Taswirar iyakar Isra'ila da Ƙasashen Larabawa

Sama da shekaru 70 bayan Isra'ila ta samu 'yancin kai, har yanzu ba a samu matsaya kan iyakokin ƙasar ba. Yaƙi, da yarjejeniya da kuma mamaya sun sauya fasalin ƙasar ta Yahudawa bayan wani lokaci, kuma wasu yankunan ƙasar ba su fito fili ba.

Ga wasu taswirori da muke da su da suke nuna ko me ya sa hakan.

Ƙasar da ta zama Isra'ila ta shafe shekaru kusan 400 ƙarƙashin mulkin Daular Usmaniyya ta Turkiyya.

Bayan Yaƙin Duniya Na Farko, da kuma rushewar Daular Ta Usmaniyya, wani yanki da ake kira Palestine - yankin da yake yamma da kogin Jordan shi ma an san shi a matsayin yankin Yahudawan Isra'ila - inda aka fitar da yankin aka kuma bai wa Birtaniya ta kula da shi.

Cikin abubuwan da aka buƙaci Birtaniya ta yi kan kafa Palestine shi ne samar da ƙasa guda ga Yahudawa, matuƙar hakan ba zai shiga haƙƙin mazauna yankin waɗanda ba addinin Yahudanci suke yi ba.

Samun wasu 'yan aware daga cikin Larabawan yankin sakamakon ƙaruwar wasu ƙananan ƙungiyoyi na Yahudawa musamman bayan kirƙiro da tsarin Nazism a Jamus a shekarun 1930 - ya ƙaro jawo ƙaruwar rikici tsakanin Yahudawa da Larabawa a Palestine.

Birtaniya sai ta miƙa wannan rikicin ga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda a 1947 majalisar ta fitar da kudirin raba Palestine zuwa ƙasa biyu -ɗaya ta Yahudawa ɗaya kuma ta Larabawa, inda aka so yankin Jerusalem da Bethlehem ya zama babban birni.

Shugabannin Yahudawa na lokacin sun amince da wannan yunƙuri, sai da Larabawa kuma ba su amince ba.

Jagororin Yahudawa a Palestine a shekarar 1948 suka bayyana kafa ƙasar Isra'ila a ranar 14 ga watan Mayu, bayan riƙon da aka bai wa Birtaniya ya kawo ƙarshe kenan, duk da cewa ƙasar ba ta bayyana inda iyakarta ta tsaya ba.

Washe gari sai ƙasashen Larabawa biyar suka kai hari ga Isra'ila, inda harin ne ya bude kofar yakin neman 'yancin kai na Isra'ila.

Yaƙin ya kawo ƙarshe a 1949 bayan an ta samun yarjejeniyar tsagaita wuta daban-daban, inda aka yi ta yarjejeniya tsakanin Isra'ilar da makwaftanta, tare da samar da iyakoki inda har aka samar da abin da ake kira Zirin Gaza a halin yanzu, (mallakar Masar) da kuma Gabashin Jerusalem da kuma gaɓar yamma da kogin Jordan (mallakar Jordan).

Ƙasashen Larabawa da ke zagayen suka ƙi amincewa da Isra'ila a matsayin ƙasa, wanda hakan na nufin iyakokin ba a bayyane suke ba.

Babban sauyin da aka samu a iyakokin Isra'ila ya zo ne a 1967, lokacin da aka yi yaƙin da ake kira Six Day War, ma'ana yaƙin da aka yi cikin kwana shida wanda yaya Isra'ilar ta mallaki Yankin Sinai da Zirin Gaza da Yamma Da Kogin Jordan da kuma wani yanki daga Tuddan Golan na Syria - wanda hakan ya ƙara yawan yankunan da ke ƙarƙashin Isra'ila. haka zalika Isra'ilar ta karɓi Gabashin Juresalem - inda ta mayar da duka birnin babban birninta - da kuma Tuddan Golan.

Wannan matakin da Isra'ila ta ɗauka ƙasashen duniya ba su amince da shi ba, har sai lokacin da Amurka ta sauya matsayarta a kai a lokacin mulkin Trump, wanda shi ne shugaba na farko da ya yi hakan.

Wani babban abu kuma sai ra'ayoyin mutane a fadin duniya sula fara kallon Gabashin Jerusalem da kuma Tuddan Golan a matsayin yankin da aka mamaye.

A karon farko, an amince da iyakar Isra'ila guda ɗaya a hukumance a 1979, kuma Masar ce ta yi hakan. A ƙarƙashin wata yarjejeniya, an fitar da iyakar Isra'ila da Masar inda kuma Isra'ila ta janye duka sojojinta da kuma 'yan ƙasarta daga Yankin Sinai, inda aka kammala hakan a 1982.

Wannan ne ya sa Isra'ila ta mallaki Zirin Gaza, da Gabashin Jerusalem da kuma Tuddan Golan.

A irin wannan lamari, Isra'ila na da iyaka da Gaza tun bayan da ƙasar ta janye sojojinta da 'yan ƙasar mazauna yankin a 2005, amma Gaza da kuma Yamma Da Kogin Jordan ana ɗaukarsu a matsayin wani yanki mallakar Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ba a fitar da iyakokin ba a hukumance.

Ana ganin za a fitar da matsaya kan batun Yamma Da Kogin Jordan da Gaza da Gabashin Jerusalem a tattaunawar da za a yi tsakanin Yahudawan Isra'ila da kuma Falasdinawan da ke zaune a yankunan da ke ƙarƙashin Isra'ila, sai dai shekaru aru-aru da aka shafe an tattaunawa kan lamarin bai haifar da wani abin a zo a gani ba.