Halima Aden: Musulmar da ke tallar kayan ƙawa ta faɗi dalilin da ya sa ta bari

Halima Aden

Asalin hoton, Giliane Mansfeldt Photography

Halima Aden, mai ado da hijabi ta farko, ta bar masana'antar ƙawa a watan Nuwamba tana mai cewa hakan bai dace da tsarin addinin Musulinci ba.

A wata hira ta musamman, ta bai wa wakiliyar BBC Sodaba Haidare cikakken labarin yadda ta zama abar koyi, da kuma yadda ta yanke shawarar barin harkar.

Halima, mai shekara 23, tana zaune a St Cloud da ke jihar Minnesota, inda ta girma tare da wasu Somaliyawa.

Tana sanya kaya marasa tsada, sannan ba ta yin adon ƙara wa fuska haske, kuma ko da yaushe tana cike da fara'a.

"Ni ce Halima daga Kakuma," in ji ta, wato wani sansanin ƴan gudun hijira a Kenya, inda aka haife ta.

Wasu kuma sun bayyana ta a matsayin mace ta farko mai adon hijabi da aka buga hotonta a mujallar nuna kwalliyar ƙawa ta Vogue, amma ta bar duk wannan a baya watanni biyu da suka gabata, tana mai cewa masana'antar kayan kwalliya ta yi karo da imaninta a matsayin Musulma.

A matsayinta na mai sanya hijabi, Halima ta kasance mai tsananin zaɓi game da tufafinta.

A farkon fara aikinta, za ta ɗauki akwati cike da hijabanta, da dogayen riguna da siket zuwa kowane aiki.

Sannan duk aikin da za ta yi ba ta cire hijabi, wannan ba ma abin a tsaya a tattauna a kai ba ne, don ko kamfanin da take tare da shi na IMG akwai sharaɗin ƙin cire hijabi a tsakaninsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Halima kenan, yayin da ta shiga wata gasar ƙawa a watan Faibrairun 2017

"Akwai 'yan matan da suke tsananin bukatar samun kwantiragi da wani kamfani don zama masu adon ƙawa," in ji ta, "amma ni ba ta ɗaɗani da ƙasa ba, haka na fice daga cikinta''.

Amma yayin da tafiya ta yi tafiya bayan ta samu kwantaragi, sai ya zamanto ba ta da iko sosai kan tufafin da take sawa.

A shekararta ta ƙarshe a masana'antar, tsayin hijabinta ya riƙa raguwa, daga ƙirji ya koma wuya, sannan a wasu lokutan ma sai ta riƙa sanya kayan matsu tana tsukewa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Halima kenan a gasar Tommy Hilfiger a London

Wani sashe na yarjejeniyar Halima ya tabbatar mata da damar yin irin shigar da take so.

To amma daga baya sai ta lura cewa sauran wadanda suka shiga harkar ta dalilin koyi da ita su ba sa samun darajtawa irin wannan.

Ta yi tsammanin wadanda suka gaje ta su zama kwatankwacinta, kuma wannan ya ƙara karfafa karfinta gwiwarta na mara musu baya.

"Da yawa daga cikinsu suna da ƙuruciya, a gare su, masana'antar na iya zama mai ban tsoro.

Hatta bukukuwan da muke halarta, ko yaushe nakan samu kaina a matsayin babbar yaya.

Yayin da take yarinya a sansanin yan gudun hijira na Kakuma, a arewa maso yammacin Kenya, mahaifiyarta ce ta koya mata yin aiki tuƙuru da kuma taimakon wasu.

Kuma wannan ya ci gaba, bayan sun ƙaura zuwa Minnesota, lokacin da Halima ke 'yar shekara bakwai, ta zama wani ɓangare na mafi yawan al'ummar Somaliya a Amurka.

Don haka aka samu matsala lokacin da Halima ta zama sarauniya ta farko mai sanye da hijabi a makarantar sakandare a gasar girmamawa da aka yi wa fitattun daliban makarantar.

"Na ji kunya sosai, saboda idan aka tsayar da ku takara, yara sai su zo gidanku sai na ce, 'Kada ku yi haka, mahaifiyata ba za ta lamunta ba''.

Amma duk da wannan tsoro Halima ta halarci gasar ƙawa ta jihar Minnesota a shekarar 2016, har ma ta samu nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Halima Aden yayin wata gasa

Kamfanin IMG ya tallafa mata a wannan harka, kuma a cikin 2018 Halima ta zama jakadiyar Unicef.

Kamar yadda ta kwashe yarinta a sansanin yan gudun hijira, aikinta ya mayar ida hankali ne kan haƙƙin yara.

"Mahaifiyata ba ta taɓa ɗauka ta a matsayin abin koyi ko kuma yarinya mai rufin asiri ba.

