Coronavirus a Afirka: Dalilai biyar da suka sa cutar korona ba ta yin illa sosai a nahiyar

  • Daga Anne Soy
  • Senior Africa correspondent
People wearing face masks as a precautionary measure against the coronavirus (Covid-19) come to Entoto Kidane Mehret Church as Ethiopian Orthodox Christians celebrate Filseta Day after the end of fasting for 15 days without consuming animal products in commemoration of Assumption of Mary in Addis Ababa, Ethiopia on August 22, 2020

Asalin hoton, Getty Images

An yaba wa kasashen Afirka da dama saboda kokarinsu wajen dakile yaduwar cutar korona duk da yake ba su da ingantattun tsare-tsaren kula da lafiya.

Nahiya, wadda ke da yawan al'umma fiye da biliyan daya, tana da mutum miliyan 1.5 da suka kamu da cutar korona, a cewar kididdigar Jami'ar John Hopkins.

Wadannan alkaluma sun yi kasa sosai idan aka kwatanta da mutanen da cutar ta kama a Turai, Asia da kuma yankin Amurka, inda rahotanni ke nuna cewa alkaluman na ci gaba da raguwa.

Kusan mutum 37,000 ne suka mutu sakamakon cutar a Afirka idan aka kwatanta da kusan mutum 580,000 da cutar ta kashe a kasashen yankin Amurka, da kuma 230,000 da suka mutu a Turai, yayin da ta kashe 205,000 a Asia.

Duk da yake ba a yin gwaji sosai domin gano masu fama da cutar a Afirka, amma babu wata alama da ta nuna cewa an samu gagarumar mutuwa sakamakon kamuwa da Covid-19, a cewar Dr John Nkengasong, shugaban hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka.

Mene ne ya sa ba a samun yawaitar masu mutuwa sakamakon cutar ta korona a Afirka?

1: Daukar mataki da wuri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sake bude galibin wuraren ibada bayan an sassauta dokar kulle

Ranar 14 ga watan Fabrairu aka bayar da rahoton farko na bullar korona a Afirka inda lamain ya faru a kasar Masar. An yi ta nuna fargabar cewa cutar za ta yadu sosai har ta fi karfin tsarin kiwon lafiyar nahiyar wanda ke fuskantar kalubale.

Don haka, tun da farko, gwamnatocin Afirka sun dauki kwararan matakai da zummar dakile yaduwar cutar.

Matakan da aka dauka sun hada da hana yin musabaha, da yawaita wanke hannu, da yin nesa-nesa da juna da kuma sanya takunkumi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu kasashe - irin su Lesotho - sun dauki mataki da wurwuri tun kafin cutar ta bulla.

Ta sanya dokar ta-baci sannan ta rufe makarantu ranar 18 ga watan Maris, kana ta sanya dokar kulle bayan kwana goma kamar yadda kasashen kudancin Afirka da dama suka yi.

Sai dai cutar ta bulla a Lesotho - a farkon watan Mayu - kwanaki kadan bayan ta cire dokar kulle. Kasar na da yawan al'umma fiye da miliyan biyu, amma ya zuwa yanzu mutum kusan 1,700 suka kam uda cutar korona yayin da ta yi ajalin mutum 40.

2: Goyon bayan al'umma

Wani bincike da PERC ta gudanar a kasashe 18 a watan Agusta ya gano cewa an samu goyon bayan jama'a sosai wajen daukar matakan kariya - kashi 85 na mutanen da aka tambaya ya nuna cewa sun sanya takunkumin fuska a makon da ya gabaci wanda aka gudanar da bincike.

"Kasashen kungiyar tarayyar Afirka sun dakile yaduwar cutar korona ne saboda an dauki tsauraran matakan kariya tsakanin watan Maris da watan Mayu," a cewar rahoton.

