Mike Pence: Wane ne mataimakin Shugaba Trump Amurka?

Bayanan bidiyo,

Why did Trump pick Pence for VP?

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence, ya zama ɗaya daga cikin mutanen da ke da faɗa a ji a Fadar White House. Shin wane ne shi?

Sama da shekara huɗu, ya kasance mataimakin shugaban ƙasa mai ƙoƙari, yana daga cikin masu yanke shawara kan manyan muƙaman da ake bayarwa, kuma yana daga cikin masu magana a madadin gwamnatin ƙasar.

Mista Pence kuma ya kasance mai jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a jaridu, a 'yan kwanakin nan, ya kasance kan gaba wurin jagorantar yaƙi da cutar korona a ƙasar.

Ban da haka ma, an ɗora wa Mista Pence alhakin kawo tsare-tsare kan hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka.

Mista Pence ya shiga siyasar White House gadan-gadan a 2016, bayan Mista Trump ya same shi har gida inda ya roƙe shi da ya zama mataimakinsa a zaɓen ƙasar.

Abu mai sauƙi ne domin gano dalilin da Mista Trump ya nemi Mista Pence ya zama mataimakinsa, Mista Pence na yawan caccakar tsare-tsaren Mista Trump.

Mista Pence ya soki tsarin da Mista Trump ke da shi na haramta wa Musulmai shiga Amurka inda ya ce wani abu ne na cin mutunci kuma wanda ya saɓa wa tsarin mulki.

Ya kuma soki Trump ɗin kan wasu kalamai da ya yi kan wani alƙali mai suna Gonzalo Curiel, inda ya ce kalaman da Trump ɗin ya yi ba su yi daidai ba.

A yanzu, ana ganin Mista Trump a matsayin mutum na biyu da ke da ƙarfi bayan shugaban ƙasa kuma mai biyayya a gareshi inda a yanzu, mawuyaci ne ya caccaki Trump din.

An yi ta samun gargada a tafiyar tasu a shekara huɗu da suka gabata.

Batu na farko da ya jawo ce-ce-ku-ce daga wurin Mista Pence ya faru ne a 2017, inda yake amfani da manhajar email ta kansa ba ta gwamnati ba, a lokacin da yake gwamnan jihar Indiana.

Bayan ya daɗe yana caccakar Hillary Clinton kan saƙon email ɗinta, an zarge shi da yin munafunci, sai dai ba kamar ita ba, ba ya karɓar saƙonni muhimmai ko kuma bayanan sirri ta manhajar email ɗinsa ba na gwamnati ba.

An kuma caccake shi kan batun da ya yi kan cutar korona inda ya ce ana zuzuta annobar.

Mai sassaucin ra'ayi

Mista Pence ya taso tun yana yaro inda yake bin aƙidar Katolika tare da 'yan uwansa biyar a Columbus da ke Indiana.

A 2012, ya shaida cewa masu aƙidar sassaucin ra'ayi irin John F Keneddy da kuma Martin Luther King Jr suka ja ra'ayinsa ya shiga siyasa.

Mista Pence, wanda ya ce shi Kirista ne kuma mai ra'ayi irin na 'yan mazan jiya kuma ɗan Jam'iyyar Republican, ya zaɓi Jimmy Carter a zaɓen 1980.

Ya ce sai a makaranta ne ya haɗu da matarsa, Karen, wadda ke bin aƙidar Evangelical inda a lokacin ne ra'ayinsa ya fara sauyawa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Tsohon gwamnan ya kuma shafe shekaru 12 a majalisa

Mista Pence ya kasance gwamnan Indiana daga 2013 zuwa 2017, ban da haka kuma ya kasance ɗan majalisar tarayya na Amurka na tsawon shekara 12.

A lokacin da yake shekara biyunsa ta ƙarshe a Washington, ya kasance shugaban 'yan Republican na majalisar, muƙamin shi ne na uku mafi girma a tsarin Republican.

Mista Pence ya an taɓa tunanin cewa zai yi takarar shugabancin Amurka a baya. A 2009, ya je wasu jihohi inda a lokacin ne aka fara yaɗa ce-ce-ku-ce cewa yana da niyyar tsayawa takara.

A lokacin yaƙin neman zaɓen 2016, Mista Pence a ko da yaushe yana bin Trump wurin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ya yi a lokacin shi ne kare Shugaba Trump a duk lokacin da aka fara caccakarsa.

Ya kare ɗan gidan Mista Trump a lokacin da ya kwatanta 'yan ci-rani da alawar Skittles.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mataimakin shugaban kasa Mike Pence shi ya jagoranci kwamtin yaƙi da korona a Fadar White House

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya taɓa saɓani da ra'ayin Trump cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama ba a Amurka aka haife shi ba (daga baya Mista Trump ya sauya ra'ayinsa game da batun).

Dokokin da ke janyo ce-ce-ku-ce

Lokacin da yake gwamna, ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma bayan sanya hannu kan dokar 'yancin addini.

Masu sukar dokar sun ce dokar tana nuna wariya ga masu maɗigo da luwadi ta hanyar ƙyamatarsu a wuraren kasuwanci saboda kishin addini.

Bayan matsin lamba, daga baya ya sauya dokar inda aka haramta nuna wariya ga ƴan maɗigo da luwaɗi.

Mutum ne mai tsananin adawa da zubar da ciki.

Mista Pence, ƴaƴansa uku kuma mabiyin addinin kirista ne kuma, ya taɓa sanya hannu kan dokar zubar da ciki mafi tsauri a lokacin da yake gwamna.

Indiana ta haramta zubar da ciki, kafin daga baya Kotun Ƙoli ta yi watsi da dokar.

A shekarar 2017 Mista Pence ya kasance mataimakin shugaban ƙasa na farko da ke kan mulki da ya halarci babban gangamin adawa da zubar da ciki, kuma tun da daga lokacin duk shekara yana halartar gangamin.