin hoton, Jeroen van Loon

Bayanan hoto,

Akwai tsananin rashin ban daki a Kibera kuma sau da yawa ana wulla ba hayan da aka kulle a leda ne cikin kwatoci

Mahaifiyar, wadda ba ta da miji ta samu tallafin karatu daga wani coci don ta karanci ɓangaren yawon bude ido.

Sai dai, an ɗage fara karantun nata watanni bakawai da suka wuce kuma shagon gyaran gashin da ta ke aiki a baya ba a bukatarta saboda mutane sun daina zuwa dalilin cutar korona.

"Akwai wahala yin wannan aikin mai cike da kazanta," in ji Misis Sakase, a daidai lokacin da aka wullo wata leda mai dauke da bahaya cikin kwatar da ke kusa da ita.

Wannan leda ce da mazauna unguwar da ba su da ban daki ke yin bahaya a ciki.

"Duk da haka, ina farin ciki da wannan aikin," a cewar matashiyar mahaifiyar. "Yanzu ina samun 'yan kudin sayen abincin da ni da iyalina za mu ci."

Ta kasance mai rike da gidansu tun da mahaifiyarta ta rasa nata aikin na aikatau lokacin annobar korona.

Fargabar cin hanci

Gwamnatin Kenya ta dauki tsauraran matakai don yaki da yaduwar cutar, bayan da aka tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar ran 13 ga watan Maris.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kasar na takaicin zarge-zargen cin hanci da rashawa bisa kayan aikin cutar korona wanda har yanzu ake bincikawa

An sanya dokar hana fita, an rufe inda cutar ta fi yawa ruf kamar Nairobi da yankin da ke gabar teku tsawon wata uku, kuma an rufe filayen jirgin sama tsawon wata biyar sannan mutane sun dinga aiki daga gida.

A dalilin haka, kashi 17 cikin 100 na 'yan Kenya a yanzu ba sa iya daukar nauyin kansu yayin da kashi 47 cikin 100 ne kawai ke da wata hanyar samun kudi a kai a kai, kamar yadda wani binciken kamfanin FSD Kenya ya nuna.

Don rage radadin talaucin, gwamnati ta dauki wasu matakai. An rage haraji kuma an cire haraji gaba daya ga 'yan Kenya da albashinsu bai kai $221 a wata ba.

"Kanana da matsakaitan sana'o'i da yawa sun durkushe, inda hakan ya sa mutane da yawa suka rasa ayyukansu. Wannan ragen harajin bai amfana masu komai ba," a cewar masanin tattalin arziki a Kenya Kwame Owino.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Asusun lamuni na duniya (IMF) ya bai wa Kenya bashin dala miliyan 739 don rage radadin Covid-19.

Sai dai Mista Owino na ganin cewa gwamnati ta gaza amfani da kudin baitul mali cikin sauri kuma yadda ya kamata don agaza wa mutane a lokacin annobar saboda wasu manyan ayyukan gwamnati da cin hanci da rashawa.

"Da farko, dole a biya ma'aikatan gwamnati albashi kuma dole a biya basussuka," a cewar Mista Owino, darekta a Makarantar Harkokin Tattalin Arziki a Kenya.

Bashin da ake bin Kenya ya karu zuwa dala biliyan 54.3 a watan Yunin wannan shekarar, ko kashi 62 cikin dari na gaba daya kudin da kasar ta samu, wanda ya ja Babban Bankin Duniya ya yi wa kasar gargadi a bara.

Gwamnati na binciken zargin cin hanci da rashawa bayan da aka ce wani bangare mai yawa na kayan agaji, ciki har da takunkumi da na'urar numfashi ta ventilator da mai arzikin nan na kasar China Kack Ma ya bayar, sun ɓata bayan da suka iso kasar, da kuma wasu ɓangarorin bashi da kudaden agaji daga hukumomi kamar Babban Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya.

'Abokanaina sun sa rai zan samu aiki mai kyau'

Ga wadanda suke kwasar kwata a Kibera karkashin shirin na gwamnati, akwai fargabar yadda gaba za ta kasance.

Asalin hoton, Jeroen van Loon

Bayanan hoto,

Jack Omonai, sanye da bakar riga, cikakken mai hada shafin intanet ne

"Kowa a Kibera na neman aiki ido rufe," in ji Jack Omonoi mai shekaru 25, wanda ya kammala karatunsa shekaru biyu da suka wuce a matsayin mai hada shafukan intanet.

Yana aiki ne a wani kamfanin shirya taruka kafin annobar amma ya ce dole aka soke komai kuma hakan ya tursasa masa shiga shirin kwasar kwata saboda ba shi da yadda zai yi.

"Abokanaina sun san na je jami'a kuma sun sa rai zan samu aiki mai kyau. Yanzu suna ganina ina kwasar bahaya daga kwata," ya ce a lokacin da yake kallon kasa cikin takaici.

"Lamarin na da matukar ban taƙaici.

"Kuma babu wanda ya san lokacin da za mu ga karshensa."