Gobarar Tanka: Mutum sama da 200 suka mutu a shekara biyu a Najeriya

gobarar tankar mai

Asalin hoton, Getty Images

Gobara ko hadarin tankar mai na daga cikin haɗura mafi muni da aka sha gani a Najeriya da ke salwantar da rayuka da ɗumbin dukiyoyi.

Aukuwar hadarin da ƙaruwarsa a cikin shekarun baya-bayan nan na haifar da damuwa tsakanin matafiya da 'yan kasa.

Ko a wannan makon an samu irin wannan mummunan hadari a jihar Kogi da ya yi sanadi akalla rayuka 28, ciki har da 'yan makaranta da iyalai 'yan gida daya, a cewar hukumomi.

A lokuta da dama irin wannan hadari na aukuwar ne a hanyar da ake yawaita hada-hada ko cunkoson ababen hawa.

Tsawon shekarun da aka dauka ana samun irin wannan hadari da ke sanadi rayuka, kusan babu wani sauyi da aka gani ko hubbasa wajen rage ko dak'ile aukuwar irin wannan haduran a Najeriya.

A kasashen da aka samu ci gaba da wuya ka iske ana dakon mai ko kaya masu nauyi ko hadura ta hanya mai cunkoso ko cikin gari.

Hadura mafi muni na motar dakon mai da Najeriya ba za ta manta da shi ba shi ne wanda ya auku a titin Okobie na jihar Ribas, inda mutum 121 suka mutu daruruwa suka samu munanan raunuka, baya ga ɗumbin motoci da Babura da suka kone kurumus.

Sai wanda ya faru a Ibadan a Nuwamban shekara ta 2000 inda mutane tsakanin 100 zuwa 200 suka mutu.

Ga ire-iren waɗannan hadura da suka faru cikin shekara biyu a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A Ranar 6 ga watan Satumban 2020, gidaje biyar da shaguna 49 sun kone ƙurmus sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a hanyar Lambata da ke karamar hukumar Gawu Babangida a Neja.

Gobarar ta auku ne bayan tankar dakon mai ta yi karo da wata tirela a kokarin kaucewa wani ƙaton rami. Babu mutum guda da ya mutu saboda hadarin ya auku ne a ranar da ba a buɗe kasuwa ba haka zalika mutane ba su fito ba.

A ranar 26 ga watan Agusta 2020, mutum biyu sun tsallake rijiya da baya a lokacin da wata mota ɗauke da lita dubu 33 na mai ta faɗi a titi da haddasa gobara a gaban ƙofar kwalejin fasaha ta Gwallamaji, a Bauchi. Ganau sun ce hadarin ya auku ne da misalin 8 na dare inda nan take mai ya rinka malalewa wuta kuma ta kama.

A ranar 14 ga watan Agusta 2020, a wani gidan mai da ke Irete na Jihar Imo, tankan mai yayi gobara tare da sanadi rai guda da kona motoci biyu kurumus.

A ranar 22 ga watan Yuli 2020 wani iftila'i ya auku a babban titin Benin-Sapele-Warri lokacin da tankan da ke dakon mai ya yi bindiga a hanyar da mutane ke hada-hada.

Jaridar Guardian a Najeriya ta rawaito cewa mutum 20 suka rasa rayukansu bayan ƙonewa ƙurmus, sannan motoci akalla 10 sun ƙone.

Ranar 17 ga Oktoban 2019, wata uwa da jaririnta sun ƙone ƙurmus yayin da gine-gine sama da 40 suka rushe a gobarar da tankar mai ta haifar a unguwar Iweka da ke Onitsha a Jihar Anambra.

Sannan shaguna sama da 500 da ke rufe sun ƙone. Gobara ta auku ne bayan motar ta ƙwace a hannun direba abin da ya kai ga kan motar ya rabu da jikinta nan take mai ya soma malalewa, gobara ta tashi.

A daren 30 ga watan August 2019, an samu rahotan mutuwar mutum guda, sannan 10 sun jikkata bayan fashewar motar dakon mai a daidai Dikko da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna. Sannan motoci da dama sun ƙone.

A ranar 2 ga watan Yuli 2019, a ƙalla mutum 50 aka ba da rahotan mutuwarsu, 100 sun jikkata sakamakon bindigar motar dakon mai.

Rahotanni sun ce mutanen sun hallaka ne a lokacin da suke rige-rige kwasar feturin da ke tsiyaya daga jikin tankin motar da ta yi haɗari.

Motar ta faɗi ne a lokacin da direba ya yi kokarin kauce wa ramuka a titin kauyen Ahumbe na Jihar Benue.

Asalin hoton, Others

Ranar 29 ga watan Afrilu 2019, mutum a ƙalla bakwai suka tsallake rijiya da baya a lokacin da motar dakon mai ta yi bindiga a harabar wani gidan man Bolek Filling Station a kusa da jami'ar kimiyya ta Makurdin jihar Benue.

Ranar 14 ga watan Afrilun 2019, an samu rahotan mutuwar mutum 12, sannan mutum 16 sun samu munanan raunuka a fashewar tankin da wata mota ta yi dakonsa a jihar Gombe.

Kamfanin dilancin labaran faransa AFP, ya ruwaito cewa motar ta ƙwacewa direba, a lokacin da ya yi kokarin kaucewa yin taho mu gama da wata ƙatuwar mota a kan wata gada da ke wajen gari.

12 ga watan Janairu 2019, an tashi da labarin mummunan hadari motar dakon mai da ya yi sanadi rayuka sama da 60 da dukiyoyi a titin Calabar jihar Cross Ribas.

A ranar 4 ga watan Oktoba 2018, wata mota da aka loda wa lita dubu 33 na man fetur ta fadi a titin Akure-Owo na Ondo, ta haifar da gobarar da ta yi sanadin rayuka huɗu da wani jariri.

Ganau a lokacin aukuwar hadarin sun shaida yadda motoci da gidaje da shaguna da ke kusa da wannan titi suka kone ƙurmus.

Ranar 1 ga watan Oktaba 2018, fashewar tankar mai a cikin dare ya haddasa asarar dukiyar ɗumbin miliyoyin Naira da kona motoci 10.

Hadarin ya auku ne a titin Lages-Badagry, sai dai ba a samu asarar rai ba.

A ranar 10 ga watan Satumba wannan shekara ta 2018, Akalla mutum 35 suka rasa rayukansu, daruruwa suka jikkata lokacin da wani tankin dakon gas ya yi bindiga a jihar Nasarawar arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce fashewar ta auku ne lokacin da ake kokarin sauke gas a wani gidan mai da ke titin Lafia-Makurdi.