Halima tana son wayar da kan yara game da yaran da suka rasa muhallinsu, kuma ta nuna wa yaran cewa idan har za ta samu nasarar fita daga sansanin 'yan gudun hijirar, to su ma su rika fatan wata rana za su iya fita.

A cikin 2018, ba da daɗewa ba da zama jakadiyar Unicef, ta ziyarci sansanin Kakuma don tattaunawa da mutane.

Halima tana fama da wata damuwa guda, idan ta tuna lokacin da ita da sauran yara ke rera waƙa da rawa lokacin da shahararrun mutane suka ziyarce su.

Asalin hoton, Getty Images

A gare ta, kamar kungiyar ta fi mai da hankali ne kan abin da take yi fiye da ilimin yara.

"Zan iya rubuta 'Unicef' lokacin da ba zan iya rubuta sunana ba. Ina yin alama ta X," in ji ta.

Tana ganin cewa duk wannan ya canza tun lokacin da ta bar harkar.

A watan Nuwamba, lokacin da ta tattauna da wasu yara ta bidiyo daga Kakuma, ta yanke shawarar ba za ta ci gaba ba, saboda yadda ta gansu zube a lokacin sanyi, kuma yayin da ake fama da wannan annoba.

Unicef a Amurka ta shaida wa BBC cewa: "Muna godiya da shekaru uku da rabi da Halima ta kasance tare da mu cikin hadin kai da goyon baya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Halima Aden kenan, yayin da take kallon wata mai adon ƙawa da Sherri Hill ta yi

A watan Satumba na shekarar 2019, an saka ta a bangon mujallar King Kong, tana sanye da jagira mai haske launin ja da koriya, da kuma wani abu da ta sanya a fuskarta.

Ya yi kama da abin rufe fuska kuma ya rufe komai sai hanci da bakinta.

"Salo da kayan kwalliyar sun kasance masu ban tsoro.

Sannan sai kuma mujallar ta sami hoton wani mutum tsirara ta sanya a bayan inda aka saka hotonta.

"Me yasa mujallar za ta yi tunanin cewa abin yarda ne a samu mace Musulma mai sanye da hijabi alhali namiji tsirara yana shafi na gaba?" Ta tambaya. Ya saɓa wa duk abin da ta yi imani da shi.

King Kong ya shaida wa BBC cewa: "Masu zane-zane, masu daukar hoto da masu ba da gudummawa wadanda muke aiki tare da su suna bayyana kansu ta hanyoyin da za su iya jan hankalin wasu kuma su zama abin tsokana ga wasu, amma labaran da suke bayarwa ko yaushe suna girmama batun.

"Na kasance cikin bacin rai, shin ko kun san irin lahanin da hakan zai iya yi wa wani?

Lokaci ne da ya kamata in yi farin ciki, amma sai na kasance cikin damuwa, saboda nice a mujallar, hotona ne.

Harkoki na sun samu karbuwa, amma tsakani da Allah ba a cikin farin ciki nake ba.

Ina matukar damuwa dangane da yadda ake ƙyamar masu sanya hijabi.

Yayin da cutar korona ta sauya komai, sannan ta kawo tsaiko cikin kowacce harka ciki harda ta kawa, Halima ta koma gida zuwa St Cloud don ta zauna tare da mahaifiyarta, wacce take matukar kauna.

"Na kasance cikin damuwa idan ina tunanin 2021 saboda ina matukar son zama a gida tare da iyalina kuma in riƙa ganin ƙawayena," in ji ta.

Duk wannan yana bayanin dalilin da ya sa, a watan Nuwamba, ta yanke shawarar daina yin kwalliya da matsayinta tare da Unicef.

"Ina godiya da wannan sabuwar damar da korona ta ba ni. Dukkanmu muna yin tunani game da hanyoyinmu na aiki.

Asalin hoton, Giliane Mansfeldt Photography

Bayanan hoto,

Halima tare da mahaifiyarta, da 'yar'uwarta Fadumo a hagu da kuma kanwarta Rahma

Hoto ba shi ne kawai abin da Halima ke murna da shi ba.

Ta gama aikin wani fim wanda ya samo asali daga ainihin labarin wani dan gudun hijira da ya tsere daga yaki da tashin hankali a Afghanistan.

Kamata a saki fim din mai suna I Am You, a Apple TV a watan Maris.

"Muna ɗokin jiran ganin ko an tsayar da mu takarar Oscar!" in ji ta.

Dakatar da Unicef ba yana nufin Halima ta daina yin aikin sa kai ba.

"Ba zan daina aikin sa kai ba," in ji ta. "Bana tunanin duniya tana bukatar ni a matsayin abar koyi ko shahararriya, tana bukatata a matsayin Halima daga Kakuma.

"Ka sani, ban taɓa zuwa hutun da ya dace ba. Ina sanya lafiyar hankalina da iyalina gaba da komai.