Hana mutane walwala ta janyo asara da dama ta hanyoyin cin abinci. A Afirka ta Kudu - daya daga cikin kasashen da suka fi tsaurara dokar kulle a duniya - an yi asarar gurabane ayyuka miliyan 2.2 a watanni shida na farkon shekara.

Kasashe da dama sun sake bude wuraren kasuwancinsu duk da yake mutanen da ke kamuwa da cutar a yanzu sun fi yawan wadanda suka kamu da ita a farkon bullar ta.

3: Yawan matasa - da kuma tsofaffi maras yawa a gidaje

Yawa ko kankantar shekarun galilin mazauna Afirka sun taka rawa wajen dakile yaduwar cutar korona.

A duk fadin duniya, akasarin wadanda cutar ta fi kashewa sun wuce shekara 80, yayin da galibin mazauna Afirka matasa ne inda ake da masu shekara 19 a matsayin tsaka-tsaki, a cewar alkaluman majalisar dinkin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Afirka ta fi Turai da yankin Amurka yawan matasa

"A Afirka kashi 3 na yawan al'ummarmu suna da shekara 65 zuwa sama," a cewar Dr Matshidiso Moeti, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO reshen Afirka.

Idan aka kwatanta, za a ga cewa Turai da Arewacin Amurka da kasashen da suka fi arziki a Asia sun fi yawan tsofaffi.

"Daya daga cikin manyan abubuwan da suka sa cutar ta yi tasiri a kasashen yammacin duniya shi ne akasarin tsofaffi na zaune ne a gidaje na musamman kuma a can ne aka fi samun yaduwar cutar," in ji Dr Moeti.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba safai ake samun gidajen ajiye tsofaffi ba a Afirka

Akasarin 'yan Afirka suna komawa kauyukansu idan suka yi ritaya daga aiki.

Babu mutane sosai a yankuna karkara don haka babu wahala wajen yin nesa-nesa da juna.

4: Yanayi mai kyawu

Bincike da masana na Jami'ar Maryland ta Amurka suka gudanar ya gano cewa akwai dangantaka tsakanin yanayin zafi, da dumi da kuma yankin da mutane ke zaune, da kuma yaduwar Covid-19.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Covid-19 ba ta yaduwa sosai a wuraren da ba su da dandazon jama'a

"Mun yi nazari kan farko-farkon yaduwar cutar a birane 50 a fadin duniya. Cutar ta fi yaduwa a yankunan da ba su da zafi sosai," a cewar Mohammad Sajadi, shugaban masu binciken.

"Ba wai ba ta yaduwa a wasu wuraren ba ne - amma ta fi yaduwa a wuraren da ba su da zafi."

5: Kyakkyawan tsarin lafiyar karkara

Cutar Covid-19 ta barke ne a yayin da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ke fama da matsalar Ebola. Kasashen da ke makwabtaka da ita sun shiga shirin ko-ta-kwana, don haka aka dauki karin matakai na kiwon lafiya fiye da aka samu bullar Covid-19.

Kasashen Yammacin Afirka da dama - wadanda suka yi fama da annobar Ebola daga 2013-16 - sun kware kan yadda za su dauki matakan kiwon lafiya domin hana yaduwar korona, wadanda suka hada da killace masu dauke da cutar, da gano masu dauke da ita, da kuma ware su a wuri na daban domin a yi musu gwaji.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aikatan Najeriya da ke yaki da cutar shan inna sun rikide wajen yaki da Covid-19

Bugu da ƙari, a Najeriya, tawagogin da ke bi gida-gida suna yin alluran riga-kafin cutar shan inna, sun juya inda suke wayar da kan jama'a kan cutar korona.

Don haka ko da yake asibitoci a galibin kasashen Afirka ba su da kayan aiki irin na wasu yankuna a duniya, nahiyar ta yi aiki da kwarewarta wajen tunkarar wasu annobobi da suka addabe ta wajen tunkarar annobar korona.

Amma hakan ba yana nufin a shantake a daina daukar matakan kariya daga cutar korona ba.